← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 69

Sashe 27

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai papa yace "Haba Sakina jimin kinason hana min ɗiyata ƙarasa cin abinci duk kinsa taji kunya, ai irin su AFREEN har gida Allah ke kawo masu nagartacan miji nagari wanda zai kula da ita ko bayan ba ran mu insha Allahu zakusha mamakin kalar mijin da zaizo mata har gida ba tareda ita kanta ta shiryawa hakan ba."

Tanti tace "Hum to muna zuba ido mu gani tunda ka ƙule mata gidin amma nidai kam dole a rage saka niƙaf ɗin nan sabida so nake na aurar da ɗiyata da yuri ah to."

"Karki damu ai zata sumu ne koda kuwa cikin niƙaf ne shi aure Allah ke haɗa shi kuda ke ƙanin sabida saka niƙaf ɗin da take yi samarin za suyi tunanin matar aure ba haka bane budurwa nawa ke saka niƙaf amma kuma ta sami mijin aure ai Allah ya banbanta mai aure da mara aure ko da kuwa cikin niƙaf ɗin ne za'a iya ganewa." Papa ya faɗa tare da kallon gun da AFREEN take da har yanzu bata ɗago da kanta ba.

"Allah sarki to Allah nuna min wannan ranar da AFREEN zata zo tace anti ga sirikinki nan yazo gaidaki kai ranar kowa sai yaga kwasar shoki aka kara kwashewa da dariya har yanzu dai banda Umma da suka gama ɓata mata rai ƙiris take jira ta fashe, AFREEN ma sai da ta ɗan murmusa

Haka dai suka yi ta raha da farin ciki har aka kammala cin abincin, AFREEN ta ɗago ta dubi mahaifin na tace "Papa anjima inason zanje gidan anti Fauziya na kwana biyu ba mu haɗu ba sai ta waya, idan mun taso daga islamiyya sai na biya tacan daga sai nayo gida."

Kamin papa yayi magana Zeinab tayi "saurin cewa "Dan Allah anti ina zuwa nima na jima bangan taba." da khair ta samu tayi maganar dan tunɗazu take son tayi magana tanason tsoma bakin ta cikin cikin firar da suke amma umma ke hararen tana mata nunin da inta kuskura tayi magana sai tayi maganin idan suka gane ɗaki."

Aikuwa itama umman da sauri tace "Jacan dan Allah da bakinsa san ciwon kanki ba ni anya kuwa Zeinab ba hurhuran ki akayi min a asibiti ba irin wanga abu na kutsa kanka inda ba'asan darajar kaba to dan ubanki babu ida zakije shegiya mai kama da maƙiyan ta kwakwata na rasa yanda akayi baki yo halina ba ko da yake yawan zama tare da masu mugun hali ai dole ki koy........

Bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba papa ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu sannan yace "Wallahi salamatou ki fita daga idona na rufe yanzu gabana kike zagin yarinya nan ta uwa ta uba ko kunya bakiji kuma ko kara babu, in ba abinki ba aikece mai mugun halin babu mai fatan ya yi hali irin naki kuma kaki koma sheganta min yarinya dan ni ubanta gani a kusa, abu na biyu shine sai taje gidan yar uwata dan baki isa ki rabamin kan ɗiyaba."

Dama tunda papa ya fara magana Fahad da Imran suka bar gun haka Safina da Amira da hamida ma su bar gun yayi saura daga maman sai tanti da umma da kuma AFREEN da Zeinab, maman har ta miƙe zata bari yurin papa yace ta dawo ta zauna."

Sannan ya juwo gun su AFREEN yace "Ku tashi kuje daga lokacin zuwa islamiyya yayi kuyi tafiyarku daga can sai ku wuce gidan Fauziyar hada su Safina kuje ku duka kukai mata ziyara."

AFREEN ta kalli papa da murmushin ɗauke afuskarta ta ce "To shikenan papa mun gode."

Yace "Akwai saƙo dana bayawa mamanku nace ta bada aikaiwa Fauziya tunda zaku tafi to ku tafi mata dashi."

Insha Allahu papa AFREEN ta faɗa tare da barin gun itama Zeinab tabi bayan kowa ya koma nasa daƙin umma sakin tsaki tayi tare da barin gun bin ta papa yayi da kallo har ta ɓacewa ganinsa ransa du a ɓace ya juwo da niyar yin magana maman tayi saurin cewa "Dan Alhaji na kada kabari abinda umma Zeinab tayi ya ɓata maka rai idai halinta ne ai ka riga ka saba kuma ina mai tabbatar maka da watarana zata daina dan Allah kayi hakuri ko kaɗan bani kaunar ganin bacin ranka mijina."

Aiko a take papa ya washe baki yana cewa "Allah kuwa sarauniya ta?" ɗan shiyasa nakeson zama a kusa dake kullum kina faranta raina baki bari wani ya bata min shi dan haka kullum nike ƙara godewa Allah da ya banike a matsayin mata aurena."

Haka dai datijawan nan sukayi ta faɗawa junansu kalaman soyayya kamar dai wasu ƙananun yara, Tanti dage zaune wajan da suka gama ɓata mata rai ta sulale ta barsu nan ba tarare da sun saniba dan kuwa su sun ma manta da tana yurin zauna a riga da an tuno da soyayya yarinta.

