Sashe 16
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A take gabana ya fad'i sai na shiga tunanin mafita ai kuwa nasamu. Sai nace masa inada mafita yanzu zanje na sami shi babban na fad'a masa na take na gayawa abokina nawa mafitar dana samu sai kuma yayi na'am da ita haka, a tare da shi mukaje muka fad'a ma mai kanfanin cewa zanje ganin gida ne mahaifina ya kira yana son gani nan sabida yau shekara biyar tun da nazo garin ban koma ba Allah da ikonsa ina fad'a masa ya yarda hada tambaya ranar da zanyi tafiyar nace masa gobe haka ya bani mak'udan kud'ad'e tare da yimin fatan sauka lafiya sannan kuma yace ga jirgi sa nan a kaimu har garin mu naji tausayin sa sabida idan yasan k'udirina ba zai yarda da tafiyar tawa. Haka dai muka shiga gari muka yo sayaya sosai ina ta tunanin shin Arahamat ta kai yaya yanzu nasan dai tana da tsayi kuma nasan da yanzu ta k'ara kuma shekarunta ishirin yanzu, haka nayi ta jidar masu kaya ita Jannah masu tsayi, nakima Tanti Fatima inata k'iyastawa na Ufadi ma haka Abbu ma haka nadai siyo nidai bansan zasuyi ba ko ba zasuyi ba Allah wa'alam kuma sai in kun saka, safiya na waye wa muka baro Canada mukasa sauka garin Niamey a take naji wani matsanacin farin ciki ya lulub'eni yau ganin cikin Niger tunda nabarta yau kimanin shekara 5 da 'yan watani bantab'a lek'ota ba sai yau na juya na rugume abokina ina farin ciki sabida gani nake har nazo gida cikin yarda Allah."
"Kwanan mu guda Niamey na shigo bus kin Agadez abokina kuwa dayake d'an Marad'i ne yabi bus kin marad'i sai gashi yau dai Allah yayi nazo gida da fatan duk zaku yafe man ba da son raina haka ya faru ba, batun kuma nayi yanda akayi na kawo kaina gida mai sauk'i ne dama ban manta da sunan anguwa mu ba haka kamanin gidan muma bai b'ace min ba duk da naga ya k'ara zubewa amma haka bai hanani k'in ganesa ba taxi kawai nashigo nayi masa kwatance ya kawoni har k'ofar gidan nan."
Yana gama fad'a labarin ya sauke wata irin ajiyar zuciya sannan. Ya na jiran jin abinda zasuce.
Suma ajiyar zuciyar suka sauke kamin Tanti Fatima tace "Allah maka albarka kuma Allah yafe mana gabad'aya tunda ma dai lafiya kake ai shikenan, gashi kazo daidai lokacin da ake da buk'atarka sabida nan da kwana hud'u za'a d'aura wa Arahamat aure insha Allah."
A take yaji wani farin ciki ya k'ara lulub'e shi yace Alhamdulilah naji dad'in samin wanan labari nayi farin ciki sosai k'anwata Allah sa alkairi, oh Allah nagode maka da ka dawo dani a daidai wanan lokacin kinga Allah da ikonsa inada rabon shafa fatihar auren k'anwata mafi soyyiwa a gareni Allah maki albarka Arahamat Allah sanya alkairi a cikin auren ya baki zaman lafiya da farin cikin mai d'aurewa da zuri'a d'ayaba, zako aminki aure irin na 'ya'ya gata sabida yanzu haka maganar danake maku ina da mak'udan kud'in da ni kaina basan yawan su ba dan haka Tanti Fatima gobe ku shirya tare da ita ku bi jirgi ku tafi Dubai siyaya ta zabo abinda takeso."
Aiko take Arahamat ta fashe da kuka tace "Yaya nagode allah saka da alkairi banida kamar ka yayana bayan mahaifina kaine uwata."
