← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 69

Sashe 57

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sanu a hankali ta fara rage kukan har ta ta daina baki ɗaya yanajin tayi shiru ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan yace "To AFREEN Nagode sai da safe yi hakuri da takuraki da nayi hakan ba zai sake faruwa ba , ki kula da kanki." Sai ya katse kiran ba tare da ya jira jin abinda zata ce ba sabida ya ga alamun ba zata ce komi ɗin ba cike da damuwa ya faɗa kan gadon sa ya kwanta tare da lumshe idonsa yanajin yanda zuciyarsa ke harbawa da sauri da sauri, tare da addu'ar neman sassauci wajen Ubangiji game da abinda yake ji a game da ita, ya kai minti biyar a haka kamin ya buɗe ido sa da suka masa jajir don damuwa da radin da zuciyar sa ke masa.

Ƙara lumshe idon sa yayi da niyyar yin bacci amma ina bacci ya ƙasa zuwa haka dai ha kusan ƙarfe ɗayan dare AFREED ya kasa rumtsawa kawai sai ya tashi ya nufi toillet ya dauro alwala ya fito, shimfiɗa darduma yayi ya fara jero nafilfili ya na kai wa Allah kukan sa cikin ikon Allah ya samu sasauci sosai daga abinda ya ke ji a zuciya sa, shine bai samu bacci sai wajen ƙarfe 4:00 sannan bacci ɓarawo yayi awon gaba dashi, kuma cikin ƙananan lokacin kiran sallah asuba ya farakar dashi cike da magagi bacci dake cinsa ya tashi ya shiga bayi ya watso ruwa a gaggauce saboda yaji ana shirin tayar da sallah ya na fitowa ya zura jalabiyar sa fara ya nufi masallaci, a ƙa'idar AFREED idan an idar da sallah asuba bai baro masallaci sai rana ta fito, amma ana gama sallah tare da yin adu'oin sa na bayan sallama daga sallah kawai ya taso yayi tafiyar sa cikin gida ba tare da yayiwa ko da dady ina kwana ba, hasali ma bai ma lura dasu ba har Ali dake kusa dashi, bacci kawai yake son yaje yayi, da mamaki Ali ya bishi da kallo, a zuciyar sa yace "To shi wancan lafiya kuwa ko dai duk soyayyar ce?"

Murmushi kawai Ali yayi tare da girgiza kai yace "Sabon shiga dole ne ya kasa controlling ɗin kasa." Sannan ya juya ya ci gaba da addu'ar sa.

AFREED na shiga ɗakin sa ya faɗa saman gadon sa ya shiga rankon bacci shi ne bai farka ba sai wajen 11 na rana yana tashi yayi miƙa tare da salati sannan ya faɗa toillet ya yi wanka ya fito ya shirya cikin shirin sa na tafiya office yayi kyau sosai saboda irin masu jikin nan ne wanda komi ka saka ya yi ma kyau, fitowa yayi a gaggauce saboda yayi latin zuwa aiki gashi har sha biyu na rana ya kusa tunda yau juma'a sauka guda sukeyi sai sun kai har ƙarfe ɗaya da rabi na rana a office, da sauri ya shiga ɓangaren maman shi ya gaida ta sannan ya cema "Ali ya tashi su wuce office." Ali da yake a shirye shi kaɗai kawai yake jira ya miƙe ya nufi ƙofa shi ma ya biyo bayansa,

Momy ha sun kai ƙofar falon Momy tace "Ba zaka ƙarya ba zaka fita."

Yace Momy zanyi idan na dawo."

"A'a wuce ko thé (🍵) ne kasha babu kyau fita ba'a ci komai ba."

Ba musu ya nufi dinning inda Momy har ta riga sa kaiwa ta haɗa masa thé (🍵) ta miƙa masa ya ƙarɓa ya sha sannan ya fice daga falon wanda Ali har ya kai gun motar shi kaɗe yake jira yana fitowa garde corps (Bodyguard) dinsa suka miƙe tare da nufar motocin su don kowane group da motar sa su wajen goma sha biyar, a cikin kowace mota da mutun biyar a cikin ta sai mota da AFREED ke shiga shida Ali da direban sa a ƙala suna fita da mota huɗu ko biyar wataran har bakwai, da sauri suka shiga gaida sa, su sunyi tunanin yau Bama za'a je wajen aiki ba tunda sun ga rana tayi.

Cikin ƙananan lokaci suka isa ma'aikatar tasu ana gama parking yayi saurin buɗe ma kansa ƙofar motar ya nufi ciki da sauri suma Bodyguard din suna ganin haka suka mara masa baya da sauri wanda shi Ali har ya riga da ya cin masa, haka kuma ya shige gabansa da sauri ya buɗe masa office ba tare da ya tsaya watawata ba ya faɗa office ɗin da sallama a bakin sa, direct kujerar zaman sa ya nufa ya zauna nan take, shi ma Ali ya nemi kun zaman sa ya zauna ya tsura masa ido bai ce masa komai ba dan yasan duk wannan saurin da yake dan yayi lati ne kuma gashi an kusa tashi, AFREED ya shiga duba file ɗin dake gabansa cikin kwanciyar hankali ya fara aikin da ya tarar masa saboda jimawa da ya yi bai je office ɗin ba, ciki minti 40 ya kammala komai da komai a sannan yakai hannun sa kan téléphone☎️ ɗin dake saman table ɗin ya dana kira,
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*

