← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 140

Sashe 97

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiru dasauri yabude kofan kofanma sai bai budu duka ba sabida tana wajen akwance tarike cikinta idanunta na juyawa dasauri Hameed yace Mamie! Mamie! Yatura dakin yashiga da sauri yana dukawa gabanta yana kallon kofa yana kiran Mamie kadan kadan Asmeey ke bude idanunta dake juyawa she could see yanda Hameed ke kallon kofa yana maganan da bataji all she s seeing is Ya Hamad, duk uban azaban ciwo hannunta tamika ahankali takama hannunsa bakinta na motsin. Yaayaa juyowa Hameed yayi dasauri yace Asmeey yanda idanunta ke juyawa tarike hannunsa gam yasa sai kawai ya ciccibeta ya dauka daidai Mamie na zuwa tace meya sameta? Dasauri yace Mamie let s go to the hospital since Yaya baya kasan dauko hijabi yana maganan yashiga tafiya da Asmeey yana sauka Asmeey na kallonsa sosai da juyayyun idanu tana motsi da baki tana magana da ba aji har motansa yakaita ya ijiyeta abaya zai taso tarikesa da muryan da baya fita tace yaushe kadawo Yaya tsayawa Hameed yayi yana kallonta her lips are still shaking tana kallonsa idanunta ajuye hakanan kawai yaji gabansa yafadi dasauri yazare hannunta daga hannunta daidai Mamie na zuwa yafito Mamie tashiga tazauna tana rikota tace Asmeey meya sameki murya kasa kasa tace Yaya kadawo! Yaya kadawo jin sambatun datake yasa Mamie ta taba kanta tace Subhanallahi mugun zazzabine ajikinta, kara gudu Hameed bari nakira Abban ku kara gudu yayi bini bini yana kallon Asmeey ta madubi har sukakai asibitin su Ya Mustapa ansan Mamie da Hameed aka karbi Asmeey sharp sharp akai admitting Hameed yace nagayama Hamadi Mamie? Dasauri Mamie tace kasansa zai rude yahau kuka awajen bari muji tukunna kira Yayanku daidai Abba na zuwa ya zauna kusa da Mamie suna jiran Dr, chan saiga Dr yafito yakira su Mama duka suka bisa yayi murmushi yace to Mama da Abba congratulations za a sami jika! Murmushi Abba da Mamie sukayi hakama Hameed aransa yace dan iska Hamadi ai wlh saina gayama su Ya Faisal Dr yace tana dauke da juna biyu na kimanin sati takwas wato wata biyu Hamad yace just few days to Hamadi yayi tafiya yamata ciki kai wannan yaro Dr yace but tanada malaria sosai and malaria baida kyau ajikin mai ciki zamu riketa anan zuwa gobe haka, dan Allah aka koma gida let her be on bed rest kartai aiki sannan ya zamto tana cikin kwanciyan hankali always saikuma ba hayaniya ko damuwa sannan next week inda hali ku kawota tafara Antinatal Mamie da Abba suka gyadamai kai sai murmushi suke Dr yace anjima kadan zaku iya ganinta tashi Abba sukayi suka godema Dr suka fito Abba na fito daidai number Baba dan kiransa Baba na dauka Abba yace to barka barka Allah fa ya albarkaci zuri a Muhammadu Sani, wannan karan Jikan namu ne namu namu Maganan Abba yasa Baba yagane Asmeey na dauke da juna biyu yace ahhh Alhamdulillah Alhamdulilah ubangiji Allah ya dayyaba yasa albarka, Allah ya raya tana ina ? Abba yace muna asibiti ba lafiya wai tanada malaria za a rikemu dai zuwa gobe Baba yace Toh Allah yakara mata lafiya Allah ya sauketa lpy Abba yace Ameen Ameen sauki sallama Baba was very very happy Wajajen 9 Asmeey ke bude idanunta ahankali Hameed kadai tagani zaune kan kujera