← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 140

Sashe 46

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

M SHAKUR
EPISODE 2
Tashi tayi tawuce wajen window tadaga labule taga Baba yafito tareda Munir sun wuce masallaci chan saigasu Mustapa sun wuce chan kuma Kawu da Baba da Hameed, chan dan har anje ruku
u saiga Hamad shima yafito, Mom ta tsare Hamad da idanu tana gyara glasses nata tana kara karemai kallo, he walks one step at a time da bala
in natsuwa sai wani sheki yake kaman ma wanka yayi, hulan kwankwasa kaji hadisi ke kansa da faran jallabiya, yayi wani irin kyau yana tafiya, tsayawa taga yayi chak duk Mom na kallonsa to her biggest suprise saitaga Hamad yadago kansa sama ya kallo exactly directly window ta chan saman bene sun hada ido, sauke kansa kasa yayi anatse yacigaba da tafiya, Mom tace
mahaukacin psycho, I said it, yaron nan yanada mental disorder normal people sun wuce no body notice me but he did, this are signs na masu mental kolo kolo brain yawan lura ina chan sama tsaye wajen window but jikinsa ya gaya masa ina nan, my daughter will never join blood with you
Saida Hamad ya shiga masallaci Mom tabar window tafada bayi tayi wanka tafito tabude wardobe, wani shadda gzinar taciro royal blue dayaji aiki da duwatsu sannan tayi salla tazo ta shirya tsaf takafa wani dauri mai kama da mafici sabida fadi ta kafa glass din nan tafesa turare takoma tazauna tana kada kafa karyansu tasha karya.
Gabaki daya half half tayi baccin jiya she
s trying to wrap kanta around kalman aure da Baba yace yamata, ga damuwa batasan ko Mom ta yarda ko bata yardaba dan tasan Mom basa shiri da this people gashi tun ranan yawon sallan bata sake ganin Mom ba, then ga Ya Hamad, tunaninshi ya addabi zuciyanta kawai fado mata yake arai nonstop, he
s living rent free in her head, her mind, and her heart so duka duka sai asuban nan tasami bacci. Shigowa dakin Mamie tayi dahar tayi wanka ta shirya dan so suke by 8 zasu wuce wajen gadon tayi tana kallon fuskanta she looks so beautiful while sleeping dudda bata gama warkewa ba har yanzu fuskanta da ragiwan ja Mamie tayi murmushi aranta tace
Hamadi na ya auri kyakkyawan yarinya
azahiri kuma tace
Asmeey Asmeey
bude idanunta Asmeey tayi ahankali Mamie tasa hannu tadagota akunyace Asmeey ta sunnar da kanta kasa kawai yausai taji tanajin kunyan Mamie ita kanta Mamie saida ta lura abin yaso bata dariya tace
ni zaki fara wani jin kunya aiko zan mangareki awajen nan
adan kunyace tai murmushi still taki kallon Mamie, ahankali Mamie ta matso saikuma gently ta rungume Asmeey, Asmeey tawani boye kanta jikin Mamie, patting bayanta Mamie tayi tace
Assalamu Alaykum Daughter na!
Runtse idanunta Asmeey tayi da sauri, Mamie tace
I am so lucky d
ana ya auro mini the most amazing and special yarinya kap duniyan nan Asma
Kaman Asmeey zata nutse akasa Mamie tace
Allah ya sanya albarka a aurenku Asmeey, Hamadi yarone na kwarai dana tabbata wata rana zakiyi alfahari kasancewanki matarsa, tashi kiyi wanka kiyi salla Asmeey yau zakije gidan mijinki
kankame Mamie Asmeey tayi kirjinta na bugawa kawai taji she
s having goosebumps, is she happy she
s married to Ya Hamad? Ta tambayi kanta cus bamata san ko farin ciki takeji ba wlh, but one thing she can say for a fact is ko bakinciki daya bataji na an auramata shi, ko jin haushi not at all, batajin hakan but kuma batasan ko she
s happy bane but then she doesn
t feel sad so she finds the whole of abinda takeji wired and creepy feeling da bata taba experiencing in her life ba
Ganin taki sakinta yasa Mamie tace
ko muje bayi na miki wankan ne?
Dasauri ta girgizama Mamie kai, Mamie tace
to sakeni
ahankali tana kirjin Mamie cikin whispering tace
kunyanki nakeji Mamie
kwashewa da dariya Mamie tayi sosai and she