*Page :* 53 & 54

"Tana fara rigin aka ɗaga a takaice yace "Amina ki zo office ɗin nan yanzu." Bai jira jin abinda zata faɗa ba ya katse kiran tare da ƙara duba file ɗin dake riƙe da hannu sa. Ko minti biyu ba ayi ba da katse kiran sai gashi ta kwonkwosa Ali ya bata izinin shigowa sannan ta buɗe ƙofar ta shigo da sallama, duk kansu suka amsa sallamar amma sai dai shi AFREED in ba kusan sa kake ba ba zakaji ya amsa ba, sannan ta gaida shi ya amsa sabida da ya shigo yana sauri bata samu damar gaida shi (wato Amina secrétariat ɗin AFREED ce)

Cike da ladabi ta ɗan gusa kusa dashi tare da yi kasa da kanta kaɗan tace "Yalaɓai gani."

Ba tare da ya kalle ta ba ya mika mata file ɗin dake ga hannun sa ta karɓa sannan yace "kije bureau ɗin ministre (minister ) Aliyu ki kai masa kice injini, idan hali gobe nakeso ya dawo man dashi."

"D'accord chef."

Sannan ta juya ta fita a office ɗin, sai a wannan lokacin ya ɗago ya dubi Ali ya sakar masa murmushi sannan yace "Ɗan uwa mu koma gida na riga na kammala abinda ya kawo ni."

Murmushi shi ma Ali ya mayar kamin yace "To muje ai naga yi baka da dama shiyasa ban takaka ba har ka ida."

AFREED ya yi murmushi yace "Wallahi kuwa amma yanzu tunda na ida ai shikenan."

Daga haka suka miƙe suka nufi kofa suka fice daga office ɗin basu tsaya ko'ina ba sai gida.

Ɓangaren AFREEN kuwa ta kasa gane kanta saboda tunda safiyar Allah ta waye take ta riƙon wayar ta ko zata ji AFREED ya kira amma shiru, haka rashin kiran nasa ya dame ta har zata zauna ta na tunanin yaye inta shi da ta damu dan bai kira ba daga fara kiran ta jiya, sosai hakan ya bata mamaki, amma kuma sai ta basar

AFREEN har ta fida rai da AFREED zai kirata sai ga kiran nashi ya shigo wajen ƙarfe 4 na yamma bayan sallah la'asar waya na ta rigin tana kallo bata ɗaga ba kamar dai ba kiran take jira ba, sai ga kira na biyu shima yana gab da katse wa ta ɗaga tare da yin sallama AFREED najin ta ɗaga saida ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai sauti har sai da taji dan shi ya ma fida rai da zata ɗaga.

Amsa mata sallama yayi, kamin ya koma cewa wani abu tace "Ina yuni?"

Wani farin ciki ne AFREED yaji ya luluɓe don kawai sai yaji yau ya kira cikin sa'a sabida kamar yaji maganar ta cikin sakin fuska, saida ya saki murmushi kamin yace "Lafiya klau" da fatan kin yuni lafiya kuma kina cikin koshin lafiya?"

Ƙasa ƙasa ta amsa da "Lafiya lau"

Yace "Ya gida ya su maman da kowa da kowa"

Ta amsa da "Alhamdulilah"

Nan dai suka ɗauki kusan minti biyar bawanda ya ƙara cewa komai amma zuciya AFREED sai bugawa take da ƙarfi fat fat fat yana tsoron ƙara mata maganar soyayyar sa ta ƙara fashe mashi da kuka can yayi ta maza yace "AFREEN dan Allah kiyi tunanin kan maganar da nayi maki jiya wallahi ina matuƙar sonki idan har kika ƙini zan shiga wani hali ki taimaka dan Allah."

Kusan kamar second talatin bata ce komai bai sai kuma tace "Inshallah zanyi shawara a kai."

"Zuwa yaushe zan samu amsar?"

"Nan da sati haka, ko yayi kaɗan?"

"Ki taimaka AFREEN wallahi sati ya yi min yawa ina laifin kice anjima."

"Ina anjima ya yuri gaskiya, ai ko tunani ban fara a kai ba."

To dan Allah ki tausaya wa rayuwa ta AFREEN kice gobe."

Saida ta ɗauki kusan minti ɗaya batayi magana ba kuma sai tace "To shikenan amma goben sai da dadare in ka yarda."

"To shikenan ba damuwa Allah ya kaimu goben lafiya."

Ya samu saken biyu bai ce komai sai kuma yace "Dan Allah zan iya kiran yau da dadare mu ɗan yi fira?"

Saida tayi ɗan jim kaɗan tace to ba laifi amma ba da dare ba sosai."

"To shikenan an gama ranki ya daɗe yanda kika ce haka za'ayi sai na kiraki ɗin."

Saida tayi ɗan gajeren murmushi sannan tace "To ba damuwa."

"Ki gaida ƴan gidan."

"Za su ji insha Allahu."

Sannan ya katse kiran cike da farin ciki yaje ya samu Ali ya sanar masa yanda sukayi da ita nan take shima ya taya shi farin ciki."
Chapter 57 · 0% Book details