Shima saida kwalla suka zubo masa yace "Baikomi k'anwata yi shiru ki daina kuka nima ban da kamarku idan ban maku ba wa zan ma ko da kuwa ace banda wanan kud'in zan shiga in fita in samo wanda za'a fita kunya to baranta nama inada anfanin mi zasu man idan ban muku."
Tanti Fatima ta nisa sannan tace "yanzu dai wuri ya k'ure da zuwa Dubai kawai abinda kenan shine a hau jirgi a tafi Niamey sayaya ko Marad'i dan can akwai komi sai d'an abinda ba'a rasaba sai ta zab'o abinda takeso."
Haka dai suka tsayar da maganar zuwa Niamey Gobe in Allah ya so ya yarda.
Haka dai suka ci gaba da firar yaushe gamo har Abbu ya dawo, lokacin da Abbu yayi tozali da Ibrahim sedai gabansa ya fad'in dan a tunanin sa fatalwa ce dan bai tab'a tunanin yana da rai ba ga shekarun da ya d'auka bai dawo ba. Nan dai daya ta bata ba fatalwa bace yayi mugun mamaki sannan kuma bai yi fushi da shi ba don ya nason ya hujarshi haka kuwa akayi ya kwashe komi da ya fad'awa su Arahamat ya gayawa Abbu a take yayi samasa albarka tare dacewa "Gaskiya shawara da abokinka ya baka tayi sabida da ka dawo mani gidan ba sakamako mai kyau da ba zanji dad'in ba tunda banida wani buri kamar naga kunyi karatu mai zurfi ku duka. Haka ma ya isa mugode wa Allah tunda lafiyar ka lau ba abinda ya sameka Allah maka albarka.
Sannan a kaci gaba da fira ana wasa da dariya har dare yayi sosai kowa yaje ya kwanta da niyar tafiya Niamey sayayya gobe in Allah ya so ya yarda.
Shima sadisu angon Arahamat ba k'aramin dad'i yaji ba lokacin da labarin zuwan yayan amarya sa ya zo kunan saba sabida kusan kulum idan yazo zance sai ta masa fira yayan ta itadai yayan ta har zowa yayi ganin sa kuma suka dad'e suna fira karmar sun san dad'e dasani juna.
Ga goben suka shirya suka tafi Niamey sayayya hada Ufadi sayayya sukayi sosai sannan ana gobe d'aurin aure suka dawo aka ci gaba da shirin biki. Darzn ranar da suka dawo k'anwa Arahamat takira su tana kuka wai an samasu examen (exam) bazata sami zuwa ba dama tunda rana suke neman number basu samu ba.
Badan Arahamat taji dad'i ba amma a haka ta hakura tunda tasan harakar karatu sai a hankali.
Yau ya kama ranar d'aurin aure, k'arfe tara na safiyar asabar a ka d'aura auren Arahamat musa da Sadisu Asmane Sanga akan sadaki 50000 d'aurin aure kam ya tara mutane sosai sabida mahaifin Arahamat malami ne da kowa ya sanhi a cikin garin na Agadez ga mutunci da datako gashi kuma daga b'angaren ango ma dangin shi da dama sun halarci taron duk da nisan dake dakwai tsakani Niamey da Agadez, Alhamdulilah kuma aure ya d'auru.
Arahamat najin an d'aura kuwa tayi ta kuka wanda kyar yaya Ibrahim ya shawo kanta tayi shiru.
Kwana d'aya da d'aura auren suka bi jirgi sai Niamey sabida a can za'a kai amarya banyan nasiha da tasha wajan abu da yayanta da Tanti Fatima kuma da Ufadi sannan tanemi iyayen gafara Mahaifin Arahamat hada kuka yayi yana samata Albarka, haka dai aka tafi da ita tana kuka Yayan ta da mahaifin ta na tayata.
Haka dai su Tanti Fatima da Ufadi suka tafi raka Arahamat Niamey gidan mijin ta..........