AFREEN na shiga cikin ɗaƙi komawa tayi kan gadon ta kwanta sannan ta kuma janyo wayar da ta bar datar a kune ne tun da zata fita kumawa tayi cikin group ɗin da ta bari suna hira taga yau duk maganar da suke akan tane nafa itama ta biye masu suna ta fira cikin nishaɗi da farin ciki kamin daga can taga saƙo wata sabuwar number ya shigo mata fita tayi daga group ta koma wajan bakuwar number kamin ta buɗe saƙon sai tayi ta tunanin to wacece ta turo mata da saƙo ta danganta saƙon da na mace ne sabida tasan babu namijin da yasan number ta inba cousins ɗin taɓa kuma sun ɗin ma ba kowa keda ita ba saƙo ukune aka turoma ta ta baƙuwar number.

Buɗe saƙon tayi a take gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta tashi zaune cike da firgici tana ƙara karanta abinda ke cikin saƙon tana ganin kamar ba gaskiya bane abinda ta karanta, cikin ƙanƙanan lokaci jikinta yafara rawa dandanan yanayin ta ya canza ƙarara ake hango tashi hankali a tare da ita bata masan lokacin da wayar ta kubece ta faɗi ƙasa ba saida taji ƙarar faɗuwar ta

Batabi ta kan wayar ba ta faɗa duniyar tunani.

Ga saƙon kamar haka..................................

Ku biyoni don jin wane irin saƙone ya firgita AFREEN har haka
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutun_
_Niger_

Wattpad@nazichou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003

_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_

Page : 25 & 26

Buɗe saƙon tayi a take gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta tashi zaune cike da firgici tana ƙara karanta abinda ke cikin saƙon tana ganin kamar ba gaskiya bane abinda ta karanta, cikin ƙanƙanan lokaci jikinta yafara rawa dandanan yanayin ta ya canza ƙarara ake hango tashi hankali a tare da ita bata masan lokacin da wayar ta kubece ta faɗi ƙasa ba saida taji ƙarar faɗuwar ta

Batabi ta kan wayar ba ta faɗa duniyar tunani.

Ga saƙon kamar haka: *ASALAM ALEIKUM MALAMA AFREEN DA FATAN KIN WUNI CIKIN KOSHIN LAFIYA, NI SUNANA KAMAL A GASKIYA TUN DA NA GANKI NAJI KIN KWANTA MIN DUK DA BAN TAƁA GANIN FUSKAR KI BA AMMA NAJI INA ƘAUNAR KUMA NASAN KE BA MATA AURE BACE SABIDA SAIDA NA BIBIYEKI HAR NAGANO DA HAKAN KO NUMBER WAYARKI SAIDA NA WAHALA SOSAI WALLAHI HAR NA FIDA RAI DA SAMU SANNAN ALLAH YA TAIMAKE NI NASAMU AFREEN WALLAHI BADA WASA NAZO BA NI AUREN KI ZANYI DUK DA BASANIN KAMAN NIKI NAYI BA ZAN ZAUNA DAKE DA KO WACE IRIN KAMA KO DA KUWA DAGA BAYA NA NA GANKI WALLAH KE MAI KYAUCE KO AKASIN HAKA WANNAN BA MATSALA TA BACE, KAWAI ADDINI DA NA LURA KINADA SHI YAJA HANKALI NA GA REKI AFREEN INA SONKI INA ƘAUNARKI DAN ALLAH INA JIRAN JIN HUKUNCIN DA KIKA YANKE DAN ALLAH BANDA SHARIYA MASOYIYATA INA JIRAN JI RA'AYIN KI A KAINA KUMA IDAN AN BAN DAMA NAZO HAR GIDA NA GABATAR DA *KAINA*
*

AFREEN da ta faɗa cikin duniyar tunani a can cikin ƙasan zuciyar take waye wannan a ina ya samu number na ya'akayi yayi bincike a kaina yasan banda aure kuma yasan sunana duk boye kaina da nake saida aka samu wanda zai nemo asalina.

Ƙarar da wayar tane tayi ya dawo da ita duniyar tunani data lula da sauri da duƙa ta ɗauko wayar da ta faɗi ƙasa kamin ta ɗago tana duba screen ɗin ganin me kiran nata yasata sakin wani sanyenyen murmushi a take ta ɗauki kiran ta kara a kunne tare dayin sallama da murmushi ɗauke a fuskar ta, daga ci wayar aka amsa sallamar tare dacewa "Hum sister ashe kina a raye amma kika manta dani har haka?"

Wani murmushin AFREEN ta ƙara saki sannan tace "Haba rabin raina kin san hakan ba halina bane wallahi karatu ne ya ɓatar dani ga na école ga na islamiyya inba dan haka ba ai kinsan ba zan iya mantawa dake ba dan Allah ki hakuri my Fanna kina raina ban manta dake ba."

Daga cikin wayar wada aka kira da Fanna tace "To shikenan my rabin rai ƙorafi ya ƙarɓu nasan da ba zaki manta dani ba to ya kwana da yawa kuma yaushe ne sabkar ku ta tahafiz?"

"Kwana da yawa sai alkairi cœurly (heartly) nan da sati ukune saukar insha Allah oubien tu va venir pour participer (ko zowa zakiyi dan ki halarci saukar)?"
Chapter 27 · 0% Book details