← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 140

Sashe 101

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

time zaki kara fita without izinina, na yafe miki this time but don t di it again okay! Gyadamai kai tayi tace nima ban sanshi ha kawai yacemin Gwaggo na nemana ne, I am sorry about everything I said to you dan ijiyan zuciya yasauke yace okay, idan kin tashi let me know, take care of yourself and my Baby kinji gyadamai kai tayi tace okay ahankali yace I love you so much Husnahhh mai ciki! Kunyane yakamata ta katse wayan da gudu tace Ya Hamadi is naughty now wai Husnah mai ciki! EPISODE 8 Sai wajajen magrib Asmeey ta tashi shima Mamie ta tayar da ita, ahankali ta tashi zaune Mamie tace jeki dauro alwala kiyi salla gyadama Mamie kai tayi tamike tsaye ahankali tawuce bayi, alwala ta dauro tafito tazo tai salloli sannan tamike wayanta tasa hannu ta dauka saitaga Ya Hamad yamata two recent miss calls wani dadi taji tana kokarin kiransa kiranshi ya shigo dauka tayi tana mikewa tsaye tace Hello from muryanta Hamad yace yanzu kika tashi? Gydamai kai tayi tace koda yaji tabude yace ina zaki? Ahankali tace wajen Mamie yunwa nakeji ahankali yace okay how are you murya chan kasa tace fine how are you? Ahankali yace gani nan acikin office dina murmushi tayi tashiga sauka kasa tawuce dinning Mamie na wajen tace yauwa kin fito ga abincin nan kici gyadama Mamie kai tayi tace thank you Mamie anatse Hamad yace me aka dafa Ahankali tace tuwon shinkafa da miyan wake da yaji da man shanu danama dayawa sai juice murmushi yayi yace Babyna duk ke kadai ko harda our little Baby shafa cikinta tayi cikeda dan yarinta tace ai be faracin abinci yanzu ba ko ? Murya chan kasa yace yafara but abincin jikina, my sperm wani kunya ne ya lullube Asmeey ta kifakai a table tana wani dariya kasa kasa Mamie tadan leko tana kallonta kawai ta kadakai tana murmushi tace ohh jama a kome dannan yake gayamata oho look at how Asmeey is miji ba wasa ba sosai suke hira haka ta cinye abincin ta tashi takai plate kitchen still waya take tace Yaya zanje nai salla yace okay I will call you idan naje gida idan baki bacci ba Maman Babyna turobaki tayi tadan kalli gefe ganin Mamie ta shiga store yasa ahankali tace I love you Baban Baby ta katse wayan da gudu ta ijiye tashiga washing few plates na wajen Mamie tafito tayi kaman bata jisu ba tace waya saki wanke wanke murmushi tayi zuciyanta cikeda farinciki tace Mamie zan iya wlh kingani ta wanke tass ta wanke sink din tace natafi salla Mamie Mamie tace dakinsu takoma taje tai sallan Isha i tahau kan system tacigaba da rubutu bayan tayi editing na sama wuraren 11 tafara jin bacci ta tashi tawuce gado Ya Hamad yakirata suka shiga hira ba wasa sai wajajen 2nadare da kansa yace taje tai bacci taje ta kwanta ranta fesss. **** Yau 15 of January na sabon shekara. Bauchi Tunda Baba yakomar da Mom she has been calm and good, dudda bawai tadawo masa da papers na gidan bane but tana zaman lpy dashi baya wani takura mata da zancen girki randa tayi he will eat randa batayiba zaici abincin da Ammi take dafawa domin yaranta she no dey for Mom s wahala. Yau Baba agidanta yake bayan sallan asubahi yashigo gidan tunda tadawo sai yaune ya nemeta a shimfida tabasa hadin kai cus tahanasa shiru tayi tana jinsa babu abinda takeji bawai kuma baya kokari bane kawai sabon jini Fawaz daban ne cinta yake kaman jaka yana kaimata duka, lamarin Baba kuma harda haushinsa datakeji na abubuwan daya mata yima Asmeey aure da marinta da sakinta bainar jama a yasa duk ya hadu batajin komi haka yayi yagama kaman zai zauce yana mugun jin dadin Mom kullum kaman tana yarinya haka jikinta yake ga kamshi ga gyaran fata da jiki, gamawa yayi ya rungumeta murya chan kasa cikeda soyayya yace Salameme na nagode ijiyan zuciya Mom tasauke tace akwai abinda zan gayamaka tafiya takamani dasauri yadan saketa yace tafiya? Gyadamai kai tayi ta yunkura tasa hannu tadauko handbag dinta taciro wani file da yar takarda tabasa karba yayi yana kallo saikuma yakalleta yace me akace anan? Ahankali tace amaida Chief Judge na Bauchi State gabaki daya Murmushi lullube fuskan Baba yayi yace woww Masha Allah! Chief Judge kai kai kai wannan good news haka dan murmushi Mom tayi tana danne kirjinta tace dole naje Abuja nai wani workshop haka tareda wasu documentation na sati guda wanda zan kawo daganan za a rantsar dani anan as Chief Judge murmushi Baba yayi yace congratulations Allah sa albarka yadanyi shiru yanaso yagayamata bikin Asmeey yau saura kwana biyar koba komi itane mahaifiyar yarinyar ahankali yace nima akwai abinda nakeso nagaya miki Mom takoma da jakanta ta ijiye tace okay menene dan tasowa Baba yayi dukdan kartai fushi yace zo Salima ahankali yaja Mom yasata a jikinsa ya rungume yana shafa bayanta Mom tai lamooo, murya chan kasa Baba yace