← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 140

Sashe 72

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma yahuta! Kinaso ki mutu! ? Hamad yafada azafafe, Asmeey tayi wani ihu da zakin muryanta yadauki gidan tace yessss, ni kabarni na mutu me ruwanka dani! Daidai su Ya Mustapa na fitowa cus Hamad yabar kofan abude they could here them, Abba biyedashi da Gwaggo da gudu jin hayaniyansu da sauran yayyinsu dasauri Abba yashiga tsakiyansu yana kallon yanda Hamad kewani irin huci yana kallon Asmeey itakuma kanta akasa tana kuka sosai tana goge fuskanta da bayan hannu yace menene Hamad? What happened ?Dukawa Ya Mustapa yayi yadauki ledan maganin yace munada rat poison agidan nan ne? Hamad ka sayo rat posion ne akwai bera adakinku ne? A mahaukacin zuciya Ya Hamad yace ask her Yaya? Ya Musty yakalli Asmeey zaiyi magana Abba yariga sa yace an ina kika samo maganin bera mezaki dashi? Kanta akasa ta daure ta danne kukan datakeji tace ci zanyi Abba ci Asmeey? Ci zakiyi ? Gyadama Abba kai tayi tace Abba so nake naci sainai bacci kawai namutu a baccin kowa ya huta at ..atl tafashe dawani irin kuka tace Abba at least kaga na mutu Mom bazata dinga zuwa gidan nan tana hurting Mamie ba kowa saiya huta, you all don t have to be angry with me abarni ni kadai, basaikun tsaneni ba dudda maganan Asmeey harda yarinta amman saida Abba yayi mutuwan tsaye haka sauran ma! Hamad da kirjinshi ke zafi yace you think tsanan ki akayi? Wayake da time na tsanan ki acikin mu ? Ahankali tace amman ai kun tsani Mom so tsananta ya shafeni, I get it I know Mom hurt Mamie that was very wrong but Mamie tafara pushing Mom, I was telling Mamie tabarmu da Mom karta shiga but she was not listening to me, but kowa hates my Mom and kun tsaneni nima cikin tsananin fushi Hameed yace ke kindaisan apart from being Matar Hamad ke kanwarmu ce ko idan kikamana shirme anan i will come and beat nonsense comot from your body tunda maybe bugamiki kai da muguwar matan nan tayi jiya yataba miki brain cikin wani irin kuka tace everybody is beating me! I am nothing! Ni ba kowa bace, kowa treat me like Asmeey is just bag of dirt, banda daraja na yar adam, i told you banga amfanin rayuwana ba I just want to die and rest, na tabbata mutuwa yafi rayuwana sauki Gwaggo tace ba shakka maganan Hameed asama kin haukace wallahi, uwarki takawo miki maganin bera dai tace kici shine kike fakemana da bama sonki yooohh dan ubanki inbanda ke jakace Mamie ta ture mahaifiyarki sabida ubanwa tayi? Ba sabida taga ana kokarin kasheki bane? Juyawa Asmeey tayi zuwa wajen wardrobe kawai tace tunda kun hanani kashe kaina I m living Kano zan koma gidanmu, bansan dalili na Mamie takara jin ciwo or got hurt kutaru ku tsaneni abar ni kadai adaki ba, I m living this house dasauri Abba yayi wajenta cus all he sees is small little yarinya with no exposure in pains and feeling guilty and insecure hannunta yakama cikeda lallashi yace My poor child Asmeey babu inda zaki cikin kuka tace Abba bazan iya auren nan ba! Bazan iyaba Abba zuciyana ba dadi I can t do this Abba barin gidan nan zanyi fine! Hamad yafadi cikeda zuciya kaman kuturu, Asmeey takalleshi tana kuka ahankali, jikinshi ya shiga tattabawa yaji babu kudi saiya juya yawuce wajen bagpack dinshi yabude ya kwaso duka cash din dayake dasu cikin sunkai kusan 30k yataho zuciye kowa na kallonsa yawani kalan jefa kudin akan gado yace pack your things kitafi ga kudin mota! Yajuya zai tafi atare duka yayinsa da Abba ganin Hamad ya zuciya sosai sukace Hamad! Asmeey ma takalleshi sosai idanunta sunyi jajur zuciyanta kaman zai fito takara harkuza, amman Hamad ko juyowa baiyiba yayi kofa zai fita Hameed da Faisal suka tare kofan ya tsaya chak yana musu wani kallo yace kutashi daga kofa na fice Abba yace Hamad badakai nake magana ba juyowa yayi idanunshi sunyi jaa yace Abba tace she wants to go tagaji she s not doing again nabata kudin mota ta tafi what else? She thinks she s the only one hurting anan? She wants to commit suicide ko? Tayi parking things nata ta tafi Bauchi taje tayi achan? She s blaming Mamie na that stood for her how dare she! She thinks all of us bama sonta? She feels we are angry with her? Tace anbarta ita kadai did she know who my mother is to me?Comparing wani abu kike ko measuring something? Cikin kuka Asmeey tace bazan taba comparing komiba, I love Mamie sama da yanda kuke sonta ma, ina tashi ita nafara tunawa I went straight naduba ta naji maganganun da akeyi har ana cemai yazo wajena yaki! Why will I come? Mezanzo namiki? Are you that insensitive Asma u dazaki bude ido and conclude anajin haushinki you think everyone is like your mother Salima! ? Kallon Hamad Asmeey tayi maganan sa sunmata zafi sosai shima kallonta yake maganganunta sunmai zafi, kan kowa na dakin yadauki chaji, bayan hannu Asmeey