← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 69

Sashe 63

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wata irin mahaukaciyar dariya yayi sannan cikin ƙananan lokaci ya kumtse kamar bashi yayi ba sannan yace "aikin ki ba mai yiyuwa bane saboda yarinya tana yawan neman tsari daga sharin mutum da aljani da kuma shaiɗan saboda kullum cikin addu'a take da saloli nafila da neman kariya wajen Ubangiji sannan ga yawan karanta littafi Mai girma da yin azkar na safe da marece dan haka ko asirin da kika tayi mata na ana saka ranar auren ta a na fasawa ba ita yake ci ba samarin nata ne yakeci, to shi wannan bai masan da batun auren bare ya ace za'ayi asirin a kai, idan anyi sihirin a kai to ba zai ci ba saboda wannan auren fa babu fashi sai anyi shi saboda rantsatsen aure ga Ubangiji kuma akwai alkairi sosai a ciki sa dan haka wahalar da kanki kawai zakiyi duk wajen wanda zakije ba zai iya hana faruwar auren nan ba sabida haka abu guda zan iya maki shine zan baki wani magani kije ki samu ɗanyan kwai ki fashe shi ki ga ma da ɗanyan nama na shanu ki samu anta rago ki yaka a ciki sai ki zuba maganin, ki soya shi sannan ki samu masu ɗuka laya su ɗumka maki da wannan wainar kwan da ki ka soya sai ki saka a pilon da yarinyar ke aza kanta, daga an daura auren za'a barta gida tayi ta zama iyayen ma zasu mance da sun aurar da ita haka iyayen mijin ma ba zasu tayar da maganar ba sedai akwai haɗari idan ha kika yarda wani ya ƙanki lokacin da kike soya wainar ko kuma ki ka saka antar da bata rago ba to abin ne zai juye a kanki ranar da'ake daura auren ke zaki bar gidan ba tare da kin yiwa mahaifin yarinyar wani abu ba zai maki kora kare a bainar jama'a idan kuwa kika tsaya basa hakuri to ina mai tabbatar maki da kanki zaki dinga faɗar abinda kika shuka kamin ki bar gidan, sannan ga kuma wani maganin ki zuba ma yarinyar ga abinci idan taci to mijin nata ba zai taɓa kwontawa da ita ba sunan yin mu'amalar aure ba sedai ta zame masa kamar hoto a cikin gidan amma idan kika bari zata ci abinci mai magani da tayi Bismillah to ina mai sheda maki cewa maganin ba zai ci ba koda taci kuma mijin na kwontawa da ita to ina mai tabbatar maki cewa ke kuwa haukacewa zakiyi hauka kuma na har abada."

Tanti ta jinjina kai tace "Boka ai wannan abin da ka zana mai sauki ne a guna ka ban maganin kawai ka sake min bayani dan zan iya cikin sauƙi ma ba wani tan garɗa."

Da kyau boka ya ƙara kallon ta sannan ya ce "Zaki iya ba'a a son a samu matsala fah."

Tace "Eh zata iya."

Anty hawa da Hajiya lubabatou sai taɓa suke kada ta amsa wannan maganin ya yi tsauri da yawa amma ina, tanti idon ta sun rufe bataji kuma bata gani kawai ta ƙarɓa."

Bayan ta ƙarɓa kamin su fito daga bukar bokan anty hawa tace ma bokan "Bacin wannan babu wata mafita."

Yace "Babu, mafita ɗaya ce sai in kashe yarinyar za'a yi ko yaron."

Da sauri tanti tace "A'a ai bana son ta mu na fison na ganta cikin mayuyacin hali ta koma kamar ba ita, a bar wannan kawai zan iya."

Yace "To shikenan sannan suka fita."

Suna fitowa har ƙarfe 12:00 na dare yayi dan haka basu tsaya tattauna maganar ba suka kama hanya sai wajajen ƙarfe 3:00 suka isa cikin garin maraɗi gidan Hajiya lubabatou suka fara biyawa ta sauka sannan suka wuce gidan Aunty hawa a nan tanti ta kwana dan tasan idan taje gidan yanzu har sun daɗe da rufewa dan haka kawai tace sai da safe.

Kamin sun kwanta Aunty hawa nata yi mata jimamin anya zata iya kuwa tace zata iya kada ta damu dan haka Aunty hawa tayi shiru da bakin ta, safiya nayi wajen ƙarfe 10 ta nufi gidan ta fara aikin ta da ya dameta.

Yau sati guda kenan da AFREED ya kasa samun wayar AFREEN duk ya fita hayacin sa haka ya sanar da Ali halin da ake ciki, Ali ya kwantar masa da hankali wajen faɗa masa cewa zai ƙara bin hanyar da ya bi ya sama mashi number ta a wacen lokacin yanzu ma haka zata kasance, amma kashe wannan karan da mummunan na labari ya dawo wa AFREED cewa AFREEN ta daina aiki da waya baki ɗaya ranar kamar yayi hauka dan jiyake idan har bai ji muryar ta ba yau to zai iya rasa ransa dan haka ya ce ma Ali zai shirya yaje Maraɗi yau ɗin nan, don kuwa har ya fara jin zazzaɓi yace zai bi jirgin da zai tashi ƙarfe shaɗaya na safe dan haka ya shiga haɗa kayan dan muna ƙarfe tara ne na safe Ali na natseye yana kallon sa cike da tausayi da mamaki abinda ke damun ɗan uwan na sa dan bai taɓa tsammanin haka daga gare shi ba, idan har aka ce masa AFREED zai faɗa soyayya da wata zai iya yin gardama bare har yayi irin wannan azabtacen son.

