← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 69

Sashe 15

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka ya shigo ya sameta yace tare da murmushi kwance a fuskar sa"Arahamat sarkin aiki kedai baki gajiya da aikin d'akin nan baida komi amma kuma dan kiba kanki wahala sai kin k'ara gyara shi dama tunda na tardo d'akin tsaftsaf nasan kece me gyaran Allah dai ya maki albarka ya baku miji na gari keda 'yar uwarki dan nasan itama yanzu ta girma. Amma ya naga banganta ba alhalin ga Tanti Fatima nagani?"

Cike jindad'i tace "Ameen yayamu abin k'aunar mu godiya muke baka jin wani irin farin ciki danake ciki ba yau duk sai nake jin duk duniya ba wanda ya fini farin cikin nayi farin ciki sosai da ganin ka yaya har narasa ya zan nuna farin ciki na, Jannah(sunan k'anwar Arahamat) itama tanan zuwa jibi makaranta ne ya hanata biyo Tanti wallahi yaya kazo lokacin dana ke mugun buk'atar ka bar na barka ka shirya kamin na kawo maka abinda zakaci sai nazo muyi fira sai ka k'arasa bani labarin ka da Canada."

Tana gama fad'ar haka tashi tare dayi tsale ta gudu abinta, murmushi yayi da yasa har fararen hak'oren sa suka bayana sannan ya nufi gun da kayan sa suke ya ciro kala guda yasaka sannan ya d'oki tapis ya shinfid'a ya tada sallah.

Arahamat na dawowa tashigo masa da kulolin abinci har guda uku da kallo ya bita sannan ya fara bud'e kulolin yana ganin abinda ke ciki guda d'atacan da kalin turawa ne da yaji kayan had'i su kwai su tomatir su mayonaise su albasa su maggi sosai dai ya had'u guda kuwa perpesun kaji ne a ciki sannan guda kuwa farar shinkafa da taji decoration k'ara kallon ta yayi sannan yace "A ina na kika sami abincin keda baki fuce minti 15 ba da fita a d'akin nan ko nace ina kika sami kud'in haka."

A shagwabe tace "tace yaya wanan dankalin turawan dama tanti ta zo dashi da yawa da zata zo tun d'azu Ufadi ta dafaya dan muci da rana kuma sai ta fasa tace sai dare shine na d'ebo na kwalla maka shi yanzu, wanan perpesun kuwa shima tanti ta bada kud'in aka sayo kajin sabida Ufadi tace mata daginta dake tchirozerine nanan zuwa sabida ka su zo su tardo gidan ba abinci idan su kwaso yinwa shiyasa tanti ta bayar a ka siyo Ufadi ta dafa masu, shine tace na d'iba maka na kawo ma."

"To nagode sosai amma miya faru naga bak'i sosai a gidan nan naga ha dagin Abbu ma sunzo."

Murmushi tayi tana sun ne kanta k'asa tace nima yaya bansani ba ka tambayi Tanti Fatima sai ta gayama ka nidai banda labarin komi nima ganin su kawai nayi."

"Anya gaskiya kike fad'a min kuwa Arahamat ban fa sanki da k'arya ba amma dai bari zan tambayi Tantin."

Jawo kulolin abinci tayi ta fara zuba masa ta tura masa gabansa fara ci yayi sannan yace "Ke bazaki ciba."
Tace "A'a yaya ni fah a k'oshe nake kaci abinka."

Murmushi yayi sannan yaci gaba da cin abinci sa suna fira, tace "Wallahi yaya idan na kalle ka sai naga kamar mafarki nake amma da nayi maka magane ka mayar min sai na yarda da zahiri ne ba bacci nake ba yau dai ina cikin farin ciki mara misali alhamdulilah Allah nagode ma da ka dawomin da yayana, wa ya isa ya min haka ko ya saka ni cikin wanan farin in ba kai ba ya ubangiji alhamdulilah alhamdulilah wallahi yaya sai nakeji kamar da ummu (mahaifiyar su Arahamat da ta rasu) ne nake fira a yanzu ina maka kallon ummu na yaya shiyasa farin cikina ke k'ara k'aruwa Allah ya duba maraicina shiyasa ya dawo min dakai adaidai wanan lokacin da nake da bukatar uwa a tatare dani Alhamdulilah bazan gaji da gode masa ba."

'Yar siririyar dariya ya saki sannan yace "Wallahi petite soeur nafi ku farin ciki au moins ku kuna gani Abbu da tanti Fatima ga Ufadi to nifa ba wanda nake gani sai jar fata amma gashi yau gani a tare daku ai kinga farin ciki na yafi naku bance ba yau zan iya yin kwana sabida farin ciki Allah shine ya cancanta a gode mawa dan haka Alhamdulilah."

"Hakane yaya bari na barka ka huta kamin ka k'arasa mana labarin ka."

Mikewa tayi tare da barin d'akin ta na jinta cikin matsanancin farin ciki. Tana fita ya k'ara maida hankalin sa ga cin abincin yana gamawa ya fito daga d'akin ya wanke hannun sa tare da kuskure bakin sa ya nufi d'akin da aka ta nadarwa Tanti Fatima da sallama ya shiga inda ya tardo su ita da Ufadi da Arahamat ana kuskus da kallo suka bishi har ya nemi guri ya zauna sannan ya d'ago ya kalle su yace "Ufadi kuskus d'in miye ake banda ni? nima asaka ni a ciki man tunda yanzu Allah yayi dawowa ta."

