← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 69

Sashe 36

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tunda AFREED ya farka yake jinshi cikin wani irin farin ciki mara musultuwa sai fara'a yake haka kawai badan yasan dalili ba har ƴan gidan sai da suka fahimci haka daga gare shi, suna zaune suna karyawa yawa sai murmushi yake shi ɗaya, tanti ta lura da hakan tun shigowar sa falon ta gane cewa yau ɗan nata na cikin farin ciki ko dan gani da tayi masa yau ana magana yana saka bakin ba kamar kullum ba itama murmushi tayi ta kallesa tace "Yau ɗana lafiya na ganka cikin farin ciki haka sai wani sakin murmushi kake, ai ya kamata araba farin cikin nan damu dan muma mu tayaka murnar kodai sirika a samar min ne?"

Kamin AFREED yace wani abun Farisa tayi saurin cewa "Ko dai yaya kayi waya da Momy ne shiyasa kake ta farin ciki nidai kam kamar tanti yau na lura kana cikin jin daɗin."

Maida kallon sa yayi wajen Farisa ya sakar mata murmushi sannan ya dawo da kallon sa ga tanti yace "Lah Tanti wallahi ba haka bane kawai dai nima yau na tashi na tsintsi kaina cikin farin ciki da bansan dalilin sa."

Murmushi tanti tayi sannan tace "To Allah dawamar da kai cikin sa." Da ameen suka amsa su duka, sannan suka miƙe daga cin abincin suka koma falon, basu jima suna fira ba AFREED da Ali da Umar suka miƙe tareda cewa Tanti Aicha ( ƙanwar mahaifin AFREED dama sunanta Aicha to yanzu namai da su AFREED su ringa kiranta da tanti Aicha dan a banbantata da tanti kishiyar Maman AFREEN dan masu karatu su fahimta) su AFREED su kacewa tanti Aicha sun koma ɓangaren su kamin lokacin tafiya Sallah juma'a yayi haka."

Da to ta amsa masu sannan sukayi gaba abinsu, suna shiga ɓangaren su kowa ya nufi nashi ɗakin, AFREED zaune saman gadon da ƙur'ani a hannu sa yana karanta suratul kahaf kuma yanayi yana duba montre ( agogo) sabida ya matsu lokacin zuwa masallaci yayi ko zai ganta ba dan komai sedan yaji muryar ta.

****** ******* ******

Kamar kullum haka mutanen gidan su AFREEN suka tattara su tafi masallaci yau kam a tare suka tafi dan AFREEN bata bari suka barsu ba, mota papa da matansa sa ita ke gaba AFREEN na binsu a baya sannan motar su Fahad shida ƙanansa Imran sun jera tsaf kwanin ban sha'awa, Suna ƙarasawa masallaci su Fahad suka nufi wajan parking ɗin maza shi kuwa papa saida ya ajiye matan sa bakin masallaci mata sannan ya juya itakuwa AFREEN direct parking ɗin mata ta nufa ta paka tata motar sannan suka fito ita da ƙannanta suka jera suka nufi hayar shiga masallacin, sun ɗan jima da zuwa sannan aka tayar da sallah dan har nafila sai da sukayi, huɗuba ma suna can aka fara har aka ida tare da su.

Ana sallamcewa daga Sallah aka fara ɗauri aure da aka gama kowa ya fito banda su AFREEN wanda haka ya zama al'adar tane sai mutane sun rage suke fitowa, kuma gashi tanata dube dube ganin ko zataga ƙawarta dan duk yau basu haɗu ba kuma yau ba makaranta sukayi ba suna hutu, kuma gashi cikin masallaci duk mutane sun watse bata ganta ba sai take tunanin ko batazo, sai kuma tace amma tace man zata zo kodai tana ƙasa yau ba a sama tayi sallah ba bari naje na dubata, daganan ta juya ta kalli su Zeinab dake jiran ta tace "ku taso mu tafi." Ba musu suka tashi.

