← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 69

Sashe 66

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su na zuwa asibiti urgence (emergency room) akayi da ita cikin gaggawa, Hasina da maman da zeinab sun kasa zama sai kai da kawowa suke, papa da Fahad da Imran kusan ɗakin da aka saka a tsaye sauran suna zaune duk sunyi tagumi, duk sun rasa abinda ke masu daɗi, banda tanti da a fuskar ta ne kaɗai ta nuna kallar tausayi, amma a zuciyarta cewa take Allah sa tayi paralysé (ciwon shanyewa ɓaren jiki).

Wajen awa uku likitoci su kayi akan AFREEN sannan wani docter ya fito suna ganin su duka suka nufi shi suna tambayar sa ya ake ciki, murmushi docter yayi sannan yace "Ku kwantar da hankalin ku yarinyar ku tana lafiya kawai tarin damuwa ne ya mata yawa sai jinin ta da ya ɗan hau kaɗan amma da ikon Allah mun samu mun daidaita shi yanzu babu wata matsala komai normal, dama abinda yasa muka jima a kanta numfashi ta ne yayi mugun bamu wahala kamin musamu ya daidaita saboda yayi nisa sosai ga barin jikinta to amma da yake Allah ya nufa ta da sauran kwana a doron duniya kunga asamu an shawo kan matsalar, yanzu haka lafiyarta lau sai dai rashin ƙarfin jiki, kuma zai daina ne a sani sanu sai dai munyi mata allura bacci, ta samu bacci karku damu amma ba zaku samu ganin ta yanzu ba sai ta farka dan tana da buƙatar bacci, abinda kuma zai hana a baku sallama a yau shine munason muka yanayin jikinta zuwa gobe da safe sai na baku sallama inshallah." Doctor na faɗar haka yayi gaba abinsa.

Duk wanda ke wajen saida ya ɗaga hannun sama ya faɗar alhamdulilah tare da murmushi kwance a fuskar sa amma banda tanti, sai a lokacin maman da zeinab da Hasina suka ɗan kwantar da hankalin su har suka nemi gun zama suka zauna tare da yi mata addu'a, a nan maman ke tambaya Hasina mai ya faru har ta shiga wannan halin.

Sai a lokacin ta tuna cewa ashe dole a tambaye ta miya faru ita kuma bata shirya abin faɗa dan haka sai tayi kamar bataji ba abinda maman tace ba, har sai da maman ta sake ta tambayar, ta ɗago tana in ina sannan ta daure ta gyara maganar tare da cewa "Maman babu abinda ya faru daga fa muna cikin fira tana faɗaman cewa ita fah bata son barin gidan su bare garin baki ɗaya, gashi nan har Niamey za'a kaita alhali duk dangin ta suna maraɗi shi kenan sai ta fara rera kuka na shiga rashin ta ai fah da kukan yaci karfin ta sai kawai gani nayi ta sulale a kan jiki ta zube saman bed sumamiya."

"Maman da bata fahimci ƙarya Hasina ta sheƙa mata tace "To ba dole tayi hakuri ba, ni da aka kayoni gidan mahaifinta tun daga Agadez har Niamey da kuma daga Niamey ɗin muka yo nan mi yasame ni ko wa nasani a cikin garin banda mahaifin ta, sai ita taki yarda da hukuncin Ubangiji?

Ita dai Hasina bata ce komai ba, sai zeinab da tace "Maman ita ma fah zata jure kawai kun san hakan sai ta faru kuma idan ta samu watani ai ni cen gun ta zan koma dan ni idan bata gida bana iya zama gaskiya."

Harara maman ta sakar ma zeinab sannan tace "Kun dai ji da shi keda ita ai kusan halin ku guda." Murmushi kawai zeinab tayi.

Ba'a wani ɗauki lokaci ba ta farka suka runtuma duka cikin ɗakin suna mata sannu duk sai taji ba da taga yanayin iyayen duk hankali su a tashe saboda ita da sauri ta kamo hannun mahaifin tace "Papa kuyi hakuri na tayar maku da hankali wallah je pas l'attention de le faire kawai Allah ya kawo.

Murmushi papa ya sakar mata sannan yace "Karki damu farin ciki family sadisu, dama hakan zata iya faruwa yanzu abu mahimmanci shine Allah ya baki lafiya."

Murmushi tayi tare da faɗin "Ameen papa."

Kowa hankali shi ya kwanta gani da sauki sosai, ƴan uwa da abokan arziki sai shigowa suke suna duba har da Adamu ƴaƴan papa da matan sa da ɗiyan ida Maryam cousin ɗin ɗiyar Abba Adamu Wada suke kusan sa'a ɗaya ita ta zo duba ta har ta ce ita wajen AFREEN zata zauna, idan ita Hajiya Zakiya kaka su da ta biyo Adamu ta zo tana ta masifa ta cikin gida amma a kasa sanar da ita jikata ba lafiya da so akayi sai ta mutu kamin a sanar dani ko babu dai wanda ya tamka mata."

Wasu motoci ne guda uku masu masifar naga sun kun kai a cikin asibitin suka nufi gun parking sukayi daidaita suka tsaya da sauri naga direban motar da tafi kowace mota haɗuwa naga ya fito yaje ya buɗe kofar baya, wata kyakkyawa ƙafa naga an fara zurowa sannan a ƙara fido da ɗayar kamin mai ƙafafun ta fito baki ɗaya, baki da hanci da na saki tare da waro idanu ina mai furta tubarukallahu ahasanul kalikin ne Masha Allah saboda ganin wata haɗaɗiya kyakkyawa nagartaciya mata da tafito daga cikin motar nan kai cewa ma matar nan na da kyau zai iya zama zagi ne wallahi faɗi tana da kyau da tsarin halitta zan iya ƙarasa littafin nan ban gama bayani kyau da tsarin halitta irin nata ba, mata wata irin class lady ba'a ma iya maga.

