← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 140

Sashe 29

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwallin he looks like wani aljanin misira da mahaukacin tsoro tajuya zata gudu karaf yakama bakin gyalenta bawai yawani rike da karfi bane hakan yasa gyalen yazame daga kanta gashinta suka wani bayyana ta tsaya chak batare data juyoba sai tahau kame kame. Ummm Ma Mamie tace nazo na gyara dakin su Areef sun bata bansan kana ciki ba sorry yakai kusan 5secs yana kallon bayanta which is so unlike him dan babu wata mace dayake tsayawa ya kalla arayuwanshi banda Mamin sa sannan yasaki gyalenta yatashi daga gadon ahankali yasauka yadan gyara riganshi ya saukar kasa da kyau, yasaka slippers dinshi dake wajen sannan yazo yawuce ta gefenta yafita tabi bayansa da kallo har saida yafita tawani duka tana dafa kirjinta, wat is wrong with her? Takai kusan 5mins aduke awajen sannan ta mike tsaye tawuce wajen gadon danta gyara sannan tayi shara wayanshi tagani agadon iPhone XR yar karama size na wayan, ko ita 11 pro max take amfani dashi, gently tadauki wayan, wayan kamshi, samin kanta tayi da zama abakin gadon Mamie takai wayan ahankali zuwa hancinta tana shinshinawa wayan smells exactly like him, ijiyan zuciya ta sauke wayan smells exactly like him is so calmling, vibrating wayan yayi hakan yasa da sauri ta sauko da wayan ta kalli screen din taga whatsapp message ne from number da babu suna. Please talk to me Hamadi saikuma wayan yasake vibrating another message na shigowa from same number I am madly in love with you Hussain! Aneesah ce! Hakanan wani abu Asmeey taji a wuyanta why did she even carry the phone? Maisa wayanshi ba key? Maisa notification nashi aren t hidden? Vibration wayan yasake vibrating another message ya shigo I was able to trace your house nazo ance kunzo Bauchi salla daci wuyanta yahauyi sosai tana kallon screen din kawai taga ruwa ya diga akan screen din hakan yasa da sauri takai dayan hannunta tadaura saman idanunta taji ashe kuka take daidai an bude kofan dakin dasauri ta dago kanta hada idanu sukayi da Hamad daya hade giran sama da kasa yana kallon wayansa dake hannunta da sauri ta ijiye wayan akan gado tawuce bayin Mamie da gudu ta shiga tana maida kofan tana rufewa, yadan jima tsaye awajen yana kallon kofan cus yaga hawaye kan fuskanta sannan yashigo yazo gaban gadon yadauki wayanshi yaga bata shiga wayan ba but he saw the messages shima, sake kallon bayin yayi na kusan 3secs sannan yawuce yafita yarufo kofan hakan yasa ta fito idanunta sunyi ja gadon Mamie kawai tawuce ta gyara sannan ta share dakin tass tafito da packer da broom sai sunan Aneesa ke yawo aranta kitchen ta wuce ta zubar sannan takoma daki tai sallan isha i ko ina Gwaggo take oho ita kadaice agidan su Ramla ma duk basa ta kanta toh salla ake kowa is happy wake zama adaki sai ita abincin ta dauka spoon tayi tahauci duk ranta abace yake ijiye wa tayi tadauki magungunanta dan kawai tayi bacci ta sha tarasa yanda zatayi ranta sai baci yake sai kawai taja karaman tsaki. Aneesah sunan ma ko dadi Mtsww taja tsaki sai kawai ta kwanta har Gwaggo tashigo mutane da dama sun shigo duk taki juyowa an dauka bacci takeyi nan ko baccin bai dauketa ba sai around 12 nadare. Wuraren biyar ta tashi daga bacci akan dadduma taga Gwaggo data tsareta da idanu tace sannu tashi kije kiyi salla Yayyinki Aya da Aysha duk sun kirani jiya da daddare amman kinyi bacci sunmin barka da salla sunce ki kirasu gyadama Gwaggo kai tayi tawuce bayi brush tayi ta dauro alwala tafito tazo gefen Gwaggo tai dalla data idar tai azkar sannan tajuyo ta kalli Gwaggo ahankali tace ina kwana Gwaggo washe mata baki Gwaggo tayi tace jibi yanda kika fara kumari dana dagaki daga gaban uwarki ohh wallahi Asama bakiyi dacen uwa ba sauke kanta kasa tayi tasa hannu ta dauki wayan Gwaggo dake wajen ta mike zatai kofa Gwaggo tace wayan ne har sai kin fita murmushi tayi tabude kofan tafice waje tafice tana dialing number Ya Aya da ringing daya taga an katse tana kira back Wucewa tayi parking space ta boye bayan wani mota tadauki wayan kafin tai magana Ya Aya tace Asmeeeey wani irin Asmeey taji zuciyanta yayi she missed her sister Mom ta hanata kiransu sukuma hardly calls hawaye kawai ya sauko daga idanunta da sauri tasa hannu ta share cikin muryan dake nuna tana kuka tace am ina kwana shiru Aya tayi saikuma softly tace cry cry Baby wai har yanzu bakisan kinyi girma ba shiru tasakeyi batai magana ba, dan ijiyan zuciya Aya ta sauke tace I secretly talks to Munir and nayi magana da Mom ma tasake yin shiru sannan tace Asmeey Mom has always been like this, Mom nada zafi and she s harsh but duk tana haka sabida mu zama wani abu ne, look at me I m a nurse today ga Ya Aysha kullum kika kunna TVC news zaki ganta, kalleki