takai tashiga share fuskanta tana kara yarda yes bakin Mom ya bita especially maganganun da Hamad ya gayamata yau, saita kalli Abba dayama rasa tacewa tace Abba I know not everyone is like my mother but she s still my mother ba yanda zanyi! I can t stay da mijin da baya girmama uwata ba! Koba komi yauna fahimci dalili guda da Mom batason auren nan Ya Hamad ya tsani mahaifiyata sosai and kowama ya tsaneta kaga ai aure bazai yu ba nahakura! Azuciye Hamad yace nima nahakura! Go and marry your Mom Kai! Kowa saida yakalli Hamad yawuce kofa ganin yanda ya zuciya zai iya barar da Hameed da Faisal yasa suka matsamai yabude kofa yafice fiuuuuu. Gwaggo tace lallai Asama yau kin gwadamin ke diyar mahaifiyarki ce Salima indai zaki bude baki ki gayama mijinki maganganun nan, yaron da duka azaban yajin da uwarki tasamiki saida kika gogamai ajiki kin manta ko? Anan ya kwana zaune dake bai runtsa ba, sabida ke Hameed saida ya hakura da aurensa mun zauna za a fara magana kenan yakiramu kan mahaifiyarki tazo Hameed yabar aikinsa na baki duk sabida muzo mu ceceki kice mana bamu sonki haushinki mukeji, Mamie na kwance gado allura na uku kenan Docta ke mata amman ki bude baki kice laifinta ne mesa ta shigan miki itace ta fara tura Uwarki, da asuban nan kafin muje dakin Mamie dukan mu muna nan muka dubaki doctor yaduba ki kafin muwuce dakin Mamie, na mance dudda jiya Mamie na layi saida tabi Hamad bayi ita tamiki wanka ta wanke miki yajin jikinki da ruwan gishi da kankara amman Asmeey godiyan dazaki mana kenan! Kin nuna mana taki kalan kitafi Allah yakiyaye hanya dasauri duka yayyin Hamad suka kalli Gwaggo harda Abba suka mata wani mugun kallo, tace Allah sa hakane mafi alkhairi kije idan darabon zamu sami jana izar ki bayan uwar ki ta halakaki zamu samu, kije Gwaggo tajuya tafice Hameed yafice Faisal yafice Ya Abdullahi yafice dakin yarage daga Abba sai Ya Mustapa ciki. Asmeey tajuya azuciye zata cigaba da ciro kayanta na sip saikuma taji takasa sai kawai takifa kanta a kofan wardrobe din tana wani irin kuka mai bala in sosai zuciya tabama Abba da Ya Mustapa tausayi Abba yariketa yakamata saiya zaunar da ita akasa yakalli Mustapa yace bani goran ruwanchan kagani dasauri Ya Mustapa yakawo bottle water dake kan desk yabude yabama Abba ya karba tofa addu a yayi ciki na sanyaya duciya yadafa kan Asmeey yace sha ruwan nan da kyar Asmeey ta iyashan kadan Abba yacire ruwan daga bakinta yashafa kanta yana kallon yanda take wani irin kuka ta taba zuciyanta tace Abba na shiga uku na lalace wlh na bani Abba, Abba zuciyana yanamin kaman yafi komi na duniyan nan nauyi, Abba mutuwa baifimini ba da irin yanda zuciyana keyi? Eh ? Abba yace kowani dan Adam da tasa kalan jarabawa aduniya kuma kashe kanka da kanka haramun ne wuta zaki shiga direct sannan kinyi wahalan banza, kingama wahala na duniya kisha wahala dan Allah baya karban ran wayanda suka kashe kansu ta sauki, kikagama wahala ki mutu kije kabari ki wahala kije lahira ki wahala toh ina dalili? Asmeey ina tauhidin ki? Ina tawakkul dinki? Ina Imani da kaddara dinki mai kyau da mara kyau? Ina yarda cewa komi daga Allah ne? Eh Asmeey? Tana wani kalan kallon Baba face Abba yaya zanyi kasan yanda zuciyana kemin sabida abinda Mom tama Mamie? Abba abin yamin ciwo sama da kowa, Abba kaga sabida ni Baba yasaki mahaifiyata! Sabida ni Mom bata magana da Ya Aya, bata shiri da Munir! Munir haushin Mom yakeji sabida ni! Sabida ni Mom ta tsaneku gabaki daya! Abba everything is happening because of me, this beautiful house, this beautiful family da kowa ke murmushi kullum baku fada bakujin haushin kowa yau because of me sabida kun shigo dani gidan nan komi ya chanza! Abba I think ni kambun baka ce duk inda na taka ko na shiga fitina na bini banda good luck, bantaba jin ance Mamie batada lafiya ba but sabida ni Mamie na gado ba lafiya everything s na faruwa because of me me me me meeeeee, Abba Abba ku barni natafi I don t want to be reason dazaisa wani abu yasami Mamie koya sami gidanku koya sameku, Abba ni yar Mom ce kome tamin is okay wlh nasaba but is not okay ya shafeku nacigaba da zama anan more and more abubuwa will happen tayaya zan kalleku? How can I look at you all bayan nasan I am the reason for everything ? Ya Mustapa yakusan kuka forget some maganganun Asmeey akwai shirme da yarinta but now datakema Abba addressing abun he understood where the girl is coming from she s feeling extremely guilty because of Mamie, bama ta kanta da ciwonta takeba ta Mamie take and she feels barinta nan will make everything okay koba komi tanada certainty cewa Mom bazata kara zuwa ba so kowa will be safe. Kanta Baba yashafa yace stop blaming kanki for mistake na mahaifiyarki! Abinda yasami Mamie Allah yariga ya kaddara hakan zai faru and it s okay komi yawuce, koda wasa
Chapter 72 · 0% Book details