← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 69

Sashe 44

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Keda ke can AFREEN bata ma ɗago ta kalle ta ba bare tayi tunanin zata tanka mata sabida tariga da ta saba da halin umma indai itace wajenta batayin daidai.

Papa ya kalli AFREEN yace "Tashi yi ta fitar ki kin jiko ƴar albarka, ba musu ta mike ta koma ɗakin ta, shi kuwa papa ya ɗauki waya ya kira ya'yan sa Adamu ya sanar dashi cike da farin ciki ya taya papa murna sannan suka ɗan taɓa hira kamin sukeyin sallama, haka ya kira maman yace ta sauko kasa yana son ganin ta, itama tanti ya kirata yace ta fito zasuyi magana, batare da jimawa ba duk suka halar a falon nan yake sanar masu abinda AFREEN ta faɗa masa cike da farin ciki suka taya juna murna, amma ko abinda ba'aso umma bata faɗa ba itama tanti da kaga yanda take barka kasan bata kai ciki ba, daga bisani kowa ya watse ya nufi nasa ɗakin.

Itama AFREEN tana shiga ta sanar dasu abinda papa ya faɗa sannan Fanna ta kira iyayenta ta sheda musu cewa sun sami kujerar Makkah farin ciki gun su ba'a magana ranar kam yuni sukayi hira yanda hajin nasu zata kasance sannan tace da safe zata kira mahaifiyar AFREEN da mahaifin nata suyi masu godiya shima baban Fanna yace zai kira papa yayi masu godiya daganan aka basu AFREEN suka mata godiya tare yiwa Khairat fatan Allah sa alkairi.

Fanna na gama wayar, AFREEN tace a kira anty Fauziya a sanar da ita, Khairat tace "Ai tariga kowaji."

Daga nan suka ci gaba da fira sai wajen ƙarfe 11 na dare kanan sukayi shirin bacci, yau Khairat a ɗakin AFREEN zata kwana AFREEN da Fanna ke kan bed ita kuwa tana saman wata ƙatuwar matala tayi ɗai ɗaya, AFREEN tayi addu'a ta kwanta tare da rumtse idonta ina sai bacci yace baya da yuri ga idanunta, dalilin kuwa shine daga ta rufe idonta sai taji cikin kunnuwanta maganar AFREED na dawo mata a lokacin da yake ce mata "Yakamata ki bar gun nan gaskiya sabida idon kowane gardi akanki yake duk da niƙaf ce a fuskar ki hakan bai kamata ba kowa na kalleki." Maganar nan ta kasa barin dodon kunnanta, kuma ta kasa bacci dan tana rufe idonta take jin maganar na dawo mata cikin kunnanta sai juyi take ta rasa mike damunta, har ƙarfe 1 dare tana kwance ta kasa bacci kawai sai ta tashi ta shige toillet ta ɗauro alwala, ta fito ta saka rigar ta doguwa ta sallah da babban hijab ɗinta ta kabarta sallah duk da lokacin tashinta sallar dare baiyi ba, amma haka ta dake tanata jero nafilfili dalilin bacci da ya ƙwaracewa idonta har saida aka yi kiran sallar farin sannan kwana ɓarayo ya ɗoke a nan saman dardumar.

****** ****** ******

Da kyar da taimakon Allah AFREED ya kai gida dan sosai zuciyarsa kemasa zafi kuma ya rasa dalilin haka, ya isa gida yayi parking ɗin motarsa ya fito ya nufi ɓangaren su direct ɗakin sa ya nufa ba tare da ya tsaya komai ya rage kayan jikin sa ya faɗa toillet ya sakar ma kansa shower 🚿 na ruwa masu sanhi dan so yake zuciyarsa tage zafin da take masa amma ina hakan bai samu ba har sai da ya gaji da dukan da ruwan kemasa ya fito dai lokacin ana kiran sallah magariba da sauri ya shirya cikin doguwa rigar sa ta zuwa masallaci yafito dan tafiya masallaci daidai lokacin su Ali da kowa da kowa suka shigo gidan, tsayawa ya masu nuni hannu cewa masallaci zai tafi ana shirin tada sallah, ba tare da ya tsaya jin amsar su ba ya nufi masallacin dake kofar gidan.