Inna ganin matar duk da bansan ko ita wacece ba naga wata irin muguwar kama da suka da AFREEN da kuma da kyau da komai ita ce AFREEN ta dabo abin ba'a cewa komai, tana ida fitowa wata kyakkyawar yarinya da bata wuce shekara goma ita ta fito wada kana kallon zaka sak mahaifiyar AFREEN, sannan cikin ɗayar motar wasu haɗaɗu samari maza suma suka fito ɗan bai zai wuce shekara 28 years ba ɗan kuwa zaiyi 25years ga su masu ga su farare tass kamar ka kwontala jini ya fito amma duk hasken basu kai matar nan ba wada nake tsammanin mahaifiyar su ce, gani nayi suna nufar shiga cikin asibitin noma nabisu a baya aikuwa zaton ya zama gaskiya dan kuwa ɗakin da aka kwontar da AFREEN nan suka shiga.

Suna shiga da sallama AFREEN da ke kwance babu lafiya da ƙarin ruwa a hannun ta tanajin sallama matar ta juyo da ƙarfi daidai matar na ƙarasa shigowa ai kuwa AFREEN mantawa tayi da wani ciwo da wata jinya da take ta ta cire abin karin ruwan babu wanda ya lura saboda suma idon na kan matar nan da ta shigo ai da gudu AFREEN ta diro daga saman gadon marasa lafiya ta nufi matar dake ƙoƙarin karasowa gunta, AFREEN na kai gun matar ta yi wani tsalle ta rukunkumeta kamar ba mara lafiya tana faɗar oyoyo momy jannah oyoyo momy na ita, sai wannan lokacin na gane cewa ashe ƙanwar Arahamat ce jannah dake Dubaï ta aure matar docter Inusa abokin papa AFREEN.

Ashe nan AFREEN tayi gadan kyau idan ka ganta ka ga AFREEN zakace itace ta haifeta ba Arahamat ba dan gaskiyar kamar su ta ɓace in badan ita ba mace mai shekaru da zaka iya cewa yan biyu ne ita da AFREEN, murmushi take ta saki kamin ta ɗago AFREEN da rugumar da tayi mata tace "Ma fille (my daughter) irin wannan gudu haka kodai lafiyar ki lau."

AFREEN ta shagobe fuska ta ce "Momy na dai ji sauki ne."

Momy Jannah ta rabata da jikin ta jawo hannun ta nufi gadon da ita ta zaunar da ita ta tace "Kinga zauna ki ƙara hutawa keda ke jinya kikayi irin wannan tashi haka ba sai kikara jima kanki ciwo ba Ni da nakeson na kuma dake kida yanzun mu tafi cen musha hira kokuwa."

"Hakane Momy ai kafata kafarki bazan ƙara koda awa ɗaya a asibitin nan ba."

Murmushi Momy Jannah ta yi sannan tace "Inshallah kuwa yanzu za'a baki sallama sai muje gida na ƙarasa maki traitement."

Daga nan Momy ta ɗago ido ta kalli mahaifiyar AFREEN tace "Aunty ina yuni mun same ku lafiya." Tana murmushi tana magana

Maman ta kaɓe baki tace "Ah sai yanzu kika ganni da kika shigo ai ɗiyar kaɗai ki yiwa magana alhalin ba ita ɗaya ba ce cikin ɗakin."

Murmushi Momy Jannah ta ƙara saki tace "Ai ita ke jinya ni kuwa ita nazo dubawa saboda muna sauka a cen gidan naku aka ceman kuna nan asibiti ɗiyata ha ba lafiya shiyasa nawo azama dan na duba lafiyar ina dalilin kun samani IIyarinya rashin lafiya bako tausayi a matsayin ta na amarya ai ya kamata a dinga lalaɓa ta har ai kai gidan ta lafiya, amma tunda nazo yanzu ai shikenan zan ga wanda zai dinga takurata."

Maman tace "To ai da dokar ta kike ku tafi cen garin ida kika fito ba sai har auren a fasa ba."

"Haba Aunty ai fasa auren nan sai bayan raina wallahi yarinya ta sai ta shiga gidan ministre komin bakin cikin mutun wallahi."

Maman najin haka ta san magana ce ta fara yadawa shiyasa bata ƙara ce mata komai ba."

Momy Jannah na ganin yayar tata bata ce komai sai ta juya ta fara kallon mutanen dake cikin ɗakin ɗaya bayan ɗaya tana sauke idon ta akan tanti, sai tanti taji gaban ya faɗi da sauri ta sauke kanta ƙasa, ita kuwa Momy Jannah tana ganin ta sauke kai ƙasa ta kwalla mata harara a ranta tace munafuka, dan Allah ya bata wata baiwa idan har ta haɗa ido da mutum idan bai da gaskiya to ta na gane hakan a cikin idon idai kai mugun ne ko munafiki to fah sai ta gano ka ɗan kwata kwata baka iya jure kallon ta cikin ido.

Momy Jannah ta maida kallon gun Hajiya Zakiya ta gaida suka gaisa sosai cikin sakin fuska dan Hajiya Zakiya tasan ta tun tana yarinya, sannan ta juya wajen Maryam da Fatima yayan alhaji Sadisu ta gaishe , sannan ta mayar da kallon ta gun AFREEN bata tare da ta gaida umma da tanti ba dan ita Momy Jannah ma ƙaramar mafaɗaciya ba halin da AFREEN ba ɗoko nata ba.

Hasina da zeinab suka gaishe ta cikin sakin fuska ta amsa har tana tambaya ya makaranta ta.
Chapter 66 · 0% Book details