AFREED na bakin ƙofar masallaci yana ta wange wangen ina zai ganta ko yauma a parking ɗin maza ta ajiye motar ta?" Ya tambayi kansa tareda nufar hanyar wajan ko da zai ganta acan to dama idan mutun zaije parking ɗin maza sai ya bi ta hanyar masallaci mata kamin yake kai wajen parking ɗin na maza, hakane ta kasance yanzu AFREED na shirin wucewa ta ƙofar masallaci mata dan zuwa parking ɗin maza dan tun tuni Ali ya kecan yana jiransa, ita kuwa AFREEN ta fito kenan dan zuwa neman Hasina ƙawarta, dama ta rika da tace ma su Zeinab suje mota su jirata.

AFREED ya taho kansa duƙe yana dana waya itama ta taho ta kusa kawowa gun shi kawai sai taji ance "Bestyyyyyyy." ba tare da ta tsaya da tafiyar da take ba ta juyo da ƙarfi dan jin muryar Hasina shima ya taho ba tareda yasan da itaba kawai ji sai tayi ta bangaji mutum ai kuwa a take ta juyo da sauri a lokacin da wayar da ke ga hannu sa ta faɗi ƙasa, da sauri AFREEN ta tsuguna dan ɗauko wayar shima ya tsuguna a tare suka kai hannu zasu taɓa wayar aikuwa sai hannuwan su suka gamu da na juna a take sukaji wani yar yar tun daga cikin kwalwarsu har tafin ƙafafun su da sauri AFREED ya janye hannunsa dake saman na AFREEN sabida shi shok ɗin yafi jansa, a tare suka ɗago cikin sauri hankan yayi sanadiyar kwarewar niƙaf ɗin AFREEN ba tare da ta sani ba ko ta lura da hankan ba, cikin firgici da mamakin kyau irin nata AFREED ya waro idanso kuri 😳 yana kallon ta ba tare da yasan yayi hakan ba, gabansa na mugun faɗuwa, a zuciyarsa ya aiyana cewa anya wannan mutum, idan mutum ce kuma wane irin masifafen kyau ne da ita haka? A take ya ba kansa amsar cewa kai ba mutum bace dan gaskiya a cikin duniyar nan babu muntun mai irin wannan bala'iyayen kyau nata.

Ya dawo daga duniyar tunanin daya lula ne a lokacin da ya tsinci zazakar muyar ta na furta " Dan Allah kayi hakuri ba da gangan nayi ba." Tana faɗar haka tan miƙa masa wayar da ke ga hannuta."

Ƙoƙarin control ɗin kansa yayi ya ƙarɓi wayar da ta gama gogewa cikin zuciyarsa yake faɗin wallahi itace wace nake nema itace ke da muryar nan mai sanhi da daɗi sauraro dole ne tayi kyau koda na jin muryar ta, ai kasan ta haɗu, a take wata zuciyar tace masa idan fah ba mutum bace?" Sauri kauda zancen yayi sannan a fili kuma sai yace "A'a karki damu ba wani abu."

Murmushinta mai kwantar da zuciya da saka mutum natsuwa ta sakar masa kuma har yanzu bata san cewa niƙaf ɗin ta janye daga fuskarta ba sannan tace "Nagode."

Da sauri AFREED yayi saurin dafe daidai zuciyar sa da ke harba masa da sauri da sauri tareda lumshe idonsa sannan ya buɗe sanadin sakar mashi ƙayatacan murmushi shinta mai kashe matum jiki da tayi, tareda kallon lips ɗinta ƙananu suna matsi a hankali idan tana magana ga gefan kumatunta duka biyu na lotsawa koda kuwa magana take ba sai tayi murmushi ba, cikin zuciyarsa ya furta zata kashe ni, hankalinsa na ƙoƙarin barin jikinsa yayi saurin ɗaga mata kansa ya bar gun ba tareda yaso hakan ba, dan gudun kada ya bada kansa.