da waya a kunnensa Mamie kuma na salla, alamun motsin mutum yasa yakalli gadon dasauri ganin Asmeey na kokarin tashi zaune yasa yace I will call u later ya katse wayan yazo wajen gadon yace careful Asmeey bari na tada gadon taba botun yayi katifan yataso tashiga bin dakin da kallo cikin rashin karfi saikuma ta kalli Ya Hameed dake kallonta tace ina Yaya? Hameed na kallonta yace wani Yayan? Cikin raunin murya tace Ya Hamad dan murmushi yayi yace aiko kinata sumbatu da sunansa dazu to yana chan kasan nan fashewa da kuka tayi ahankali tace wlh na gansa tasowa Mamie data sallame salla tayi tace kindaiga Hameed dai ko Asmeey ahankali Asmeey tace Mamie wlh na gansa shiya daukeni zama Mamie tayi kusada ita tace Hameed yajiyoki yazo ya daukeki dasauri ta kalli Hameed, mugun kallo ya watsamata yawuce abinsa yafita daga dakin, Mamie tace mezakici? Fuskanta ta share tace tea Mami tamata ta karba tana kallon tea brain dinta na kokarin recalling taga Ya Hamad har tana rike hannunsa, ai tasan Ya Hameed baida idanu kaman na Ya Hamad dazu har idanun Ya Hamadi tagani, da kyar tasha tea akazo aka mata wasu allura nan da nan tayi wani bacci koda Hameed yadawo tayi bacci ko kallonta baiyiba yama Mamie sallama yatafi. a sanar da Hamad ba anaso sai an koma gida, washe gari aka sallamesu aka bata magunguna. Mom na zaune cikin gidan Fawaz dan yanzu kusan kullum saitazo dudda rabonta dashi tun a kano but coming there is now her new therapy, wayanta ne yahau ringing da sauri ta daga wayan Mama ce wayan takai kunnenta Mom tace Ya akayi? Cikeda kwarema a munafinci tace ya gajiya hala kina kotu ko nakira ne na tambaya ko ke an aiko miki da taki ankon? Gashinan na karbi nawa na iyaye ganasu Nana kyauta ina gayamiki Maman su Aya ko sisin mu babu ciki Anatse Mom tace ankon wa? Dan shiru Mama tayi chan tace wlh abin nan namin ciwo yanda mutanen nan suke nuna u are nobody, ke gaki mara daraja akan yarki, keya kamata ki turo mana anko fa ke mai y a amman sai masu danda ke aiko mana Mom jitayi zuciyanta yafara radadi gane kan zancen, Mama tace kinsan ance dashi da Asmeey zasu dawo daga kasan waje January, ga anko nan za a hada bikinsu dana Hameed on 20th ayi, ga anko nan na manya lashe iya leshi da atampa embellish, ina mai tabbata miki Ammi Maman su Ramla itama ta amsa nata dana yaranta kecedai wacce batakaiba, gaki banza kin haifa musu bakisan da auren yarki ba yanzu biki yazo shima baki sani ba Mom bata tabajin abu ya tsaya mata arai ba irin na yau, Mama cikeda watsa fetur a wuta tace hmmm na manta fa yanzu Hamadi yasha karfin mu indai kudine, wai kinsan Umara da mijinki yaje da nawa duk Hamad din yabiya kuwa? Rannan Baban su Nana Allah ya matsi bakinsa yake gayamin ke kinga zafafan motocin daya siya musu agidan nan, kinga yanda aka gyara gidan, kinga estate din dasuka gina su yaran, to yanzu haka Mustapa na China kampani zasu gina anan Nigeria kampani iya kampani kaman dangote fa, ai wlh Hamad yasha karfinki Maman Aya! Baki isa kirabasa da matarsa yanzu ba! Yanada kudi da capacity daureki if u try nonsense Mama tai maganan da gayya dan itama Mom batada mutunci, wani abu Mom taji ya soki kirjinta ta daure tace hmmm in yasan wata baisan wata ba, ko duka kudin duniya ya mallaka kafin Hamad