Haka ɓangaren AFREEN ta kasa jure rashin duk da ba wani tsawon lokaci suka ɗoka a tare ba amma tana mamakin yan da akayi ta kamu da son sa har haka, dan tayi tunanin zata jure rashin jin muryar sa amma ina abun ya ci tura, saboda har ga Allah ita ɗin ma na walaha dan kullum cikin kuka take, haka duk in zatayi bacci sai ta cire sim card ɗin sannan ta kuna wayar ta shiga whatsapp ɗin tunda ba goge shi tayi ba ta dinga kuna voice ɗin sa ta saurara har sai bacci ya kwashe ta, saboda idan bata yi haka ba to fah bata iya bacci, abinda AFREED bai yi tunanin yi ba.

Yau dai itama AFREEN ta kasa jure rashin jin AFREED a waya dan haka kawai zuciyar ta ta yita ingiza ta da saka sim card ɗin ta ta kirashi ko zata samun ragin zogin da zuciyar ta ke mata haka kuwa akayi AFREEN take ta ɗoko sim card ɗin ta in da ta ajiye ta saka ta kuna wayar ba tare da ta tsaya komai ba kawai shiga contact ɗin ta, ta nemo number sa ta tura kira daidai ƙarfe 10:12 na safe AFREED ya fito da ga wanga kenan don yin shirin bin jirgin da zai kaisa maraɗi a ƙarfe 11:00 kawai sai yaji wayar sa na ringing babu abinda ya zoma masa a rai sai AFREEN dan kullum yinin yake yana jiran kiranta ko message ɗinta kusan a ko wane lokaci cikin duba wayar sa, dan haka da sassarfa ya nufi bed 🛏️ ɗin sa ya ɗoki wayar sa da mamaki yake kallon number dake yawo a saman screen ɗin wayar shi, ba tare da ya tsaya ƙarasa mamakin da yake ba yayi saurin ɗaga kiran gudun kada kafin ya gama mamakin kiran ya tsinke kuma shi ya maida kiran yaji shi a kashe, yana ɗagawa ya ƙara a kune kamin yake furta wata kalma AFREEN tace "Assalamu alaikum."

Da sauri AFREED ya amsa sallamar duk yana ji kamar a mafarki da sauri ya "Dan Allah AFREEN kada ki kashe wayar bari na katse kiran na maido maki kira."

Cikin sanyayar muryar ta tace "To"

Da sauri ya katse kiran da sauri ya mayar gudun kata kashe wayar yana jin ta ɗaga ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi gaske wanda ita kanta AFREEN saida ta lumshe ido tare da sakin ajiyar zuciyar a ɓoye.

*Alhamdulilah wannan gamin dai nayi ƙoƙari*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_

*Page* : 61&62

Da sauri ya katse kiran da sauri ya mayar gudun kata kashe wayar yana jin ta ɗaga ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi gaske wanda ita kanta AFREEN saida ta lumshe ido tare da sakin ajiyar zuciyar a ɓoye.

Ba tare da ya tsaya ko gaisawa sunyi ba ya fara da faɗin "Wife ina kika shiga haka kinyi mugun tayar min da hankali duk na shiga wani saboda rashin ki yanzu kasa jurewa nayi na da rashin muyar ki kuma shiru babu labarin ki, kinga ni nan yanzu nake shirin zuwa Maraɗi har lokacin tashin jirgin da zan biyo ya kusa, inshallah ya zamuga juna nagaji da baye boye gara ayita ta ƙare zanzo na gaida papa sannan na faɗa, idan na dawo sai na turo su dady su zo kawo kudin auren ki ma chérie dan hakan zafi min komai farin ciki in buɗe ido in ganki a kusa dani."

Ƙarshen tashin hankali AFREEN ta shige shi ɗan a mugun zabure ta sauko daga saman gadon ta kamar AFREED na ganin ta wani mugun fido ido abinka ga mai ido sai ko suka firfito waje sosai,kamar tana ganin AFREED, a mugun tsorace tace "A'a dan Allah ka faɗa tafiyar ka barta har daga baya ba yanzu ba, kuma papa bai nan yayi balaguro dan haka ba ma sai kazo daga yazo zan faɗa maka sai kazo."

AFREED ya ɗan shiga shok jin daga yace zai zo ya gaida iyayen su duk tabi ta rikice, kawai sai yace "AFREEN lafiya kika rikice haka daga na faɗa zanzo na gaida iyayen ki, ko bakison gani na ne ko dai akwai abinda abinda kike boye min ne?"

Saidai AFREEN ta daidaita nutsuwar gudun kar ya gane cewa ta ɓoye masa wani sannan ta koma ta zauna bakin gadon tace "Haba kamar dai bana sonka da zance bana son ganin ai kin har akwai wanda keson ganin ka bayana yake to amma ka bari har papa ya dawo sai kayi zuwa guda sai kuzo ma tare da su dady ayi komai da komai ai zaifi ko to ni da kaina na matsu na gammu a inuwa guda muna fira cikin nishaɗi yanzu dai kayi annulé ɗin zuwanka har wani lokaci zaifi."
Chapter 63 · 0% Book details