Sashe 20
Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn EPISODE 9 Dakinsu ta shiga bayi tashiga tai wanka dan batai wanka ba tun safe fitowa tayi tabude sip taciro wani gown na atampa mai kyau yanada blue floweres shiryawa tsaf tayi tasaka sannan tazo gaban madubi takalli fuskanta har lokacin fuskan yayi ja sai kawai taji har kunya kunya takeji ma tafita mai ta dauka ta shafa a fuskanta sannan tazo dauki kwalli tasaka duk dan tai looking normal hakan saiya rage redness na fuskanta amman saitayi bala in kyau gashinta ta warware a wanke yake har tsakiyan bayanta gashi baki gwanin kyau batada full gashi sai tsayi but is scanty and silky combing tayi sai kawai ta dauki blue veil ta yafa tadan fesa bodyspray dinta ta tashi ta kalli madubi murmushi tayi saita fito ta sauko kasa babu kowa a falo saita fita tana tafiya ahankali zuwa wajen masu kitso Ramla dahar an gama mata kitso tace wat happen to fuskanki? Zama tayi kan tabarma tace faduwa nayi laaaa lallinki yayi kyau Ya Ramla tai maganan da sauri dan ta kauda maganan, takalli lallin Yusra tace Yusri iyyeee Irin naki za a min Yusri ta washe baki Amina tace Ya Asmeey kiyi irin kitsona dasauri tace shiko zanyi Yusra tace ga Mom tafito wani kalan faduwa gaban Asmeey yayi da sauri ta sauke kanta kasa Mom tashiga tahowa wajen fuskanta kaman bata taba dariya aduniya ba tana sanye dawani simple gown na Cotten irin na Egypt din nan masu manyan mayafi sai wani mashahiurin kamshi take idanunta akan Asmeey dataga tai wanka harda chanza kaya, Yusra na ganinta tayi murmushi tace Mom saura ni ana gamama Amina za amin kitsona asamin beads Amina tace Mommy lalle na yayi kyau dan murmushi kadan tayi tace yayi sosai takalli Asmeey da kanta ke kada cikeda authority da isa da iko tace ayi miki kitso only banda lalle ba Asmeey kadai ba hatta su Yusra yara da su masu lallen da masu kitson da Ramla saida suka kalli Mom, wani iri Asmeey taji cus tanason lalle duk salla Allah yasani lalli da kitso da saka sabon kaya are the measure things she looks forward too, amman saita gyadama Mom kai ahankali muryanta nadan breaking tace .toh Mom strictly Mom tace good! You re going to law school bayan sallan nan, henna kowani iri is not allowed sake gyadama Mom kai tayi ahankali kanta akasa, Mom tajuya tawuce abinta batare data kara kallonsu ba tana tafiya kaman itace mai gidan masu lalle da kitso suka bita da kallo asace ana mamakin gadaran matan, duk yanda Asmeey taso ta daure takasa kawai saiga hawaye sharrr dasauri takai bayan hannu ta share kafin wani ya lura dan kanta na kasa, me lallen tace menene law school Ramla? Ahankali Ramla tace makarantan dakake zuwa kazama cikakken lawyer, da gaske ba a barin lalle mai lallen tace amman ai yanzu lalle nan da nan yake gogewa kuma shampo na goge lalle lokacin yayi aisaita goge lallen Ramla tace tunda Mom tace kartayi kartayi mubar maganan nidai Asmeey tai shiru zuciyanta baya mata dadi kawai kitson ma kaman kartayi but tasan Baba zaiyi magana, haka aka gama na Yusra sai akahau mata kitso shiku mai bala in kyau yan kanana ana cikin mata Kawu ya iso daga Gombe. Tashi duka yaran sukayi bata tashi ba Ramla tace tashi muje mu gaida su Kawu ahankali ta tashi suka wuce wajen motansu, wani magidanci na mai kama da Abba na Kano sosai tareda wata mata da yara mata, Matar tace ana kitso ne Asmeey ba a gama ba dasauri Asmeey tace eh Mama ta rungume Nana da Baby tace Nana, Babyyyy suma suka rungumeta Nana is 15, Baby kuma 12 sai sauran yaran Maza ne guda hudu, daidai nan Kawu ya gama magana da masu gadi yazo wajen yaran duka suka gaidasa idanunsa nakan Asmeey yace meya sameki a fuska Asma kafin tai magana Yusra tace faduwa tayi Kawu ahankali yace sannu bakiji wani ciwon bako gyadamai kai tayi tayi murmushi still ya tsareta da idanu dan kaman mari daidai Baba na fitowa daga flat, Mom da Ammi kuma suna zuwa daga backyard, wani kallo Mom tama Asmeey hakan yasa tajuya ahankali tawuce takoma wajen kitso, Baba yayi hugging dan uwansa cikeda farin ciki suka shiga gaisawa while masu gadi na kai kayansu side nasu, Asmeey takoma wajen kitso tazauna aka cigaba tana kallon yanda kowa ke murna, su Nana suka taho wajen basuyi lalle ba suma Ramla tace kuje kuhuta ku chanza kaya kar lallen yabata wannan sai kuzo amuku wucewa sukayi dan chanza kayan. Suna chanza kaya suka dawo, suna cikin kitson Munir yazo wajen kaman bacci ma yayi dan idanunsa yayi ja bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey ana mata kitso ba dudda yana ganin fuskanta yasan aikin Mom ne yazo wajen yadan harari Nana dake kallonshi yace ni tsaran wasankine kike kallona kallon Ramla Asmeey tayi Ramla ma takalli Asmeey suka wani kwashe da dariya bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey tayi dariya ba, Ramla tace sannu Ya Munir itakuma