yasan dukiya ni nake cikinta nakuma dandana nayi wanka ciki! Mom tai maganan cikeda girman kai tace Allah dawo dasu zan gwada muku cewa saidai ayi koni ko shi! Dolene dayanmu baya duniya shine za ayi bikin nan! Sannan y ata zata cigaba da zama dasu! Barikiji y ata saina karbeta wallahi! Biki dai saidai ayi na Hameed namiki alkawarin nan inhar nice Salima Mrs Muhammadu Sani Turaki! Ta buga kirji tana kashe wayan. SEE YHUU SATURDAY EPISODE 7 KANO! She doesn t really know abinda ke damunta but somehow she understood kaman ciki gareta, Mamie kaman kunya takeji takasa mata maganan cikin, su Ya Hameed ma haka to ai su maza ne, but matan Yayyin dasuka zo gaisheta sai mata Allah sauketa lpy suke, Matar Ya Faisal Anty Nana harda dan kuka dan har yanzu ita batada ciki. Itakuma duk kunyansu takeji balle ta tambayesu, dakinta taje dan sallan la asar tai shiru tadauki wayanta ta duba batada any miss call ko chats from Ya Hamad she knows ba a gayamai tana rashin lafiya ba even last time sabida ansan zai damu same with now ko itama bazata so ya damu ba but kuma she wants him to call her ijiye wayan tayi tashiga bayi tayi salla tana zaune kan dadduma Anty Asiya Matar Ya Musty tabude kofan tace oya muje an gama girki juyawa tayi zata wuce dasauri Asmeey tace Anty Dan dakatawa Anty Asiya tayi ganin Asmeey na kokarin mikewa tsaye saita shigo tareda maida kofan tarufe tace am menene Asmeey? Dan kallonta Asmeey tayi saita rasa yanda zatai maganan saita shiga wasa da yatsunta tarasa mezatace Anty Asiya tace menene Asmeey wani abu na damun kine? Gyadamata kai tayi sai kuma ahankali tace mesa Mamie kaman tanajin kunyana? Tadanyi shiru Asiya tai wani murmushi Asmeey tace rashin lafiyan menayi a hospital? Dariya saida ya kufcema Anty Asiya tace laaaaaa aini nasan Mamie bazata taba bude baki ta sanar dake ciki gareki ba akwai wannan kunyan bafulatanan tareda Mamie saidai likita ya gayamiki but zata kula dake, nima nan Dr yagayamin nakira su Nana na gayamusu, ciki ne dake Asmeey har wata biyu, su Ya Hamadi an raya sunna wani irin kunya yakama Asmeey batasan sanda tajuya tarufe fuskanta da hijabi ba Asiya tadinga dariya tace ahhh kajita aikin gama yagama munsan komi ustazan munafukai keda mijin naki dukawa Asmeey tayi tana rufe fuska sosai Asiya tace nidai sauko natafi tafice abinta kai Asmeey saitaji tanajin kunyan kowa yanzu ciki gareta? She s going to be a Mom? Ita da Ya Hamadi are going to be parents? Hannunta takai ta taba cikin sai kawai taji wani dadi da sanyi ya lullubeta no wonder Mamie ke nan nan da ita hawa gado tayi ta kwanta tayi shiru tadaga yatsunta tana kallo dama haka ake ciki da wuri sau uku sukayi fa ko? Rannan farko da kaman baiyiba sai da safe ya karasayi, yayi da daddare na biyu daganan aka karbeta takoma wajen Mamie, bai karayiba sai rannan dazaiyi tafiya da daddare sau uku but hartayi ciki? Tai shiru saita sake murmushi tawani rufe fuska yanzu shikenan kowa yasan abinda sukayi the only person dataji tanason gayamawa is Munir dasauri tabude waya taciro numbersa zata kirasa tagaya masa amman sai kunya duk ya kamata, tayaya zata wani gayama Munir tanada ciki she s very shy, sai kuma ta shafa cikin tadan dage riganta takalli flat tummy
Chapter 97 · 0% Book details