← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 140

Sashe 6

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR OYA JOIN GROUP DINA INDA NAKE POSTING UWA KO UKUBA IDAN KINA CIKIN 1-8 DONT JOIN 9 PLEASE https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn EPISODE 3 Around 10 nadare Hameed yashigo dakin wuta ya kunna yana kallon Hammad dake bacci mai nauyin gaske yawuce bayi ya watso ruwa yafito daure da towel yaje yasa boxer kadai yazo zai kwanta ya tsaya yana kallon Hamad, saiya tashi yakai hannu yasake gyaramai bargon dayake lullube dashi sannan ya kashe wuta yahau gadonshi, ya kwanta daidai wayanshi na ringing ya daga yakai kunne murya chan kasa yace Zeezee daga tachan bangaren tace Ya Hameed baka kirani ba why is your voice so down haka kaman you are not happy wat is it ? Dudda akwai duhu juyowa yayi yakalli gadon Hamad ahankali yace my brother is sick Zee dasauri tace subhanallah your twin? Wanda akama operation last week? Gyadamata kai yayi yace yes! Murya chan kasa tace ayyahhh so sorry Allah yabashi lpy, Ya Hameed kanason twin brother ka sosai murmushi kadan yayi kaman bazaiyi magana ba yace I don t even love him as much as he loves me! Hamadi na sona sosai fa, he s not much of a talker but actions nashi speaks love, anytime I m sick baya bacci he stays all night yana kula dani, before nace kaza or nafurta i want kaza Hamad yamin is as if he reads my mind, kokuma my mind na jikinshi ne I don t know but kaman magic, saisa anytime he s sick jinake rayuwana ba dadi, sai narasa ina zansa kaina naji dadi, most times he knows we all get worked up idan baida lafiya saisa baya fada mana, he s always sick ne yau mura, gobe kai gata kaza, he feels bad yana unnecessary damunmu shi ba sikla ba, even today bansan he was sick ba cus bayaso mu damu, and bansan why I didn t noticed ba cus I m always the first to know whenever he s sick, I m feeling very bad Zee I don t give dan uwana dsame kind of love and care he gives to me Zee tace t say that, kanason brother ka sosai saisa ma har kakejin guilt din nan, anyways shi kadaine ban sani ba agidanku, bantaba ganin twins da ba a san daya ba sai akanku dariya Hameed yayi for the first time yace Hamadi baya hoto, he hates pictures, he hates cameras, bayason mutane, Grandama dinmu tace mutum daya kadai Hamadi keso aduniya Dasauri Zee tace waye? Ahankali yace Mamie! Idan kinga yadanyi few magana ko hira to da Mamie ne, gashi you will never hear meyake cemata kaman munafuki, Gwaggo always call him makiri takadirin yaro dukansu sukahau dariya yadan tsagaita yace t worry bari yaji sauki zan jawoshi muzo zance gidanku tare murmushi tayi tace okay ahankali yace bari ki kwanta we will talk tomorrow agaida Mama bye bye. Bauchi! Wai bazaki tashi ba Asmeey? Wata doguwar matashiya fara dake tsaye gaban wani gado haka mai kyau 6/7 tahau dukan wacce ke nannade cikin bargo da ba a ganinta tace kowa yatashi anyi salla an tafi aji banda ke, bazaki tashi ba sai Baba yashigo gida daga masallaci wai Husna ko motsi batayiba, baccin ta takeyi lafiyayye, bude kofan dakin akayi hakan yasa wacce ke tsaye gaban gadon ta juyo da sauri, wata hamshakiyan mace ce tsaye gaban dakin mai jiki yar gajera haka dan batada tsayi ga farin glasses a kan idanunta tana sanye da dogon hijabi har kasa mai kyau ga charbi a hannunta, tanada jiki, fuskanta babu alamun wasa, kana ganinta kawai kasan no nonsense mutane ne hakan yasa yarinyar dake tsaye gaban gadon cikin whispering tana kallon wacce ke cikin bargon ta side na idanu tace ai ga Mom nan awani mahaukacin zabure yarinyar dake nannade cikin bargon tawani yaye bargo ta taso da mugun gudu akuma firgice tana dirkowa daga gadon har tana neman fadi sabida baccin dake idanunta jikinta ba karfi amman ta dafa gado ta tsaya da kyau tana goge idanunta da gefen bakinta da duk miyan bacci, daga ita sai yar rigan bacci daya tsaya mata a knee fari fari, kanta babu dankwlali gashinta dayake a tsefe baki sidik yayi biji biji ya sauko har gadon bayanta, fara ce sosai like asalin fara dan tafi wacce ke tashinta haske ma, ba siririya bace tanada dan kiba unlike dayan da siririya ce sosai saidai tafi wacce ta tashi daga baccin tsayi da matured face alamun kaman ta girmeta, sannan wacce ta tashi na bala in kama da matar dake kofa kaman tayi kaki ta tofar, har yanayin rashin tsayin saidai yarinyar da dan tsayinta ba laifi but bawani sosai ba dan akafadan wacce ke tashinta daga bacci tsawonta ya tsaya, strictly matan dake kofan babu wasa kan fuskanta cikin wani thick powerful voice tace okay ita Ramla bata isa ta tasheki ba kinaji ana tashinki kinyi shiru right ? Baki tabude zatai magana babu wasa kan muryan matan tace idan kince uppan sainazo wajen nan na daura miki mari stupid girl! Shiru taja bakinta tayi gabanta na faduwa dum dum