← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 69

Sashe 49

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Inusa wani shahararren likitane da yayi suna a faɗin duniyar nan kuma da yasan aikin sa, yayi karatu sosai a fannin ciwu wuka da yawa dake damun ɗan Adam, yayi karatu akan ciwon dake damun fatar jikin ɗan adam yana da ilimi akan ciwon ƙwaƙwalwa da ciwon ido ciwon haure da irin wanda ya shafi mata da na kwada dana sihe da na zuciya dama sauran ciwuka da ban zana ba, dan haka yayi fice ko ina a san shi, da Alhaji Sumana dadyn AFREED da kuma Alhaji Sadisu mahaifin AFREEN da shi Dr Inusa duk abokan juna ne tun suna yara, shi ya fi su yin karatu mai zurfi dan yana kasashan waje yana karatu duk su dadyn AFREED da papan AFREEN sukayi aure dan haka baisan matan su ba, itama Arahamat mahaifiyar AFREEN wato matar Alhaji Sadisu, yasan tane dalilin auren ƴar uwar ta daya ke.

Sosai yayi yawon duniya, dan kasanshan duniya ɗaya ɗaya ne baje ba, ba tare da ya ƙarasa karatun sa ba yayi aure ya auri Jannah (wato ƙanwar Arahamat mahaifiyar AFREEN) haɗuwar sa da Jannah kuma ta dalilin abokinsa ne Ibrahim (wato ƴayan su Arahamat da Jannah) da suka game wajen karatu a New York (in masu karatu basu manta ba Ibrahim na wani aboki ɗan masu arziki da suka haɗe wajen karatu a kasashen waje), yanzu suna zaune a Dubai yanzu haka, ba gari guda suka zauna ba sabida yawan tafiye tafiye da mijin nata keyi yau in suna wannan ƙasa gobe suna wacen Niger kaɗai idan zai taho sai ya barosu saboda karatun yaransu da suka saba da irin na ƙasar waje, ya shahara sosai a aikin sa kuma ya ƙware iya ƙwarewa fiye da tunanin mai karatu, ya san aikin sa sosai dan har a ƙarsa wajen neman sa suke zuwa idan wani abu ya ƙaƙare masu to da ikon Allah shi zai warware sa sabida ya nemi ilimi sosai yanzu haka cikin neman sa yake, idan yazo Niger yana wata uku bai koma gun iyalinsa ba saboda ya malaki asibiti guda huɗu biyu a babban birnin Niamey ɗaya a Maradi ɗaya a Zinder, yana wata ɗaya a cikin asibitin sa da suke cikin garin Niamey yaje Maraɗi ya wata ɗaya ya koma Zinder yayi wata ɗaya, to shi duk mara lahiyar da yayiwa aikin da ikon Allah sai yaji sauƙi sedai idan ciwon ajali ne mara lafiyar yake ko kuma ciwon da bai shafi asibiti ba.

Kamar wata baiwa ce Allah ya bashi dan taimakon al'umma duk ta dalilin wannan aikin nasa ya zama wani shahararren mai arziki, kuma baisa tsada a cikin harakar yiwa mutum magani cikin asibitin sa ba, dan haka kowa najin ya zo gari ko lafiyar ka lau zaki ga mutane na tafiya ya duba su.

Suna shiga cikin office ɗin na Dr Inusa yace su zauna, momy dai sai binsa da kallo take ta matsu ya faɗa mata halin da ɗan ta yake ciki suna cikin, suna zauna wa suka fara gaisawa sannan yace "Madame nasan baki sani ba amma nasan kin koda a bakin mijin ki ne kunji sunana, mu abokan juna ne tun muna yara dalilin da yasa baku sanni ba ni bana wayan zama a nan kuma idan nazo ayyuka sun min yawa ban samu dama na leƙaku bare har mu gaisa shima mai gidan naki sai in yana gari yake zuwa mugaisa har nan asibiti ko ya isko ni ɗayar, shima Alhaji Sadisu haka yake oisko ni asibiti idan naje Maraɗi ai nasan kisan shi, amma shi nasan matar sabida ita ɗin yayar mai ɗakina ce."

"Kema kuma nasan ƴaƴan ki maza da ɗaya daga cikin ƴan biyun nan sabida Alhaji Sumana ya taɓa kawo ɗayar nan tana ciwon ciki an yi katari lokacin ina gari ni nama duba ta, ba tare da na cikaku da surutu ba bari na faɗa maku abinda ke damun ministan namu wato AFREED."

Bai ƙarasa rufe bakinsa ba Ali ya turo ƙofar da sallama ya shigo, cike da sakin fuska ya amsa masa sannan Ali ya ƙarasa gab dashi ya duka yace "Dady ina kwana ya aiki."

Dr ya saki murmushi tare da shafa kan Ali sannan yace "Lafiya lau alhamdulilah ashe ɗan uwan naka ne ba lafiya."

"Eh wallahi dady"

"To miyasa a lokacin da kuka kawo shi baka zo ka faɗa man ba tunda ai kunsan ina gari dan shekaran jiya ma ranar asabar a nan kuka yuni ko?"

Ali yace "Wallahi dady duk na rikice na marasa mizan yi shiyasa na kasa tuna ma da kana nan."

Dr Inusa yace "To shikenan tashi ka zauna insha Allahu ɗan uwan ka zai samu lafiya duk ku kwantar da hankalin ku."

Ali ya nemi guri ya zauna yana jiran ji ƙarin bayani.