Murmushi Ufadi tayi kamar ba itace mai galazawa Arahamat ba tace "Ai kam wanan magana sirine tsakanin mu kabari idan ka k'arasa bamu labarin ka sai d'an sanar da kai kad'an daga cikin wanan sirin karka damu ai dole a sakaka a ciki, amma kamin nan kaje ka kwanta ka huta ka kwaso gajiya."

"Ufadi ai banjin bacci ne wallahi sabida farin ciki nakasa yin bacci har kwantawa nayi da naga bacci ba d'okata zai yiba na taso na fito."

Tanti Fatima tace "Hakane yanzu ci gaba da gayama na yanda akayi har kazo gida muji kuma ma har ka gane hanya ka kawo kanka."

Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fara da cewa "Wanda ya kaini asibiti shi yaje ya samin sauran manyan akan yi shawara cewa su saka gwamnatin Niger ya dinga ma yan makarantar daake turowa k'asashen waje biya sabida in iyayen wasu na da hali wani na shi iyayen basuda. Haka dai sukayi ta taunawa har suka tsaida magana guda akan zasu tintib'in gwamnati, To Allah da ikon sa sai da suka tintimb'i shuwagabani Niger da maganar sai suka amince da shawarar haka aka dinga bamu 50000 duk wata kuma nasami wata restaurant ina masu aiki shara da guga suna biyana a haka nake samin kud'in nike wasu yan buk'atu na sabida a restaurant din da nake aiki nan suke ban abinci wajan kashi uku a yini, kuma ina tara wasu kud'i da nake b'oyewa a cikin kayana sabida na d'aukar wa raina cewa dana tara kud'in jirgi baro garin zanyi, a haka har muka koma karatu abokina shima ya dawo, kwanci tashi ba wuya a wajan har na cika she kara uku a garin kuma a lokacin ne na tara kud'in jirgi da zan dawo, daran wata alhamis nake gayawa abokina da yanzu nasami kud'in jirgi gidan zan koma, sai yake cemin idan kaje gidan zaka dawo ne nace masa a'a ina tafi na tafi kenan, wace Ibrahim kada kayiwa karatun ka haka kuma shekara guda ya mana saura mu k'arasa sannan idan kajewa Abbu gida a haka ba kai ba diploma ba degree ba wata takada da zai nuna masa cewa ka k'arasa karatun gaskiya ba zaiji dad'i ba kuma fushi zaiyi dakai, sabida dan ga sami sheda me kyau ne da karatu mai zurfi yasa ya tilasta maka zuwa gari nan kuma dan katsaya da k'afafun ka ne ba sai ka je nema wajan wani ba kuma dan ka talafawa k'ananka mata da shi kanshi Abbu d'in tunda ba k'arfi da shi ba, ga shekarun da kayi ba kaje ganin su kuma sai ka koma masu ba wani labari mai kyau sannan kuma shekaru ukun da kayi sun tafi a banza kenan?

"To da ya fad'i haka sai naga yayi gaskiya kuma naga shima tun farkon zuwan mu da yaje hutu bai k'ara zuwa ba sedai yayi waya dasu, sedai baban tashi hankali na shine wani sa'in idan na kwanta bacci sai nayi mafarkin Arahamat tana kuka ta na rik'o hannu na amma kuma idan zan mata tambayar duniyar nan baza ta fad'a min abinda ke sa ta kuka ba sedai ma idan taga zan takura ta da sai ta fad'a sai ta tafi ta barni hakan ba k'aramin tayar min da hankali yake ba, sedai kawai nayi ta yi mata adu'a sabida, kuma sai nake tunanin duk lokacin da take cikin damuwa ne ko aka mata wani abun ya kesa ina marfakin ta tunda ba kulum nake yi ba. In tak'aice maku dai a shekara da na kamala karatu na a shekara ne ina shirye shiryen zowa gida wata babba ma 'aikata ta d'aukeni aiki sanadin nasami sakamako mai kyau fiye da nakowa nine ma nayi na farin gashi fannin da na karanta shi sukeda buk'ata amma nak'i mutanan sunyi sunyi har linka min albashi sukayi amma nak'i saida abokina ya lalab'a ni tareda k'armin kwarin gwiwar cewa zai jirani har nayi shekara guda ina aikin sai mu dawo gida tare kuma yace idan nasamin kud'in shekara guda zaifi min sabida da kud'in shekara guda yace zan iya bud'e wani kasuwaci da zan tallafi dangina da shi ya fad'a min hakane sabida gani yayi duk sanda aka nemi nayi wani abu nak'i to da ya kawomin zancan dangina shikenan ko minene zanyi."

Sai da ya d'an nisa kamin yaci gaba "A haka dai na yarda ba dan naso ba. Bayan shekara guda da wata biyu da kama aikina, nayi niyar zowa gida sabida nayiwa kaina alk'awali yanzu babu abinda zai hanani zuwa gida sai wani ikon Allah ban fad'a wa abokina k'udirina ba har saida ya gani ina had'a kaya ya ke tambaya ta lafiya nace ni tafiya ta zanyi wace."

Yace "Shine baka gayamin ba, ba munyi alk'awalin tare zamu koma ba?"

Nace "Gani nayi duk ina fad'a maka tafiya ta hanawa kake yi shiyasa ni kuma wanan nayi alk'awalin ba wanda ya isa ya tsayar dani daga abinda nayi niya gaskiya nayi kewar dangina nesa ba kusa ba."

Murmushi yayi sannan yace "Karka damu abokina nima wanan karan ina bayan ka sedai wani hanzari ba gudu ba shin kasanidan ma'aikatar da kake aiki suka san tafiya zakayi kuma bazaka dawo ba zasu iya bin duk hanyar da suke so su hanaka komawa ba, in jindai ka shirya abinda zaka ce masu ko?
Chapter 15 · 0% Book details