dum, matan tace nabaki 3min do whatever you want to do kifito kiwuce aji kona saba miki dawani irin sauri tajuya tayi bayin dakinsu matan ta kalli dayan budurwan da kanta ke kasa tace kekuma me kike jira? Oya bacemin daga sight kiwuce kitafi aji kema dasauri yarinyar tace toh Mom hijab nata dake kan gadon ta dauka tasaka da sauri tawuce gaban dressing mirror su tadauki Al Qur anin ta tazo wajen sai kuma takasa wucewa, babu wani yaro in this house da baya shakkan Mom kawai ajininta abin yake, she s so scary cus bata da wasa and batason nonsense even a bit, ganin haka yasa Mom tajuya tawuce tabar wajen itakuma Ramla tafito, Babban gidane sosai tashiga sauka kasa ta sauko falo tabude kofa tafita gidansu is a very biggggg house, ga flats daban daban chan tawajen masallacinsu akwai wani katon class tawuce direct tabude kofa tashiga yaran gidan su ne ciki, 6boys ne awajen akwai dan 20yrs sai sauran duka kanninshi ne sai kuma mata yan 8yrs, da 9yrs sai ita datashigo ta zauna tana sauke ijiyan zuciya ganin Malamin su bai shigo ba yar 9yrs din tace Ya Ramla ina Ya Asma Yar 8yrs tace hmmm Ya Asmeey ai bata tashi ba, Allah yasa Malam yamata dukan latti jiya daman ta dakeni ballamata harara Ramla tayi tace zan fasa miki baki fa, wayace ki taba mata hoda ba saisa ta dake ki ba turo baki tayi tajuya ta cigaba da karatunta daidai nan Malaminsu ya shigo wani Ustaz ne da dingilallen wandonshi yasa hula akai ga dorina akan kafadarshi ko kadan baya ragama anyone cikinsu wanda hakan umarnin Baba ne saisa suke tsoronshi ba wasa duk wacce tai latti ko takasa bada hadda akwai duka although hadda Saturdays and Sundays suke bayarwa, baice komiba yawuce gaban aji ya zauna zauna. Tana shiga bayi ko brush batayiba tafito tasa hijabi tai salla ko azkar batayi ba ta mike tsaye tadauki daddumanta ta ijiye kan gadonsu tadauki Qur anin ta tazo kofa tafito gabanta na faduwa sosai ta shiga sauka kasa tafito tawuce class ta window ta leka ganin Malam yana aji haba saita kasa shiga idanunta take sukai ja, masallacinsu ta kalla tasan Baba na ciki but dazaran tawuce zata shiga masallacin Malam zai hangota hakan yasa tajuya takoma flat nasu tabude tawuce kitchen nasu tana bude kofa taga wata mata but bata dazu ba wannan looks exactly like Ramla tareda wasu mata da kana ganinsu kasan yan aiki ne binta da kallo matan tayi hakan yasa arude idanunta sunyi raurau tai wajen matar kaman zatai kuka tace Ammi wani kallo matan tamata tace yauma kin sake latti ko Husna saiga hawaye kaman jira take tace Ammi dan Allah kisani kowani aiki zanyi I will even cook abincin lunch din su Yusra saikicema Malam kene kika sani aiki yau su Gambo basajin dadi basu tayamu aiki ba kinji Ammi wlh dukana zaiyi Ammi na kallonta tace inaji ana tashinki fa kikai shiru Asma u? Mesa bakiji kullum kece ke latti eh kinsan idan Baban ki yazo yaganki a kitchen din nan ranki harda nawa saiya baci da safen nan dan haka wuce kitafi kibama Malam hakuri kinji girgizama Ammi kai tayi kawai tasaki kuka zatai magana cikin kakkausan murya akace Asma juyowa tayi arude ganin Mom ce saida kirjinta yayi mugun faduwa kawai tafashe da kuka sosai taboye bayan Ammi tace na shiga uku wayyooo Allah Ammi Mommy zata dakeni mari na zatayi Ammi dan murmushi Ammi tayi tace Mommy dan Allah kimata hakuri kada ki tabata yanzu zata tafi kinsan Asmeey akwai tsoron duka Mom zatai magana duk sukaji muryan Baba. Meke faruwa awajen nan? Duk juyawa sukayi daidai Baba na karasowa wajen ya tsaya dab da Mom yana kallo kitchen din yana jiyo kukan Asmeey, yan aiki duka suka gaidashi but baima iya amsawa ba yace meke faruwa? Meya faru Asma u ke kuka? Mesa bataje makaranta ba ? Cikin kuka Asmeey tace Baba Mommy dan kallon Mom yayi dake kallonta rai abace saikuma yakalli Asmeey dake lekowa daga bayan Ammi yace zonan ba musu ta taho ahankali tana goge fuskanta da tasan Baba bazai taba dukanta ba baya dukansu, agabasa ta tsaya kanta akasa yace mena gayamiki kan zuwa aji latti da asuba ahankali tace kace nadena? Baba yace so danazo na tadaku kika tashi kika kalleni ina wucewa natafi daman bacci kika koma? Fuskanta tashiga gogewa takasa magana, Baba dake kallonta yace kinaso ki gamu da fushina ko ? Girgiza kai tayi tace Baba bazan karaba kayakuri shiru yayi yana kallonta saikuma yace zoki wuce kitafi bakinta na rawa tace Baba Malam zai dokeni saikuma ta rushe da kuka Mom tamata wani kallo dayasa tayi kan Baba zata shige jikinshi Baba ya kalli Mom hakan yasa ta dauke kanta tawuce tashiga kitchen din shikuma yace wuce muje ba musu tabishi suka fice tana murmushi, har ajin nasu yayi sallama Malam ya amsa yana tasowa Baba yace basai ka tasoba Malam kaga Asma u sai kuka take sabida tasan tayi latti amata afuwa adaga mata kafa nayau gobe tayi latti amata hukunci murmushi Malam yayi
Chapter 6 · 0% Book details