← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 140

Sashe 91

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauke ijiyan zuciya ahankali, cikin muryan lallashi da tsantsan so yace I am sorry Baby, kiyafemin Cikin murya mai bala in rauni Asmeey tace .tafi barni kukan is not even making her talk properly, murya chan ciki yace kinaso nakasa yin abinda nazo yi anan? Cikin muryan kuka tace ahankali cikin murya mara kwari yace kukan nan yana dagamin hankali sama da komi, I will come back soon and get u kinji ? Gyadamai kai tayi kaman yana gani yace stop crying now and wipe those tears bayan hannunta takai kam fuskan ta goge hawayen tass, murya chan kasa Hamad yace I love you alot! Wasu fresh hawaye ne suka zubomata kaman zata kurma ihu ita kawai mijinta yadawo she don t think she can do this rayuwa babu shi, ahankali yasake cewa Asmeey ganin he s seriously disturbed yasa ta gyara muryanta tace kakai gida? Murya chan kasa yace no ina mota ne ? Ahankali cikin tsananin son Hamad tace kaci abinci toh? Sanyi sosai Hamad yaji da tambayan yace no but zanci nakai gida, kinci abinci? Gyadamai kai tayi tace eh tareda Abba shiru yayi saikuma ahankali for the second time yace I miss u dan kukan datake rike taji yasake dawo mata muryanta na rawa tace yaushe zaka dawo? Allah sarki tabasa tausayi, from the way she talks kasan she couldn t hold it in any longer Asmeey is missing him kaman zatace wayyo Allah, dan dakewa yayi yace soon! But kidena kuka kinji, idan wani abu yasameki I will not be able to cope, u mean alot to me Asmeey, when u are not crying i get strength nayi all work sabida nadawo dawuri, but when I am worried sabida ke I will not be productive gyadamai kai Asmeey tayi, ta share fuskanta ta saita muryanta da kyau tace wazai kaika gida? Ahankali yace dreba dawani security personnel haka kaman escort ne gyadamai kai tayi, Hamad yace Ya Hameed yakawo miki Ice cream ? Gyadamai kai tayi tace eh, nagode murmushi yayi yace okay, me kikeso nasa akawo miki gobe ?Ahankali tace bakomi gyadamata kai yayi yace idan gari yawaye gobe i will be busy, zasu kaini police station for wasu formalities da documentation sai kuma bank, jibi shine zanje office nasu and meet with the CEO tareda lawyer na daganan aiki zai fara gyadamai kai tayi tace Allah bada sa a Yaya Ameen matar Yaya dan murmushi tayi, ahankali tace garin nada kyau? Gyadamata kai yayi yace yes yafi Nigeria kyau, u will love it here but akwai sanyi murya chan kasa tace yaushe zakamin ho .ton ..k..ka? Shiru Hamad yayi saikuma yasaki dan murmushi jin matarsa is asking for abinda yayi hating d most wato pictures amman saiyace zan miki pictures gobe in sha Allah, download Snapchat a wayanki zansa Munir yamiki adding dina gyadamainkai tayi tace okay yasake yayi shiru kafin anatse yace I have to go now, zan basu wayansu gobe I will call u with my new number gyadamai kai tayi zuciyanta yasake mata badadi kaman karya tafi saitaji kaman batada lpy, ahankali Hamadi yace Baby murya chan kasa tace uhmm anatse yace be eating and stop getting worried everything is going to be okay, we will see soon kinji gyadamai kai tayi hawaye na cika idanunta murya chan kasa yace I love you Asmeey kasa amsawa tayi ta katse wayan dasauri takifa kanta a filo tana kuka saida aka tada salla ta tashi tai asuba tahau gado bacci yayi gaba da ita Mamie ita tashigo dakin tadauki wayan Hameed dazai tafi aiki tabasa. Wuraren 10 Asmeey ta tashi da mugun zazzabi, wasa wasa Asmeey tafara ciwo rashin lafiya saida Mamie takira Musty yazo magunguna yabata da allura bayan ya duba jikinta, akace kar wanda ya gayama Hamad, rannan all through Hamadi bai iya yakira ba ko bai iya yayi sim din bane oho hakan yakara damunta kuka kawai shine aikinta. Tunda ya shiga garin they welcome him with flowers masu kyau aka daukesa awata latest tesla mobile car, wani skyscraper apartment aka kaisa lafiyayye 34th floor ne suite dinshi security yace this is ur suite Sir you can change the password anytime u want yabude mai kofan kunga gidan Hamad Ya Allah wani lafiyayen apartment ne an gyara komi harda decorating is a one bedroom glass apartment falon nada girma gawasu fararen chair ga mahaukacin fine kitchen ta gefe dayan yanunamai bedroom wani hamsakin gado an ijiye abubuwa da yawa agadon ansa welcome Mr Hamad, saikuma computer room nasa kunga computers da desktop da aka ijiyema Hamad all courtesy of Microsoft ga abinci da dama security yace make yourself at home Sir, your appointment tommorow is 10AM Gyadamai kai Hamadi yayi yawuce yatafi Hamad ya tsaya yayi shiru a katon dakin yana kallon duniya gabaki daya ta glasses din yana tunanin inama shi da Asmeey natare. Wanka yayi yabude akwatinsa ya jera komi a drawer abubuwan Mamie yaciro he s hungry cake yaci sai yazo yadan ci fruits daya gani awajen all other things bai taba ba shima kasa bacci yayi saidai barawo ya daukesa sabida tunanin Asmeey. Washe