Ali da Umar da mijin tanti A'ishah da sauri suka nufi cikin gida dan ɗauro alwala ba tare da sun jima ba suka fito sai masallaci dan har an tayar da sallah.

Haka tanti da ƴan matan ta suma suka shiga suka fara sai gabatar da sallah suna kammala suka baje kan bed suna sauke numfashi gajiya, Fariya ta fara tashi ta nufi toillet tayi wanka sannan Khadijah tana fitowa Farisa ta shiga, haka Amal da ummi suna nasu ɗakin suna hutawa, suna gana shiryawa suka gabatar da sallah isha'i sannan gaba ɗayan su suka dawo falo dukan su a saman kafet suka zube sannan suka shiga hira suna cikin hira ne Farisa ta kalli Khadijah tace "Sister yau naga wata halitta dama akwai mutane masu mugun kyau kamar aljanu wannan yarinyar kyau ɗinta yayi mungun bani tsoro dan ko a India samun mai kyau irin nata sai an tona duk da tana zubi da indiyawa sabida idan ta shiga a cikin su ba za'a gane cewa ita ɗin ƴar Niger ce kuma ƴar maraɗi, amma dai mamanta ba'indiyace shi kuwa mahaifin ta balarabe ne ko? dan gaskiya sai in wannan yaren ne guda biyu suka haɗu har za'a samu damar samun mai kyau irin ta, lokacin da idona ya sauka kanta wallahi har saida na zabura kaɗan ya rage na zuba da gudu sai naga mutane nata zuwa wajen ta suna hoto sannan na yarda da muntun ce ba aljana ba, kuma danaga tayi karatu, ke ita har muryar ta daban take da ta kowa wallahi kinji yanda take sakin karatu cikin sanyayar ku zazaƙa muryar ta sosai yarinyar ta birgeni dubi fah ko ƙwayar idonta chocolat color ne.

Murmushi Khadijah tayi tace "AFREEN kenan kikenufi ai nima sau ɗaya na taɓa ganin fuskarta sai yau na biyu sabida kyau dake gare take rufe fuskarta ita da kanta tsoron kyau ɗin ta take har ƴan gidansu suna mamaki shi, kuma batun babanta balarabe ne ko mahaifiyar ta ba'indiyace ban sani ba wannan, abinda na sani shine mahaifin ta haifaffen garin Mali ne amma bansan mahaifiyar ta ko wace irin ce ba shima dalilin ƙanwarta Zeinab na sani tunda da ita muke gaisawa duk da ita AFREEN ɗin muke sa'a guda da ita, kuma wallahi babu ruwanta, gata da son mutane ga mutunci ga kamala uwa uba tsoro da addini da masu zama da ita sunce idan kana tare da ita to wallahi ba zaka taɓeba, sosai nakeson ƙawance da ita to ba sosai muke haɗuwa ba shiyasa, ai AFREEN tayi a rayuwa yarinyar tanada hankali sosai ga nutsuwa kuma ita kowa nata ne."

Amal tace "Wallahi anty Khadijah nima dana ganta saida naji tsoro gaskiya tanada masifafen kyau mara misali."

Farisa tace "Da garin nan nake da sai nayi ƙawance da ita wallahi."

Fariya tace "ina ma ya AFREED zai ganta yace yana sonta daga nan idan ta yarda sai ya aureta ta haifa mana yara masu kama da ita gaskiya da munji daɗin samun ta cikin zuri'armu kodan kyawawan halayen ta wallahi, dan na lura AFREEN ɗin nan matar manya ce iri su ya AFREED ɗin dasu ta dace Allah ba yayan mu ita ameen."

