← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 69

Sashe 26

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsorace Zeinab tayi saurin juyowa tana dana ƙirjinta idonta a warwaje tace "Lah anti kece? wallahi harkin ban tsoro ina shirin gudu wa bansan kina nan ba ashe kece ke girki a kitchen ko motsinki ba'a ji wallahi ni inasama breakfast déjà yana kan dinning saboda wani mugun kamshi dake tashi wallahi kinji wai kamshin zanice a kusa na yake ashe yana cuisine yanzu ne aka fito dashi kai amma anti ki iya girki irin wannan kamshi haka kullum girkin anti da kalar kamshin sa babu rana dazakaji wannan na kalar kamshin wannan ga ɗadin ɗanɗano, ɗaɗin girkin anti ni ban ma taɓa jin irin sa ko girki Maman dake da mugun ɗaɗin mai taɓa ƙwaƙwalwa wallahi naki ya fishi, gabaɗaya gidan maman ta koya mana girki amma babu wanda ya kamo ki ya iya wa hata anti Khairat ma da a tare aka koyamaku amma naki yafi ɗaɗin certe itama nata yaji garɗi amma bai kai naki ba, ai gidan nan iya girki mai mugun daɗi daga ke sai maman da anti Fauziya, kam anti kinji watanan wada ta iya girki kamar ka cire kanka ka bata idan kana cin girkin ta dan garɗi girkinta wato anti Fauziya amma duk da haka bata kaiki ba naki na daban ne wallahi anti ni inaso na iya girki sosai anti amma duk in nayi ba zai yi ɗaɗi naki ba dama zaki cire hannuwan ki kiban?"

Murmushinta mai ƙara mata kyau ta saki tace "Kai Zeinab uwa tsoro da surutu wannan zuba haka kamar an jonaki, idan an ji tsoro addu'a ake ba waro ido ba kinji ko, kuma girki ai kema kin iya kuma yana ɗaɗi sosai sannan idan kina so ai sai na cire hannuwan nawa na baki?"

"Kai anti wasa fah nake maki wallahi ya zance ki ciro hannuwan ki ban to ke fah, wallahi anti ke komai naki mai kyau ne idan kina magana ko murmushi kuncin ki har lotsawa yake bama saikinyi dariya ba ga tafiyar ki da tafi komai mugun birgeni idan kina tafiya kamar bakison taka ƙasa ne ko kina mugun jin tausayi ƙasa yanda kikasan hawainiya na tafiya haka taki tafiyar take ko kaɗan ba'ajin ƙarar tafiyar ki idan kina yi mutum zai iya cewa idan kina tafiya ƴangace kike alhalin ba haka bane wallahi kalar taki tafiyar ce haka nidama zaki koyamin anti inaso wallahi anti idan aka kalle ki dole mutum ya koma kallon ki ko yanason ko bayaso koda kuwa mace ƴar uwakice, dan ma baki fita kullum sai da niƙaf, nida nikeda wannan kyau naki da babu wata niƙaf da zansa sedai na diga firgita mutane da baiwar kyau da Allah ya min hum," Zeinab ce ke wannan surutun tana murmushi.

"Oh ni Zeinab yaushe ne wai bakinki ya buɗe haka kina tazuba kamar an biyaki to Allah ya shiryaman ke ni bari naje na ajiye kayan nan na tsaya ina sauran shirmanki har hannuna yayi sanhi," AFREEN ta faɗa tana me yin gaba abinta.

Da sauri Zeinab tasha gaban tareda tara hannu zata ƙarɓi kayan dake ga hannu AFREEN tace "Anti kawo na tayaki kaiwa dinning ɗin."

"A'a Zeinab jeki ki ƙarasa aikin ki zanji da wannan kinjiko na hutar dake."

"Anti ai har na ƙarasa kawo kawai na tayaki shirya mana table ɗin."

"To jeki ida ƙarasa fito dana na cikin kitchen ɗin."

Da gudu Zeinab ta juya ta nufi hanyar kicin tanacewa "Wallahi anti duk abinda na faɗa akanki gaskiya ce ba shirme ba."

Murmushi AFREEN tayi tare da girgiza kanta tana cewa "Allah shirye ki Zeinab, a tare suka shiyar dinning ɗin tsaf.

Zeinab tace "Anti wallahi duk in kinyi girki sai naji idan inaci kamar karna daina."

Wani murmushin AFREEN ta koma yi sannan tace "Dan Allah Zeinab surutun nan naki ya isa haka kada kikai gasamin ciwon kai jeki kiyi wanka sai ki fito ki karya kinji ƴar albarkar ƙanwata."

Kollon AFREEN ɗin tayi sai tace "To shikenan anti na mai tsada."A guje ta kwasa da nufi ta bar gun da sauri AFREEN ta tsayar da'ita tace "Zeinab ban hanaki gudu ba wai ke ba zaki iya tafiyar hankali ba dole sai kin haɗa da gudu?"

"Lah anti na manta yi hakuri daga yau na daina insha Allahu," sannan tabi hanyar ɗakin nasu ta shige. Ita ma AFREEN ɗakin nata ta nufa.