garin nan sai yamma suka dawo dan saida aka budemai komi yadawo gida ya kara gyara suit dazaisa dan gobe ne zaije aslin Microsoft office by 11 na safe. EPISODE 6 Da asubahi yatashi he s missing zuwa masallaci, jin kiran salla, one of this days zai zagaya area yaga idan zaiga wani mosque around, daddumansa ya shimfida yayi salla ya idar yayi shiru yana tunanin Asmeey, wlh abukace yake, he needs matarsa, he needs her beside him, ga sanyi yanaji, takalmin data sayamai ya kalla, sai kawai yadaura hannu saman maransa yayi addu a, Allah ya dubesa sai kawai gaban nasa ya kwanta, Al aninsa yakaranta har saida gari yasoma haske sannan yatashi yashiga bayi yayi wanka yafito yahada coffee yasha da dan dambun naman Mamie ya maida komi fridge yadawo daki yafara shiryawa. Shiryawa yayi cikin wani black suit daidai jikinsa dayamai bala in kyau, ya daura necktie yasa covershoe, kagansa bazaka dauka Hamad bane he s fair so he look American sef, kallon madubi yayi saiyaga kaman bashiba gabansa faduwa yayi, he s feeling nervous, wat if yakasa introducing software nasa da kyau? What if he got shy? What if he stutter? Agogo ya kalla is 9:58 hakan yasa ya zauna yadauki wayarsa Mamie yakira dake zaune kusada Asmeey data gama kwara amai takoma bacci, Gwaggo tace zazzabin kawazucin Hamad Asmeey keyi, tashi Mami tayi tabar dakin sannan ta dauki wayan ganin number kasan waje da gudu ta dauka tace Hamadi murya chan kasa yace Mamie kaman yana gabanta anatse Mamie tace ya kake? Ya wajen? Kana lafiya? Menene yarona? Dan shiru yayi sai chan yace Mamie gabana nata faduwa! Ahankali Mamie tace mesa? Dan ijiyan zuciya ya sauke yace yau zan fara zuwa kamfanin by 11, yanzu goma na shirya but nakasa fita ahankali yace i am scared Mamie dan murmushi Mamie tayi koda yana yaro he s very brilliant but idan an kirasa za a basa kyauta baya yarda yaje wani zubin saidai takama hannunsa yana boye fuskansa ajikinta suje, murmushi tayi tace kayi azkar yau? Gyadamata kai yayi yace Anatse Mamie tace being scared, feeling nervous is a normal thing and it s okay dan kanajin hakan! Mamie tadanyi shiru tace kahadiye fears dinka! Face it! Kaikaci gasan nan so nothing can pull you down, kaje wajen nan kanuna musu kai jarumina ne kaji Hamadi? Gyadamai Mamie kai yayi ahankali, Mamie tayi dan murmushi tace they will love you cus nobody comes in contact da Hamadi na dabazai so shi ba, a ina zaka hadu da lawyer ka da Ya Mustapa yabada ku? Anatse yace a gaban building din Mamie ta gyadamai kai tace wuce kutafi kafin kashiga wajen ka karanta Allahumma Lasahala gyadamata kai yayi yace okay saikuma ahankali yace ina Asmeey? Dan murmushi Mamie tayi taboyemai tace suna tareda Munir a parlor yasata kallon cartoon, ta warware so don t u worry dan ijiyan zuciya yasauke yace tom Alhamdulillah, bye Mamie bye Allah yabada sa karfi yaji ya shigesa yamike yadauki jakansa da laptop dinsa ke ciki yafito yawuce kofa yana budewa security na tsaye yace good morning Sir Gyadamai kai Hamad yayi, yasa hannu ya karbi jakan Hamad suka wuce kasa yau wata arniya benz aka daukesa da ita yashiga baya har champagne an ijiye masa but baitaba ba bayashan alcaholic drink, he s feeling nervous wayansa ne yay kara, lawyer yamasa message ya iso suna kaiwa suka daukesa yace Hamadi kaine ka girma haka? Adan kunyace Hamad yayi murmushi tunda yazo sai yau yaga wanda ya iya hausa shima bawani sosai ba dan anan aka haifesa, hutu kawai yake kaisu Nigeria, ciki suka shiga kai Hamad baitaba ganin kampani haka ba mai kyau, parking sukayi suka fito Lawyer mai suna Kamal ya gyarama Hamadi necktie da suit nasa yace Masha Allah kayi kyau muje security yayi gaba suka shiga elavator sai sama 15th floor sukaje kofan na budewa Hamad yaga mutane ma aikata maza da mata sunkai 100 ana tafi sosai ganinsa. Welcome Mr Hussain! Sai chan gawani mutum dayaci mahaukacin hadadden suit yazo wajen rikeda flowers yakalli Hamad dan sunada hotonsa da komi na passport yamikamai flowers yace welcome champion, Mr Hussain Hamad Abubakar! We are honored to have you here kan Hamad na kasa ya karba yace thank you Sir CEO ya tsaya yana kallonsa sai yayi murmushi love at first sight sunada wani believe na yaro mai kaman disorder disorder haka are damn genius, a resume na Hamad he made mention he s a shy person bayason too much crowd, and pictures and seeing him in reality sai yaji damn he love the guy, hannu yamikama Hamadi alamun gaisuwa dan kallonsa Hamad yayi looking somehow wired kafin ahankali yamika masa hannunsa yayi murmushi yace s go wucewa sukayi tareda Hamad lawyer da some team na biyeda su abaya, Hamad baitaba ganin conference room this fine ba zama akayi ga bottle water agaban kowa sannan aka fara main event din, aka bama Hamad main floor yamusu introducing software din kafin asalin rannan lunch. Tashi yayi daga kujera dauke da system dinsa ahankali yatafi gaban smart board ya kunna system
Chapter 91 · 0% Book details