Khadijah har ta buɗe baki zatayi magana , kamar ance ta juya sai taga ga AFREED tsaye kusa da su, Ali da Umar da mahaifin sa suna ƙarasowa cikin falon, ganin Khadijah tayi shiru yasa su ɗaga kawanan su dan ganin miye yasa ta yin shiru suna haɗa ido da shi ya watsa masu wani uban harara, da sauri duk suka sada kansu suna muzurai kamar munafukai daga nan kowa ya shiga taitayin sa.

Basu wani ɓata lokaci ba a falon ba tanti A'ishah ta fito itama, sannan masu aikin gidan suka kawo masu abincin nan saman kafet gaba ɗaya suka gewaya suka ci abinci.

Suna kammalawa kowa ya nufi ɗakin shi, yau basu tsaya fira ba sabida gajiya da suke da.

AFREED na shiga ɗakin ya koma shiga toillet ya watsa ruwa sannan ya fito yayi shirin bacci cikin sanhin jiki duk yau jinsa yake wani irin, wayoyinsa da ke saman kujera dake cikin ɗakin ya ɗoko sannan ya nufi bed ɗin sa tare da kashe hutar ɗakin sannan ya ƙara ƙarfin AC dan mugun zafi yake ji kamar yanda zuciyarsa har yanzu bata daina yi masa zafi ba yana cikin yin addu'a shiga bacci wayarsa da itace duk wani ɗan uwansa ko iyayensa ke samun sa, itace ta ɗauki rururi, kollon wayar yayi ganin wanda ke kiransa bai sa ya daina addu'ar ba saida ya kammala sannan ya ɗauki wayar da niyyar maida kira sai ga wani kiran ya shigo, ɗoka yayi ya ƙara a kunan tare dayin sallama, ana amsa sallamar yace "Dady ina wuni, anyuni lafiya, ya gida, ya Momy, da fatan duk kuna lafiya?"

Dady yace "Lafiya lau AFREED da fanta kuma kuna lafiya?"

"Lafiya lau dady."

Dady yace "To madala yaushe ne zaku dawo."

AFREED yace "Jibi insha Allahu."

"To Allah kaimu, amma inason kafin ku dawo kuyi ƙoƙari kuje gidan aminina Alhaji Sadisu ku gaido shi na faɗa masa kana cikin garin nan kuma har kuna shirin dawowa shine yayi ta faɗa miyasa da zaku zo ba a faɗa masa ba aida kun sauka gidan sa, indai taiƙaice maka dai ya nuna min baiji daɗin rashin sanin zuwan kaba shine yace na bashi adress ɗin gidan A'ishah shi yazo ya ganka kamin ku tafi sabida rabonsa dakai tun kana jinjiri da yazo sunanka , sai kuma inya haɗu da hoton ka a TV, shine nace masa ya bari kai zaka zo har gida ka sameshi."

Sedai AFREED ya ɗan nisa sannan yace "Inshallah dady gobe zamuje kwai ka turoman da adress ɗin gidan sai muje nida Ali da Umar insha Allahu."

Murmushi mai sauti dady ya saki wanda har saida AFREED ya juwo shi sannan yace "yawa ɗan albarka yanzu zan turoma da adress idan Allah ya kaimu goben sai kuje, sai da safe Allah maku albarka.

Da ameen AFREED ya amsa sannan yace Allah kaimu safiya lafiya."

Daga nan dady ya kashe kiran komin minti 1 ba'a yi ba sai ga soƙon adress ɗin gidan Alhaji Sadisu ya turo masa ta whatsapp, yana duba bawa sai ya kashe data ya kwanta ai yana rumtse idonsa..............

Sai kunji ni a page ta gaba😜😜😜😜
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*

*Page* : 41 & 42
Chapter 44 · 0% Book details