Nana jibi yanda tawani sunnar dakai kaman irin Ya Mustapa asalin Babban yayanmu namata magana hararan Ya Ramla yayi yasake tamke fuska sosai shi adole babba sannan yakalli Asmeey yace Mom is calling you yajuya abinsa, faduwa gaban Asmeey yayi sosai ta tashi da rabin gashi akitse tawuce Nana tadan saci kallon Munir da tun tana yar karama take sonshi Ramla tace dalla kidena tsoronshi murmushi tayi tace cikamin ido yake Ya Ramla baki Ramla tabude tace Munir din ahhh babban magana shigowa falon sukayi ga Baba da Kawu akan carpet sunashan shayi dake kamshi sosai Baba dake kallon Asmeey tun shigowanta yace ina zaki da gashi haka ba kallabi da sauri ta taba kan tace Mom ke kirana yanzu na manta da kallabin wajen kitso ne gyadamata kai Baba ta wuce sama afalon Mom taga Mama, Mom na shiri da Mama sosai da Kawu but Mamie kano ne dai basu cika shiri ba dakuma Abba suma bawai fada suke ba kawai dai haka suke sunfi shiri da Ammi su, Mama dakecin samosa tace Hajiya Salima I trust you dan Allah Asmeey ma ki sama mata gangariyan miji gaskiya dan matar manya ce yarinyar nan ga kyau ga diri dudda naga sai karewa take maybe zullumin zuwa law school ne akunyace Asmeey tadan sauke fuskanta kasa, Mom tahade fuska tace zonan rawa hannayenta suka fara har Mama saida ta lura amman taja baki tai shiru kafin ta shiga black book din Mom, wucewa Asmeey tayi gaban Mamanta wani kallo Mom tamata tace wuce ki daukomin kayan dana dinkama Maman ki da wanda na dinka miki dasu Nana wucewa tayi bedroom din Mom, Mama tace ohh baki gajiya Hajiya Salima! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah kara girma da daraja kawo kayan Asmeey tayi bakin Mama har kunne Mom nada kudi so manyan exclusive atampopi ne Mama tace Allah dai yaja zamaninki wlh Babansu Aya shi kanshi yasan yayi dace saisa har yau har gobe kece yar gaban goshi, Aya zatazo namata godiya ko, mijinta ya fitar da zakka dubu dari biyar ta aikamin wlh murmushi Mom tayi na isa irin abin nan takeso Asmeey ta kalli Mom tace Mom natafi ? Mom tace yaron nan has been calling you go and talk to him kafin ki koma wani iri Asmeey taji, badaman yakira bata dagaba saiya kira Mom, wucewa tayi tafita daga dakin, dakinsu ta wuce ta zauna kan gadonsu tadauki wayan taga 5miss calls nashi, instead of takirashi back sai kawai ta kwanta ahankali kan gadon tarike wayan a hannu within 2mins bacci mai dadi ya kwasheta cus tun asuba data tashi bata koma bacci ba tana wajen Mom, kusan 1hr tana bacci sannan wayanta ya shiga ringing firgigit tabude idanu tana tashi zaune tana mamakin yanda bacci ya saceta haka, daukan wayan tayi takai kunnenta ahankali tace hello Wifey how are you ? Abu taji ya tokare mata wuya she hates d name sosai, da kyar tace fine yana murmushi da tana iyaji a muryansa yace sorry banzo ba har yau ban dawo garin ba sai yau, ya shirye shiryen salla ni da Mommy na zamuzo washegarin salla gyadamai kai tayi batace komiba cus bama tasan mezata ce ba, matse murya yayi yace I can t wait to see you my wife Asma wani iri jikin Asmeey yamata ta runtse idanu, Fawaz yace kullum sainaga fuskanki a bacci, I don t know why I love you this much, me kikamin ? Kin magana tayi Fawaz yace wai yaushe zaki dainajin kunyan mijinki eh? Relax and talk to me babu abinda yakai muryanki dadi arayuwana ? Murya chan kasa mai dari dari tace kitso akemin zan koma akarasa dan shiru yayi he feels kaman bata sonshi but he don t care, ahankali yace okay kije toh zan kira anjima take care dasauri ta katse wayan ta ijiye wayan akan gado tanemi another blue veil karamin veil tadaura saman kanta sannan tafito Ammi tagani tana fitowa daga dakinta kaman itama ta hauro tai salla ne ganin kanta bangare daya himm bangare daya a kwance tace meya faru ba a gama miki kitso ba har yanzu Asmeey kowa yayi nashi kitson agidan nan? ahankali tace Ammi bacci ne ya kwasheni a daki hararanta Ammi tayi tace wuce ni kafin in mangareki awajen nan yarinya kaman mage wucewa tayi tafita sauka kasa Ammi biyeda ita tabude kofa tafice Baba tagani da kanshi yana bude gate murmushi yalwace a fuskanshi, motan su Abba na danno kai dan nasu ne agaba hakanan gaban Asmeey yawani fadi shigowan motan zaro idanu tayi tace Ammi Gwaggo ta iso ? Daidai nan yaran wajen lalle harda su Ramla da Munir dake wajen dasu Nana suka kwaso da gudu suna ihun. Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyoooo Kashe motan akayi Abba ne yafara fitowa yana sanye da manyan kaya da charbi a hannunsa atare duka yaran gidan sukai kan Abba. Abba oyoyoooo! Abba yabude hannunshi dukan uban yaran ya rungumesu, Mamie ma tafito ta zagayo ta dayan bangaren yaran suka saki Abba ta zago ta gaban motan suka rungumeta, Ammi dahar ta wuce tajuyo takalli Asmeey dake tsaye tace wuce muje kiyi gaisuwa hakanan kawai saitaji tabajin kunya da nauyi