← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 69

Sashe 1

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRITE:

_PAR_

*QUEEN ZEEFAT*

Yar
Mutan
Niger

Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_BISMILAHIR RAHAMANIR

Page 1

Dandanzon matasa ne maza da mata ke fitowa daga cikin wata babba kofa wada a samata aka rubuta *LYCEE TECHNIQUE DAN KASAWA DE MARADI* hakan ya nuna cewa makarantar boko ce gashi kuma kowane matashi da jakar makarantar sa a baya wasu kuma a hannu kowa sai kama gaban shi yake sanadi tashi da akayi daga makarantar, wata yarinya ce ke tafowa tana nufo kofar makarantar hannun rike da wata farar takarda da jikar makarantar a dayan hannu sanye take cikin dongon hijabin ta har kasa da nikaf a fuskar wada ko eyes inta ba'a gani don fuska rufe take gaba daya ga safa da take sanye da ita ta hannu da ta kafa duka ilahirin jikinta rufe yake babu abinda ake gani, tana tafiyar ta mai kama da hawainiya cikin kwonciyar hakali da nutsuwa kamar mejin tausayin kasa a haka har ta kawo baki kofar makarantar tayi wajan wani shago dake gefan makarantar mai shagon dake zaune daga daya bangaren shagon yana ganin ta ya taso yace malama mikike bukata banji mitace ba sai gani nayi ta mika masa takarda hanuta ya karba yayi cikin shagon da takadar a hannu sa ba'a fi minti biyu ba sai gashi ya fito daga shagon ya mika mata takarda biyu a maimakon guda da tabasa karba tayi ta bude jakar makarantar ta fido kudi ta mika masa ta juya takoma cikin makarantar da takardun a hannu ta daidai wani office ta tsaya ta kwonkwasa sai ga wani datijo ya fito wanda baza ya fuce 50 years tadan rusuna ta mika masa daya takardar ta juya da dayar wajan parking space dake cikin makarantar ta nufa tsayawa tayi daidai wata hadadiyar benz kirar mercendy ta bude jakar ta makaranta ta fito da makulin mota budewa tayi tashiga ta tayar da motar tare da barin cikin makarantar a lokacin da daliban dake cikin makarantar basu huce mutun shida sabida kowa ya kama gabansa.

Driving tayi natsawon minti 20 kamin take kawowa wata kayataciyar anguwa daga ganin anguwa ba me yawon mutane bace sabida yanayin ta ya nuna hakan ga wani hadadan kuma babban filin ball daya ya karama anguwar kyau macha allah
Wajan wasu mayan tsararu kuma kayatacin gidaje guda biyu dake irin daya naga ta nufa komin su gidajan irin dayane sedai guda yafi guda girma shima ba sosai ba wanda ya fi girma a cikin gidajen ta nufa tana dana hon mai gadi ya wangale mata tagamemiyar porte (get) in gidan ta tura hancin motar ta a ciki, tsaruwa haduwa kayatuwa kai yayine gidan karsha ne wajan haduwa babu abinda ba na rayuwa a gidan parking space kadai ma na gidan abin kalon to baran tanama farfajiyar gidan

Parking in motar tayi a parking space dake cike da motoci sun kai kala 10 ta fito daga cikin motar ta kule tareda fitowa daga parking space in tayi hanyar shiga gidan, gidan dauke yake da sashe guda uku daya a gefen hagon gudan a kefan dama se dayan natsakiya kuma shine bangare mafi girma da ke cikin gidan hanyar babban bangaren tanufa tare da murda wata daleliyar kofar da zata sadaka da falon gidan shiga tayi hade da salama a bakin ta wada in ba kusa kake da itaba ba zaka taba jin abinda ta fada wooow nace tare da furta allah sarkin dadi inji barawon takanda lokacin dana tsintsi kaina a wani katarfaran falon da ya tsaru iya tsaruwa komi na falon brown and milk color ne, falon dauke yake da bedroom guda biyar da cuisine (kitchen) guda se set uku na kayatatun kujeru sabida girman falon da dan madaidaicin table central (center table)milk color shi ba babba ba shiba karami ba wanda ya kawata tsakiyar kujerun se TV stone dake jikin bangon falon akasa tare da wata tangamemiyar TV dake manne a bango babu ce kadai ha babu a ciki ga wani kayatacen kamshi dake tashi a falon mara misali
sabida shagalta danayi wajan kalon tsaruwar falon har na manta da rahoto nake dauko maku falon ne ya tsaru irin tsaruwar da ban taba gani irinta ba sai a TV

Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi kofar daya daga cikin bedroom din dake falon ta mudar kofar tashiga da kafar dama hade da yar siririyar salama a bakinta wani ni'imtacan kamshi mara misiltuwa ya daki hancina nace macha allah, babu wani tarkace a ciki amma ya hadu daga bed da wardrobe sai dressing miror da kujera babba guda dake gefe sai douche interne (bathroom) da abin ajiyar jaka kusa da armoir (wardrobe ) da abin rataye kaya da ke manne da bangon dakin sai agogo itama manne a can saman bango babu abinda babu a cikin na more rayuwa kana ganin yanayi dakin zaka gane na yan mata ne daki dai macha allah