is all thanks to Mom kika gama Law at 20 yanzu sauranki Law school, look at Munir 400level Medicine Mom raised amazing kids kawai dai approach nata is harsh all of us know this gyadamata kai Asmeey tayi tana kuka mara sauti, Ya Aya tace ke da Munir should stop feeling kaman Mom hates the two of you, besides the Mom dana sani bata dukan daya wuce saurin kai mari idan tana koya ma karatu bakayi ba ko wani abu data saka highest ta daddakeka ajiki oh tana miki sama da haka? Lumshe idanu Asmeey tayi ita kadai tasan me Mom kemata muryanta nadan cracking sabida kuka tace Aya tace kingani ya isa stop crying ai yau zanzo Aysha ne bazata iya zuwa ba sai kun dawo daga kauye sabida sunje salla a Abuja tareda family mijinta zanzo yau murya chan kasa dake cracking tace Ya Aya please take me with you idan zaki koma dan shiru tayi tace tom nazo i will try again kaman yanda na sabayi but Mom bata bari let s see idan this time zata yarda gyadamata kai tayi ahankali Aya tace kije ki gaida Mom today wat you did jiya was very wrong and tell her sorry kinji gyadama Aya kai tayi tace ahankali Ya Aya tace akwai wani abu dakikeson gayamin ? Girgiza kai tayi tace ijiyan zuciya Aya tasauke tace akwai plenty clothes dana saya miki zan kawo miki yau harda very very fine abayas masu kyau murmushi tayi tace thank you Ya Aya nakira Ya Aysha? Ahankali tace no you don t have to I will talk to her, okay Baby Sis bye take care ahankali tace tom bye zare wayan tayi daga kunne ta kifa kanta akan kafafunta tana kuka but mara sauti batajin dadin rayuwanta at all duk ta tashi daga bacci she feels inama bata tashi ba tai tai bacci haka kawai sabida Mom saukan abu me taushi taji asaman hannayenta dake kan knees din hakan yasa ta dago kanta ahankali wani soft handky ne mai bala in taushi dake kamshi gashi so warm dasauri ta dago kanta bayanshi ta iya gani dan yawuce yana sanye da farin jallabiya ya sanya farin hula na kwankwasa kaji hadisi kamshin hanky kawai taji tasan Ya Hamad ne rike hanky tayi ahankali da hannayenta sannan ta matse takai saman fuskanta wani lumshe idanu tayi feeling super calm and warm dan sanyin asuba dukya hura hancinta kusan 1good minutes tana ahaka sannan tace mike tsaye tafara tafiya ahankali tawuce flat dinsu tabude kofa ta shiga duk yaran basa falo wucewa stairs tayi tana kallon side din Mom gabanta na faduwa tawuce falon Baba tai sallama tareda bude kofan, Baba na zaune tareda Abba duk suka bita da kallo tace ina kwanan ku Baba da Abba Abba yace Ya jikin kin tashi lpy Alhamdulillah ta amsa kanta na kasa ahankali Baba yace why did u come to this side ? Kanta na kasan tace nazo na gaisheku ne Baba shiru yayi bai kara magana ba tamike tsaye tafice side din Ammi ta wuce tabude kofa sai alokacin taga duka yaran harda su Nana da Ramla duk suna wajen tayi wajensu Ramla tace ke baccin lafiya kike tayi jiya murmushi tayi tace maganin da Ya Mustapa yabani ne daidai Ammi tafito daga bedroom dinta tace Ammi ina kwana Ammi tayi murmushi tace Asmeey yaya jikin an tashi lpy ahankali tace lafiya lau Nana ta kalla tabata wayan Gwaggo tace tayani kaima Gwaggo tana maganan tamike tayi kofa suka bita da kallo tana bude koda daidai itama Mom na bude kofan side nata suka hada idanu ta ganta tana fitowa daga side din Ammi ta dauke kanta sai kawai tajuya takoma dakin tarufe kofan yanda kirjin Asmeey ke bugawa kaman zai dare. Ahankali take tafiya tai wajen kofan ta tsaya hannuwanta na rawa takasa bude kofan handky na hannunta ta matsa sannan taji karfi da jarumta yazo mata ta daga hannu tabude kofan ahankali tareda sallama chan kasa Mom na zaune afalonta kan dogon kujera tayi crossing kafa daya kan daya ga table gefenta da sliced fruits ke kai sai wani journal haka data rike a hannu da glasses a idanunta tana dubawa ko nuna alamun da tasan mutum na wajen batayiba maida kofan Asmeey tayi tarufe ta shigo dakin tana tafiya kaman wacce akama kaciya da kyar tazo tsakiyan dakin tana facing Mom tai kneeling ta zube guiwowi akasa ko Baba dasu Abba bata musu kalan gaisuwan nan muryanta na rawa tace good morning Mom Idan banza tai motsi Mom ma tai motsi next page ma tabude na journal din datake karantawa tadauki fork na fruits taci, zuciyan Asmeey harwani girgiza yake, bakinta na rawa tace Mom dan Allah dan Allah kiyaf min, Mommy I am sorry sake bude next page Mom tayi tadauki slice na grape tasaka abaki saida ta cinye tass sannan ta sauke journal din ta ijiye akan kujera tajuyo da kanta tama Asmeey wani irin kallon kaman zatazo ta kasheta har lahira komawa baya Asmeey tayi ta jingina da kujeran wajen Mom tawani kada kafa tafara huci tadaga hannunta ta bugi kirjinta dake wani tense sound tace ni zaki gani jiya ki zubar Asmeey! ? Dasauri Asmeey ta girgiza kanta arude
Chapter 29 · 0% Book details