s so suprise dabataga any sadness regarding aurenba sai kawai taji alakanta abin da yarinyar tagaji da azaban mahaifiyarta saisa take farin ciki da auren, Mamie tayi murmushi tace
cikani naje bayi nasamiki macleen a brush sai kiyi wanka nakawo miki kari kiyi nasan yanzun nan Gwaggo ma zatazo
ahankali tasaki Mamie tana wani juyar da kanta Mamie ta kadakai tawuce tabude drawer dakin inda Aya ta ijiye ma Asmeey kayan dazata saka yau tabi hanya tace
zan kiramiki Ramla ta tayaki
Mamie ta shiga bayi tasamata toothpaste tafito tace
tashi kije
saukowa daga gadon tayi ahankali Mamie tajuya zata fita ahankali tace
thank you Mamie
tawuce bayi da sauri
da kyar ta iya cire rigan jikinta da kanta da hannu dayan tayi komi da komi tafito Ramla tagani zaune kan gado tana mata murmushi sosai tace
Amaryan Ya Hamadi
cus Munir saida yagaya mata jiya but amana dan he couldn
t contain her joy kaman zatai kuka taturo ma Ramla baki tace
ni ba amaryan kowa bace nidai
Ramla ta tashi tana daukan cream tana zuba mata a hannu itama tana sawa tashiga tayata shiryawa ita ta tayata saka hook na bra abaya sannan tasaka gown na atampa mai kyau free dinki ne bubu sabo a atampa Ami kyau dauke kai tayi da sauri saikuma batace bataso ba ganin haka sai kawai Ramla tafice da sauri taje dakinsu tana mamaki chan tadawo da jakan makeup nata ta zauna kan dadduman taciro kwalli tace
bari mufara sashi
tsaf Asmeey ta tsaya tasamata sannan ta shafamata lip gloss bakinta sai kyalli yake Mamie tashigo da tray na tea da chips dasauri Ramla ta tashi ta amsa tace
Mamie kawo
Mamie takalli Asmeey da taga Ramla na mata kwalliya sai kawai Asmeey ta chanza a idanunta, she looks big and matured bubun atampan data sane ko auren da aka mata ne oho but saita chanza, fita Mamie tayi tabasu wuri bayan tace
tadaure taci
Ramla tace
ci sai mu cigaba
chips tasa hannu ta dauka taci saikuma ta kalli Ramla tace
tayani ci muka gama ki shafamin hoda Ya Ramla
ahankali Ramla tace
Asmeey kinason Ya Hamad ne dama?
Dasauri Asmeey ta kalli Ramla sai tafara kokarin magana takasa batasan mezatace ba lips dinta suka shiga rawa da kyar tace
baki Ramla ta tabe tace
munafuka! Wlh kina sonsa cus u look happy today zakibar gidanmu
tass suka cinye Ramla ko ta shafamata hota da abubuwa da dama Asmeey bata hanata ba harda shafa mata eye shadow, tashafa mata janbaki pink tunda taga tanason amata makeup din, tadauki dankwalin atampan tamata dauri mai bala
in kyau sannan tadauki gyalen ta gold tayafa mata bayan tasaka mata da kunne masu kyau takawo mata takalmi flat shoe ta feffesa mata turare sai kawai ta tsaya Tana kallon Asmeey tace
wlh lalle da karayan hannun nan yayi hindering having that full Amarya look but kinga yanda kikai kyau Asmeey zoki kalli madubi
ahankali Asmeey takalli kanta amadubin kaman ba itaba tama kanta kyau kwalliyan da Ya Ramla tamata kaman wata professional makeup artist faduwa gabanta yayi dasauri tace
Ya Ramla mu gog
shigowa dakin Munir yayi yana washe baki ganin Asmeey saiya tsaya chak kaman ba Asmeey ba she looks exactly like Matar aure, like Amarya, tayi wani irin kyau looking very very matured, da kyar yarufe kofan yataho wajen baiyi wata wata ba kawai ya rungume Asmeey sai kawai ya fashe da kuka Ya Ramla tace
yasin zanje nakira Nana taganka kana kuka
dasauri yadago kansa daga jikin Asmeey idanunsa sunyi jazur duk ruwa ya harari Ya Ramla datai dariya ta kwanta kan gado tana kallonsu sannan yakalli Asmeey da duk saitai wani iri for the first time tunda ta farka saitaji kuka yazo mata amman tadaure, ahankali takai hannunta saman fuskanshi tana gogemai idanunta na tara hawaye tace
na yafemaka duka kudadena dakaci bashi da wanda na baka ijiya
haba Ramla da Munir sai dariya kyakyakya kaman mahaukata, Asmeey tai kwabe kwabe da fuska tana kallonsu tace
to biyani kudina
UWA KO UKUBA?
Chapter 46 · 0% Book details