banso ni da ke mukara fada ina tsananin sonki Salima kema kinsan haka amman rayuwan nan yarana sune rayuwata inason yarana, nasan deep down ban miki adalci ba dana kama, na aurar da Asma u batare dana sanar dake ba amatsayinki na mahaifiyarta mun tattauna akai amman nai hakan ne sabida na kawo karshen rashin jituwanku kiyakuri Salima Shiru Mom tayi jikinta na radadi amman ta daure, Baba yadan kara sassauta muryansa yace ayi taron bikin Asma u nan da kwana. Biyar ashirin ga watan nan, shima Hameed zaiyi aure so tare za a hada bikinsu, daman naso kema kiyi naki taron anan ki gayyaci yan uwa da kawaye azo miki, asa albarka konawa kikeso wlh zan baki kiyi bikin nan, bazaki iya daga tafiyan sai bayan waliman bikin ba? Eh Salima ? Me EPISODE 8 Yanda Baba ke magana da Mom zaka dauka yarinya ce cikeda lallabawa, daurewa Mom tayi ta danne komi ahankali tace nasan abubuwan danayi yasa kama Asmeey aure bakomi yawuce daman abinda yasa fushina yakaru harda yaron baida sana a amman yanzu kam komi yawuce saidai gaskiya bazan iya wani taron biki ba, natarasu wace Amarya zan nuna musu yarinyar da bata hannuna? Kasan kalan burin danaci akan bikin Asma u? Anyways bakomi yariga yawuce haka Allah ya kaddara kawai abinda nake cewa shine sabida bikinta bazan fasa zuwa aiki na ba, ni da zan karbi sabon appointment zanyi tafiyana gobe, gaskiya! Shiru Baba yayi tunda dai tace takura batai hayaniya ba is the most important thing to him, anatse yace shikenan zan kaiki airport dakaina gobe, zan baki miliyan biyar wannan kaman na sauke nauyi ne na abinda na miki amatsayinki na mahaifiyar Asmeey ga kudin bikinta kema murmushi Mom tayi tana hadiye komi tace to nagode wayansa ya dauka yamata transfer 5M tai murmushi tace nagode rungumeta yayi yace komi yawuce matana haka ya kara komawa second round da third round da 4th round sai wajajen 1 yafito daga bangaren Mom din, shima zaije kano but sai ana gobe biki dole yaje daurin auren dansa Hameed, Ammi ma zataje gobe sabida kai akwatin Hameed but zatabar Ramla ta zauna da yaran da yan aiki sabida school, Ramla taci kuka cus taso taje saida Baba yasa baki yace bayan sun dawo zataje tamusu kwana biyu sannan tahakura Munir ma school bazai barsa yaje ba. Washe gari Mom tahada kaya a LV bag Baba da kansa yakaita airport yarakata har ciki yawuce yatafi yana tafita tashiga line na jirgin kano not Abuja tai kwafa tace da ni daku za aga wanda zaici wasan nan! I m going to carry my daughter! Karshen auren nan yazo! Idan ko bahaka ba cikin ni ko Hamad dole zakuga gawan daya! Kano! Mamie kwata kwata bata bama Asmeey kayan mata ba inama zata iyasha cikinta ya shiga wata na uku yanzu ne take asalin laulayi, kaniyanta takeci sosai, mugun laulayi take, batason kamshi batason wani batason any kind na smell, sau daya aka mata gyaran jiki na fata ba a kare lafiya ba, warin abubuwa yasa tadinga amai sai zazzabi saida ta jera kwana uku skin dinta irritating nata yakeyi sabida warin abun. Kowa na gidan tausayinta yake har Abba, har yayin Hamad dan Asmeey najin jiki, tuni ta ijiye kunya gefe daya dan idan tafara wani zazzabin tarasa meke mata dadi, ko ina zaka iya zuwa kaganta agidan a kwance, kwadayiko har kasa taso tafara ci Ya Mustapa yahana sabida yawu, yayyin basu taba zuwa hannu banza basu kawo mata wani abuba, kowa naji da ita kaman kwai kaman ita tafara ciki, kawai duk tausayinta suke, ga ciki ga ba miji, gata yarinya, ga babu mahaifiya tsaye akanta, yayyi sun dauka tana kasan waje, so they re taking care of her like an egg wlh, matansu ma girke girke suke suna aiko mata dashi cus cn abinci is hassle, har Zee takan mata su iloka ta aiko mata dashi, kai Asmeey na jin jiki, dudda Mamie na cikin hayaniyan biki but she s taking care of the girl very well, bama ta fita, wani sabon kaunar Asmeey take ba kadan ba, hakama Abba zai iya kira sau biyar daga kasuwa yana tambayan jikinta koyace yaga kaza ya siyamata Mamie ta tambayeta tace eh aba yaran shago su kawo gida. Gobe za akai akwatin Zee na Asmeey na gidan adakin Abba, but sai Ammi ta iso Mama ma haka duk yau zasuzo, Hamad na kula da ita sosai shima, yanda yakejin sonta da cikin nan abin yabaci kaman zai zare, shima yaune flight nasa 18th to da daddare zai iso. Tana kwance a falo babu dankwali akanta da aka mata kitso kanana jiya masu kyau fuskan nata yayi kyau tarame but tayi wani irin kyau bana wasaba hannunta rikeda cube din sugar guda biyu wanda yanzu shine abinda take masifan so yana hanata tara miyau abaki ga cartoon tana kallo a Tv Ya Mustapa yashigo gidan tareda Faisal yunkurawa tayi da kyar zata tashi zaune Ya Faisal yace yi kwanciyarki Asmeey dudda haka tashi tayi zaune taja dankwalin atampanta tasa asaman kai shi kansa Ya Mustapa is not happy da ramanta but he knows harda ciki da kewan miji she will change, zatai kiba
Chapter 101 · 0% Book details