Sai muyi fatan Allah kaisu lafiya...........
Na QUEEN ZEEFAT yar mutan Niger
Muje zuwa..............💃💃💃💃💃
Alhamdulilah
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
ECRITE:
_PAR_
*QUEEN ZEEFAT*
Yar
Mutan
Niger
Wattpad@nazhabibou
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_
Page 10
Yau kwana shida kenan da haduwar Arahamat da Sadisu, amma har yanzu bai sake dawowa ba duk tabi ta damu, haka yanzu ma tana cuisine (kitchen) tana aiki tunanin sa take, cikin zuciyar tace "To wai miyasa na damu da rishin zuwan sa ne? Duk Nabi nadamu" wani b'angare na zuciyar yace sabida sauran kud'in sa dake wajan ki ne, da sauri ta furta "Hakane allah sa dai yazo ya karb'i kud'in sa kar ya barni dasu in shiga uku gashi kuma ni ban san idan zan gansa ba bare na kaima sa."
Da dadare banya sallar isha'i wani yaro ya shigo gidan su Arahamat yace "wai ana kiran wata yarinya buzuwa doguwa waje."
Ufadi dake zaune tsakar gida da tace "Wake kiranta."
Yaron yace "wani a waje."
Ufadi tace "Je kace tana zuwa".
Yaron ya juya ya fita Arahamat dake cikin daki tunda taji yaron da ya shigo yace ana neman wata buzuwa doguwa gaban ta ya yanke ya fad'i ta san da itace ake nema "To amma waye? itadai tasan ba mai zuwa wajan zance kuma ita ba wanda ta tab'a nunawa gidan su to yanzu waye ke nemanta?
Bata k'arasa tunanin da take ba tajiyo muryar Ufadi na cewa "Ke Arahamat taso ki fito ana neman ki a k'ofar gida yau dai kin sami meso da kulun kina cikin gida har kin kai girma na gida idan aka shigo ba mai gane tsakanin ni dake wacece uwar wace d'iyar, mutana ta guga kafad'a kizo kin tile a gida ba mai sonki, yarinya sai bak'in jini mtssss."
Fitowa tayi daga d'akin tace "Ufadi Abbu fah?"
"Mtsss yana cikin d'akin shi munafuka zakije kiyo masa gulma ko?"
Ita dai ba tace mata komai ba ta nufi d'akin mahaifin ta samun shi tayi yana zaune da alkur'ani a gaban sa da alama karatu ya gama ta d'an rusna tace "Abbu ana nema na a waje."
Ba tare da ya dago ya kale ta ba yace "Waye?"
"Nima ban sani ba Abbu."
"To jeki amma kada ki dad'e kuma ki kula da mutuncinki."
Ta amsa da "To" sannan ta tashi tafita bata tsaya bin ta kan Ufadi dake ta yada mata magana da jefa mata harara ba directe (direct) waje ta wuce.
Dayake da duhu a wajan sai haskin farin wata yasa tayita dubawa bata ga kowa ba, tana shirin juyawa ta koma taji ance "Sannun ki malama."
Da sauri ta waigo gun da taji sautin maganar ya fito, bata dai gane kowaye ba kawai sai ta k'ara matsawa kusan shi, aiko ta ganeshi tace "Lah kaine?"
"Eh nine ashe kin gane ni?"
"Haba ba dole na ganeka ba tunda sauran kud'in ka na guna, ai se in ka karb'e su kawai zan manta a lokacin nasan ba ha'kin kowa a kaina."
Waro ido yayi waje yace "Lah ashe ma zaki manta dani daga zarar na karbi kud'i na ko? Ko irin wanan d'an zumuncin ba za muyi ba dan mu ringa kaisawa."
Tace "A'a bahaka nake nufi ba idan dai mun had'u a hanya ai zamu gaisa."
"A'a gashinan kin fad'a da bakin ki cewa da zarar na karbi kud'in na zaki manta da ni."