← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 69

Sashe 6

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khairat tace "ah kenan sai muntun ya k'arasa karatu ne ya girma kuma ya isa aure? to tun yuri garama ki farka daga baccin da kike ah to, kingan ninan idan ahmad yace zai kawo kudin aure na a gobe, to wly yarda zanyi ah to mi kake yi da karatu ga sunnah manzon Allah saw, idan naje gidan nasa sai na karasa karatun a can, ke ni daga na k'arasa wanan shekaran shikenan bawani karatu da zanci gaba da shi, kedai rik'a min adu'a na karbi licence d'ita shekara nan shikenan nida école (school) munyi ban hannu sai d'akin miji insha Allah" ta fad'a tana dariya. "To ameen grande Soeur Allah ya taimaka kuma ya kawo miji na gari musha biki ranar akwai casu in Allah ya yada."

"Hum kinji kamar da gaske, ga ki nan wa ta irin ustaziya dake wane casu za kiyi gayi ne kawai kike" ita dai AFREEN murmushi kawai tayi bata ce komi ba.

"Yawa 'yar uwa na ma tuna kisan wai dazu na dawo daga gidan anti fauziya na had'u da wani a hanya wai shi abdul majid bari na nuna maki photon (pic) shi, yanzu ya turo min a whatsapp wai so na ya ke da aure kuma yace min ba garin nan yake ba dan tahoua ne shi, kedai ban matsaya na saurare shi da kyau ba Kawai nace mishi ni gaskiya ban nan gayin fira a titi sai yace na shigo motar sa ya ragemin hanyan nace nagode, babu yanda baiyi ba kan na shiga motar sa wai ya karaso da ni gida nakiya dad'a daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki, ban san sa ba, ban taba gani sa ba shikenan sai na d'ane motar sa ya kawo ni gida kinji kamar wace bata da daraja da kamun kai, ko bama haka nan ba, in fah yana kawo ni daidai papa nazo wa ya gan ni to sai yaya, Lale yau da papa ya kakarya ni wlh." Khairat ta fad'a tare da shiga ma'adanar photo na wayar ta.

AFREEN tace "Lalai kam gara dai daba ki shiga ba ko ba dan ka papa ya gan ki ba ai se ka nema ma kan ka daraja."

Ta fido photon ta nuna wa AFREEN tace "kin ganshi fah sis?," "lah anti shima kyakyawa amma fah ya ahmed ya fi shi kyau, to anti ya batun ya ahmed naga kuma kinyi wani Abdoul majid, ko kun b'ata da shine?" AFREEN ta tambaye ta a tak'aice. Khairat tace "ah haba ahmed fah shi ne k'ark'ashi zuciya ta shine na ke so da kauna, wanda nake mafarkin ya zaman miji na insha Allah taya ma zamu b'ata, sedai wani inkon Allah kuma kawai dai na yada na bashi numéro (number) na ne sabida baka san yata Allah zata kasan ce da kai ba, tunda bakada masaniyar ko waye mijin ka ba sai wanda Allah ya zab'a maka."

''hakane kam rabin raina Allah kawo da mafi alkairi," Khairat ta amsa da "ameen petite Soeur, tashi kije kiyi wanka kiyi change kizo ki kwanta kinga akwai école gobe in Allah ya kaimu, idan kika dawo makaranta gobe mun karasa firar insha Allah."

Tashi AFREEN tayi ta nufi douche (toillet) wanka tayi tare da yi brossage din baki ta dauro alwala ta fito, direct wajan coiffeuse (dressing mirror) ta nufa tayi abinda yaza ma mata al'ada kamin ta kwanta, sannan ta wuce gun armoir ta ciro kayan baccin ta, sabida a d'akin ko wane cikin su akwai kayan d'an uwan shi a cikin nashi kayan sabida gudun irin haka, kamin ta dawo saman gadon ta kwanta tuni Khairat tayi bacci haura wa tayi itama kan gadon ta fara karanto adu'o in bacci tana idawa tayi bismillah ta kwanta kusa da Khairat, bata wani d'auki lokaci ba bacci ya k'washe ta.

K'arfe biyu daidai na dare AFREEN ta farka da adu'ar tashi daga bacci a bakin ta, sauko wa tayi daga kan gadon ta nufi toillette, shiga tayi ta wanke baki, ta dauro alwala, ta fito ta canza kaya ta d'auko hijab da darduma ,saka hijab d'in tayi tare da shinfid'a darduma ta koma bakin gadon kusa da Khairat, ta dan ja hannun ta tace"anti tashi ko yau ba zakiyi sallan ba ne."

Khairat ta buda idon da suka mata nauhi tace" s'il te plait AFREEN laisse moi dormir wly j'ai sommeil ("please AFREEN let me sleep wlh I'm sleepy)" "dan Allah Anti tashi mana" mtsss taja dan k'armin tsaki sannan tace AFREEN dan Allah ki barni wlh yau bacci nake ji sosai je kiyi taki kawai" daga haka AFREEN ta nufi kan darduma ta tada salllah, sai da ta kai karfe ukun dare ta na nafila kamin take sallame wa gabada ta mike ta ninke darduma da hijab ta mayar da su ma'adanar su, ta dawo saman gadon ta kwanta, ba itace ta farka sai wajan karfe 5:15, tashi tayi ta nufi toillette ta d'auro alwala ta fito ta nufi gadon ta tayar da Khairat, tare da gabatar da raka'atanul fijir sannan tayi sallah asuba, kur'ani' ta d'auko ta fara karanta wa, sai 6:30 kamin ta koma toillette minti 10 ta fito d'aure da serviette (tawel) cikin k'ank'anin lokaci ta shirya tsaf da ita cikin riga da jupe (sket) na atanfa da suka mata matuk'ar kyau macha Allah, ta ciro hijab tasaka da nikaf ga hannu, da jakar makarantar ta tace ma khairat, dake zaune har lokacin kan darduma.