Tana karasa shiga dakin taje dan gaba da kofar dakin tacire takalmin dake kafarta ta juya tayi bakin gadon dake cikin dakin ta zauna ta cire nikaf da hijabin da ke jikin tare da cire safar hannu ta da ta kafa ta mike tare da nufar wardrobe ta bude ta ciro serviette (tawel) juyowa tayi da niyar nufar hayar toillet take nan takardata da biro dake hannu na suka subice min la'illaha illa anta subhanaka inni kuntum bina zalim ku kuke ganimu bamu muke ganin kuba na furta tare dajan baya da karfi sanadiyar tozalin da nayi da kyakyawar fuskarta juyawa tayi tare da shigewarta toillet da sauri nayi wajan peper da biro na dan na dan labarta ma masu karatu haduwar yarinyar da kyau dinta bai musultuwa banta ganin kyau irin nataba ko acikin larabawa da turawa

Yarinya yace da bazata fuce 18 years ba dogowa amma ba can ba tsayin ta daidai da ita siririya ce amma ba sosai ba ita ba fara ba kuma ba za'a sanyata a layin bakake ba yarinyar café au lait ce (shacolate in milk color) irin black americain din nan ce idan kanganta a kusa da wani black americain din ita zaka iya cewa tanada haske amma ba sosai ba da kaire mutun zai tantance kalar fatar ta ma saidai a kimanta gashi girar ta ya kwanta luf luf sai sheki yake da daradaran idanun ta farare tas dasu se bakin da ke cikin idanu ita nata brown ne mai kamar baki da zarazaran gashi idanuta tsaf dasu sai dogon hancin ta har baka da dan karamin bakinta da ya karama fusakar kyau da sheki allah ya mata kyau na gasken gaske baza taba iya musulta kyau irin nata sedai a kiman tashi shima sabida du yanda zaku misilta ta tafi da hakanan

Turo kofar toillet din tayi ta fito daure da tawel da ya sauko mata har ga gwiwa sanan da daya kuma a saman kanta ga ma zauna da allah ya azirtata dasu kamar ba na karamar yarinyar yar shekara 18 ba wajan dressing mirror tanufa ta ja dan taburan ta zauna mika hannu tayi saman dressing mirror din ta dauko wasu hadadun turare guda uku irin na shafawa ajiki ta shafe jikinta gaba daya dake da damshin ruwa kafin ruwan su tsane a jikin ta janye tawel din dake saman kanta saiga gashi ta ya bayana wanda yake dogon baki kirin dashi daga zaune da take gashi yakai har kusa da ma zaunanta da kadan bai ida tabo suba ta dauki abin busar da gashi tana busar dashi da ya bushe ta dauki man kai mai kyau ta shafa masa tare da daukar mashaci ta shace gashin take gashi ya gara kyau da sheki ta dauki shoushou (ribon) zatasa saka ta kasa sabida yawa da tsayin gashi baza iya daure shiba tayi tayi ta kasa a haka ta hakura ta barshi zube a bayan ta tashi tayi ta nufi wardrobe ta fido wata hadadiyar doguwa riga mara nauhi baka mai ratsin ja tasaka tare da dauko hijab da darduma ta rufe wardrobe komawa tayi wajan dressing mirror din ta feshe jikinta da dadadan turare na fesawa mai kamshin gaske tsakiya dakin ta dawo tashinfida darduma tasaka hijab tare da tayar da salllah.
Tana idar da sallah tayi adu'o inta ta mike ta linke dardumar da hijab sanan ta mayar dasu inda suke komin ta cikin tsari nutsawa da kwonciyar hankali take yinshi ta dauko dan kwalin rigar dake saman gado ta aza a saman kanta daya rufe duka ilahirin kanta sai dan jelar gashi daya fito a bayan ta da ya kusa tabo mazaunan ta komawa tayi wajan dressing mirror din ta dauko ribon din ta fita daga cikin bazata

Commenté

Et

partager

Comments

And

share
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRITE:

_PAR_

*QUEEN
ZEEFAT*

Yar
Mutan
Niger

Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_ BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM

Page 2

tana fita daga dakin ta nufi stairs dake dauke da bedroom uku dakin dake gefen dama ta murda ta shiga da salama, wata mata ce da ba zata fuce 45 ans (years) ba fara tass da ita kamar ka kwontala jini ya fito matar tayi masifar haduwa kana kalon fuskar ta zaka hango muguwar kamar da suke sosai da yarinyar sedai sosai tafi yarinyar haske amma yarinyar ta fita kyau nesa ba kusa amma kana ganin ta zakasan cewa mahaifiyar tace sabida kamar da suke dakin mahaifiyar tata shima yayi matukar haduwa masha Allah
Chapter 1 · 0% Book details