Itama juyawa tayi ta bar gun ta nufi inda aminiyarta ke tsaye tana kallon su, tana ƙarasawa Hasina tace "Kai besty yau kinyi babban kamu kinga yanda mutum can ke kallon ki duk ya wani rikice a kanki kuwa gashi niƙaf ɗinki kuma ta ɗage sosai, kowama ke yakema kallon ƙurila juya kika yanda mutane ke kallon ki kamar sunga sabuwar halitta."

Sai a sannan ta lura da niƙaf ɗin bata ga fuskar ta ai da sauri ta gyara zaman niƙaf ta daidaita ta sannan ta saketa ta rufe mata fuska rufe sannan ta juya taga wanda mutane suka taru suna kallon ta da sauri ta ja hannu Hasina suka nufi wajan motar ta ida su Zeinab ke tsaye suna jiran ta, sai a lokacin ta samu damar sauke ajiyar zuciya tace "Besty kinga abinda yasa nan nake ɓoye fuskata duba kiga wanda mutane suka taru suna kallon na wallahi duk sai najini a takure."

"Rabu dasu haba kallon kaɗai ke nasu, ina maki maganar mutuman nan da kika yadawa waya kinyi min shiru." Hasina ta faɗa tana kallon AFREEN

Murmushi AFREEN tayi tace to "Besty ya kikeso nace maki ni babu wani kallo da naga yanayi min kawai daga haɗuwa, shirme ne kawai irin naki, idan kuma wani kallon ya min to bai huce shima na mamaki ne kamar yanda sauran mutanen sukayi ba."

Hasina tace "Hum sedai in kece baki gani ba nikuwa nagani wallahi bama kamar rikicewar danaga yayi, ni kam nahango wani abu a cikin idansa wanda ke baki ajiye hankali ba bare ki gani, kuma ni wallahi naga kamar ma MINISTRE DES DÉFENSES ET DE SÉCURITÉ ne wallahi baki ga shima da babette a fuskar sa, amma firgici ganinki da yayi bai san ma ya cire shi ba."

"Kai besty mi zai kawo minister (minista) nan gurin ba tare da masu tsaron sa ba shi ɗaya haba kema dai kinsan hakan ba zai yiyu ba, da shine da a lokacin da na bangaje shi har nayi sanadiyar faɗuwar wayar sa to da yanzu matakan tsaron sa sun lalasani koda ace anesa da shi suke to yanzu zakiga sun rugo sunyi magani na, barema basa yin nisa da shi kullum suna liƙe da shi kamar shiwinggum, kuma da a ce anan yayi Sallah da kin dinga ji kukan motacin jami'an tsaron da suke kare lafiyar sa tun kamin a shiga masallacin, kuma gashi bama a maraɗi yake ba, yanzu haka ma bai taɓa zuwa garin nan ba, kinga ko a TV ba muji ance zai zo ba, dan haka ki bar ma faɗa kada ajiki.

Hasina tace "Kuma hakane fah to amma wannan yayi mugun kama dashi, ta yiyuwa ko wani ɗan uwan sa ne kuma fah kawata kusan sunan ku irin ɗaya ne ministan da tsaro, Shi AFREED ke AFREEN ni ina ma zaizo ya aure minke."

AFREEN ta taɓe baki tare da cewa kindaiji da shi ni mi zanyi da wani minister, KAMAL ɗin na ya ishe ni, shi kaɗai nakeso da kauna, kuma insha Allah shine mai gida na, yanzu dai ba wannan ba ku shiga mu tafi gida."

Gaba ɗaya suka shiga sannan ta tayar da motar sai gida..................

( nima sai nabi tawa hanyar nace bari na barsu hakanan har bayan kwana biyu kuma sai mu waiwayesu)
Chapter 36 · 0% Book details