"anti na tafi, sai na dawo" Khairat ta dago ta kale ta tace to a dawo lafiya Allah ya tsare" ta amsa da "ameen" tare da fice wa daga d'akin.

Tana fita ta nufi escalier direct d'akin mahaifin su ta nufa, tashi ga da sallama, yana zaune a falo kan darduma da kur'ani a gaban sa da alama karatu ya gama zauna wa tayi kusa da shi tace "papa ina kwana antashi lafiya" papa ya amsa da "lafiya lau AFREEN, har kin shirya, yau dreba zai kaiki ko kuwa da kanki za kiyi conduire (driving)?" tace "a'a dreba zai kaini yau bana jin conduire d'in" papa yace "ok to kinyi kari kuwa" " a'a amma yanzu zanyi kamin na wuce makaranta" papa yace "to shikenan ki samu fah ki kayar kamin ki wuce, karb'i kudin makarantar ki" papa ya fido da 1000f ya mika mata yace to a dawo lafiya" AFREEN tace "ameen papa na gode.

Daga nan ta nufi dakin mahaifiyar su ta gaida ta a gurguje ta fito sanadin gani da tayi ta kusa makara. kasa ta sauka tayi dakin umma ta gaida ta, umma ta watsa mata harara tace "in ban kwana ba kin gani kinibabiya Kawai nace ban son wanan gaisuwar dole ne sai kin gaida ni koni uwar kice" AFREEN batace komi ba ta juya zata fita wata yarinya da ba zata fuce 14 ans (years) "tace dan Allah anti AFREEN nazo ki wuce dani makaranta tunda ke da yuri kike zuwa idan natsaya jiran su marie zasu sa nayi retard (lati) dubi fah har yanzu ko shirya wa ba suyi ba bare ma ayi batun karyawa", da murmushi AFREEN ta juyo tace to ke kin karya ne" girgiza kai tayi tace "a'a yanzu zan karya anti" AFREEN tace "to shikenan d'auko jakar ki sai ki fito mu karya tare sai mu wuce" yarinyar tace "to anti gani nan zuwa."

AFREEN na fita yarinyar ta juya ta dubi mahaifiyar ta tace "umma gaskiya abinda kike yiwa anti AFREEN ba ki kyautawa, du gidan nan akwai me biyo ki har d'aki ya gaida ki inba ita ba, ko kin taba gani anti Khairat ta shigo dakin nan ta gaida ki, sedai idan kun hadu a falo, yanzu ma da ta gane halin ki ta daina gayar dake gaba d'aya, sabida irin wanan abin da kikewa anti AFREEN, amma ita anti AFREEN nasan da komi zaki mata ta ba zata daina gaida ki ba."

Wani irin mugun kalo umma ta watsa ma yarinyar tace "kinsan wlh Zeinab ki fita ido na, na rufe ke wace irin banza yarinya ce da ba ta san ciyon kanta ba ke dai ba ki kaunar ki ga an taba wacan munafukar yarinyar, to wlh ki kiyaye ni Zeinab, ko nuna maku da ake a gidan nan a fi son ta daku ko ciyo abin bai maki, to wly ki shiga taitayin ki, ki dawo hankalin ki ma in kina dawo wa."

Simi simi yarinyar da aka kira da Zeinab ta fice d'akin ba tare da ce ma umma komai ba.

AFREEN na fita daga d'akin umma ta shiga na Tanti ta gaida ta Tanti ta amsa tace "AFREEN har zaki makaranta."

"Eh" AFREEN ta fad'a a tak'aice tanti tace k'arbi zumu ki sha" tanti ta d'auko zumuwar ta mik'a mata, karb'a tayi tasha cuillère (spoon) guda ta mayar mata da sauran ta fita, take gun cin abinci ta nufa idan ta tardo Zeinab gama karyawa ta na jiranta, thé (tea) kawai ta had'a ma kanta tasha suka fice daga falon, direct inda dreba yayi tsaye da mota yana jiran su suka nufa, gaida dreba suka yi sannan Zeinab ta bude masu gidan baya suka shiga dreba ya tayar da motar ya doshi k'ofar fita daga gidan mai gadi nagani haka ya tashi ya wangale masu tamgamemiyar k'ofar gidan ya fice da motar.

Shiru kake ji cikin motar ba me cewa komi, can dai Zeinab ta katse shirun tace " anti dan Allah ki yi hakuri da abinda umma ke ma ki wly watarana zata gane ta dena maki hakan" AFREEN ta juyo tayi d'an murmushi me sauti wada seda kyawawan fararen hakoran ta suka bayana tace "kar ki damu k'anwata ni ban taba rike umma a zuciya ba, sabida nasan watarana sai labari bai komi kinji, itama umma uwa take a gare ni ,dan haka ni ba d'auki abinda take min a wani abu ba, ki ma daina min wanan zancan, in kina ban hakuri sai na ga kama kin nuna min umma ku ka dai ta haifa ban da mu," "anti wlh ba haka nake nufi ba" Zeinab ta fad'a da sauri, daidai nan a ka kawo k'ofar makarantar su Zeinab dreba ya ja ya tsaya, Zeinab ta bude k'ofar motar ta fita.
Chapter 6 · 0% Book details