Dr yayi yasu rubuce rubuce a saman wata pepper sannan ya ɗago yace "Ba komai bane ke da mun AFREED sai tunani damuwa wanda haka yayi niyyar saka mashi ciwon zuciya sedai an riga da an shawo kan matsalar insha Allahu ciwon ba zai ƙara tashi ba sai wani abu daga Ubangiji dan sosai aka shawo kan matsalar, sai kuma taimakon da kuma zakuyi mashi shine a daina barin shi yana zama shi ƙaɗai hanka na bada gudunmawa wajen saka shi tunani ko da bai zai yi maku magana ba ku dinga zama kusan da shi kuna hira ta wasa da dariya tun yana shiru har sai yakai ya saka maku baki a zancen ku, kuma wajen aiki ya daina zuwa har na tsayi sati biyu saboda ya ƙara warware wa, a daina barinsa cikin damuwa kuma a guji abinda zai ɓata masa rai har na tsawon watanni shida kuma kada a yarda ayi wani abu da zai tayar masa da hankali sosai har na tsawon watannin nan da na an bata sannan yanzu idan har ya ji sauki kada ku matsa masa dole sai ya faɗa maku abinda ke damun sa dan baiyi niyyar faɗa ba kuka sa shi dole, zai iya shiga damuwa kuma a kuma ƴar gidan jiya ciwo ya dawo sabo idan yayi niyya shi zai faɗa maku da kanshi cikin lalama, idan aka yi haka insha Allahu komai zai dawo normal da ikon Allah.

Sai a lokacin momy ta sami damar magana tace "Mungode sosai wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba dajin cewa zai samu lafiya kuma an shawo kan matsalar, godiya muke Allah ƙara ilimi."

Ameen Dr Inusa ya faɗa sannan ya ƙara da cewa "Zaku iya shiga ku ganshi nasa an tanadi special chambre sabida shi ni nace ka wanda ya ƙarɓi kuɗin komai a wajenku har na ɗaki da Ali yaje biya, sabida nima ai ɗana ne, idan na masa aiki ai kamar nayiwa yaro na ne fata na dai Allah bashi lafiya."

A tare suka amsa da ameen sun Fariya dai sun zama ƴan kallo sai bin kowa na office ɗin suke da kallo sun ƙasa magana da sosai ɗan dattijon nan abokin dady ya birgesu sabida yanda suka lura ya ƙare da aikin kuma daga gani baida matsala wayis ne ba ruwan sa da ɗaukar kai duk da arzikin da Allah ya masa bai ɗauki kansa wani abu ba, sai ma sauƙin kai da yake dashi sosai, su da suke ganin a na nuna sa a télé (TV) basuyi tunanin za su ganshi mai sauƙin kai haka ba.

Farisa tace kin zuciyarta"Ashe shine ya duba ni da na yi ciwon ciki ni ban ma lura ba lokacin ina halin rashin lafiya, da ace masu kuɗi da ilimi zasu ɗauka cewa ɗaya suke da kowa da duniya ta gyaru."

Farisa na zancen zuci bata masan har su tashi suna niyyar fita ba sai da momy tace mata "To ke mi kike jira?" sannan ta dawo hankali ta bi bayan su.

Shikuwa ya cigaba da duba takardunsa.

Suna shiga ɗakin da AFREED ke kwance a ciki wani kamshi mai ɗadi ya bigi hancin su ga ɗaki tsaf tsaf kamar ba a cikin asibiti ba sedai ace masha Allah a guje Fariya da Farisa suka ƙarasa idan AFREED ke kwance yana baccin wahala da abin sérum (ƙarin ruwa) a hannu sa kwana yake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, duk suka riƙe masa hannu suka fara kiran "Yaya yaya tashi daga bacci kayi mana magana dan Allah ko faɗa ne kayi mana kaji yaya."

Ali ne ya ƙaraso ya katsa masu tsawa tare da cewa "Baku da hankali ne baku ga ya samu bacci ba amma kukeson ta yarda da shi baku san ma yanda akayi ya samu bacci ba amma kukeson sai kun tashe shi maza ku matsa daga nan."

Da sauri suka ja da baya dan sun san Ali bai taɓa masu irin haka ba yanzu ma sun san da dalili duk sai suka nemi kujera suka zauna momy ta kalle su ta girgiza kai tana murmushi a ranta tace "Yau fah ba zaku gane kan Ali har in ba gani yayi ɗan uwan na nasa ya buɗe ido sun koma gida lafiya mai ba." Sannan ta ƙarasa ta zauna kusa da AFREED tana kallon fuskar da bakin sa kamar zai yi magana

Suna a haka Dr Inusa ya shigo da magungunan da yada ce AFREED ya dinga sha har sai sun ƙare Ali ya miƙawa sannan yace "Nan da awa biyu zai faraka insha Allahu sannan zai ji sauƙi sosai dan haka kada kuyi magana sosai har sai ya tashi dan gaban kansa, su kuwa wa'inan magungunan idan ya tashi abashi wani abu mai ɗan nauhi ya ci sai ya sha."

"Ok dady mun gode za ayi yanda kace."

Murmushi Dr Inusa yayi ya ce "Ku daina gode man ai nima ɗana ne."

Ya juya zai fita daga ɗakin har ya kai bakin ƙofa ya buɗe sukayi kiciɓis da dady zai shigo wanda dirowarsa kenan garin, gama hannu sukayi suna dariya tare da gaisawa sannan suka koma daga ciki a tare."

Su Fariya a na ganin dady sai aka shiga farin ciki da gudu suka taso suka rungume shi shima ya riƙe su sosai suna mashi sannu da zuwa Ali ma ya taso ya ƙara so inda suke a tsaye momy kaɗai ke zaune tana kallon su tana sakin murmushi."
Chapter 49 · 0% Book details