Tana shiga ɗakin ta ta wuce toillet dan yin wanka, bata tare da ta ɓata lokaci sosai ba ta fito da tawel ɗaure a ƙirjinta bakinshi iya cinyoyinta ɗaya tawel ɗin ɗaure akanta kusan wani drawer ta ƙarasa ta buɗe ta fito da abin busar gashi sannan ta rufe drower taje gun soket ta saka abin busar da gashin sannan ta fara busar da shi tana kammalawa ta mayar da shi ma'ajiyar sa tareda komawa gun mirror ta zauna ta fara shafe shafen mai da turaruruka humra masu mugun kamshi mai gigita tunanin masoyan da haɗaɗen kamshi mai kwantar da zuciyar duk wani ma'a buci son kamshi ta ƙarasa shafe shafen ta nufi wardrobe ta fitar da wasu haɗaɗu English wears riga da wando riga puple wando baƙi a take ta haɗe cikin ƙananun kayan ta wanda suka kamata sosai suka fito da gaba ɗaya surar jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba idan ka ganta kamar ka saɓe ta ka gudu, komawa tayi gun mirror ta dauki turaren feshe kala uku ta shiga fesawa jikinta idan ta fesa wannan ta ajiye ta fesa wannan zakace wani babban bahon turare ne aka malayar a jikinta da kuma ɗakin nata sabida wani haɗaɗen kamshi ne ke tashi a jikinta da kuma ɗakin gabaɗaya ita dama ba ba'a buciyar yin kwalliya ba kuma ba dan wai bata iya bane kawai bata yine tana kammala kominta ta koma kan gadon ta kwanta tare da janyo wayar ta kuna data tana chatting da kawayenta.

Wani group ɗin familyn sune ta shiga tareda yin sallama tare da tura emoji na sannun ku ai kuwa kamar jiranta suke suka mata ca ah AFREEN kece yau da magana a group ɗin kullum ke karatu karatu ba damar ki hayo ayi fira wasu kuwa suna ah sis munyi miss ɗinki ya karatu duk tayi ta basu amsa daidai da saƙon kowa, tana cikin chatting ɗin Zeinab ta shigo ɗakin tare da sallama sannan ta ƙara so inda take tace "Anti inji papa ki fito mu ƙarya ke ɗaya ake jira."

AFREEN ta tashi zaune sannan tace "Jeki kice ganinan zuwa."

"A'a anti zanjira ki mufita tare wallahi anti AFREEN kinji wani kamshi mai sanyin ɗaɗi dake tashi a ɗakin nan da jikinki lale anti kina jin ɗaɗinki kuma idan nace komai naki na daban sai kiyimin gardama amma ko bani ba nasan watarana wani zai faɗa maki ko kuwa har antaɓa faɗa maki hankan wa ya sani."

"To sarkin ƴan iya magana nidai bari na ɗauko hijab ɗinna mu wuce," ciro hijab ɗin ta tayi daga wardrobe tasaka har yana jan kasa sannan ta kama hannu ta suka fice a ɗakin, kowa ya halarta a gun cin abincin sune kawai ake jira suna zuwa suka zauna AFREEN ta gaida iyayenta sannan ta zubawa kanta abinci baki wanda zata iya ci kamin papa yayi bismillah ya fara ci sannan kowa dake wajen suka fara ci al'adar gidan suce duk idan zasu ci abinci sai papa ya fara kaiwa bakinsa kannan iyayen su mata sai yaran daga babba zuwa ƙarami shiru bakajin ƙarar komai sai ta spoon can maman da ke hankalce da AFREEN tace "AFREEN abincin nan fah sai kin cinye shi naga kamar bakai sonci, kuma miye abin saka hijab dan zakizo nan, anyi mutum kullum cikin hijab dai wai baki gajiyane?"

Murmushi tayi sannan tace "Kai maman ai zan cinye shi insha Allah ba wani dayawa bane, kuma ƙananun kayane a jiki na shiyasa na saka hijab gudun kada wani ya shigo."

Kamin maman tayi magana dan ƙaramin ƙanansu wato Imran yace "kai anti kedai kinason saka hijab ne."

Dayake kusanta yake sai ta ɗan shafa kanshi tace "Autan maman ai na sabane da kaima mace ne ai da zan koyama ka ne ya ƙaratu injin dai nata ƙoƙari?"

"Karatu alhamdulilah, Allah ya sawaƙe ko dani macece bazan yarda nayi ta saka hijab kullum kamar wani kala."

Duk wa'inda ke gun su kwashe da dariya banda umma da duk haushi suke bata, sai Fahad da yayi murmushi dan bai cika yin magana ba kokuwa kace ka ganshi yana dariya sai ajima sabida shi magana ma wahala take mashi bare yayi dariya idan yana ga yuri zaya iya ƙinyi magana duk abinda kuwa za'a ce har abada gun ba zai ce komai ba wani lokaci ba har mantawa ake da yana gun kusan halinsu guda da AFREEN saidai itata ma fishi yin magana.

Papa yace "Imran bakada dama"

"Wallahi papa da gaske nake inada ni mace ne bazan iya irin na anti AFREEN ba gaskiya."

"To kuma sai Allah ya fito dakai a namiji." papa ya faɗa yana murmushi.

Aiko da sauri Imran yace "Inda naji daɗi kenan."

Nan ma dariyar sukayi sun tsagaita dariyar ne Tanti tace "Gaskiya AFREEN ki rage saka niƙaf da mayan hijaban nan naki idan bahaka ba taya zaki wani zai gangi yace yana sonki har kiyi aure nida nakeson ace tare dake da Khairat za'a aurar a lokaci guda kinga maman Fauziya zata dinga mana kurin cewa zata aurar da ɗiyar ta amma kinga idan auren Khairat da naki yazo lokaci guda babu batun mana kuri."

"Ah to faɗa mata sabida kunfi kusa." maman ta faɗa

Ita kuwa AFREEN duƙe kanta tayi tare da cewa "Kai Tanti aure nikuma tun yanzu."

Tanti tace "Ban gane miki nufi da tun yanzu ba kina nufin baki isa aure bane ko miye? to ko Zeinab yanzu aurar da ita ake bare ke masha Allah da kika girme mata sosai sabida kin bata kusan shekara 6."

AFREEN dai kanta a ƙasa bata ƙara cewa komai ba."
Chapter 26 · 0% Book details