← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 140

Sashe 5

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

sonshi haka karasowa cikin dakin Ya Abdallah yayi yace ai ba Areef ba harsu Akram da Abdool dukansu haka sukeson Hamad, Areef oya come Uncle Hamadi is sick today makema Babansa kafada yaron yayi, Hameed ya ballama Areef harara aiko ya tsala ihu yana shiga jikin Hamad garin haka ya takemai ciwo wani kalan runtse idanu da karfin gaske Hamad yayi dayasa Hameed da sauri yadaga Areef yana karbansa, Abdallah yace Subhanallahi Hamadi, sannu, Hamadi Gwaggo tace shikenan Areef yatakemai wajen aiki duba kagani ko wajen na jini Abdullahi jin haka asauri Hamadi ya daura hannunshi awajen murya chan kasa dake fita da kyar yace m fine bottle water Abdallah yadauka yabashi amsa yayi yakai bakinshi yasha kadan duk sukai shiru suna kallonshi barinma Gwaggo, akufule da karaman murya yace kudena kallona mundena Gwaggo tace amsa da sauri, Hameed yatashi yana sauke Areef yawuce bayi, yace s time for magrib Gwaggo tace Abdullahi kaga nima kamani ka kaini kasa kamata yayi suka fice, Hameed daya fito yajira Hamad shima yadauro alwala suka fito suka wuce masallaci. Suna magrib suka dawo gida da sallama suka shigo falon, Abba suka gani zaune a falo dayake kokarin cin tuwonsa na dare, duk yayyinsu na falon, Hameed yawuce dinning yazauna tareda Faisal suna danna waya, sai Ya Mustapa zaune wajen Abba tareda Abdallah sai Mamie dake zaune a gefensu, karasowa ciki yayi dukansu suka kalleshi harda Abba daya dakatar da abincin dayake ci ya tsareshi da idanu irin kallon da uba kema dansa na nazarin yanayinsa din nan da kula, sauke kansa kasa Hamad yayi yakaraso har wajen yadan duka cikin muryanshi mai cikeda natsuwa yace sannu da zuwa Abba anatse Abba na lurada shi yace jikin yahanaka zama karatun dakukeyi a masallaci bayan magrib ne? Gently ya gyadama Abba kai batare dayayi magana ba, Abba yadan jinjina kai yace Maman Doctor yaci abinci kuwa? Anatse Mamie tace kowa yaci abinci banda shi kallonshi Abba yayi babu wasa kan fuskanshi yace zonan kaci abinci, Doctor bani maganin dazaisha na dare ba musu yataho yazauna gaban Abba kanshi akasa Faisal da Hameed suka kalleshi, Hamad yadan dago kanshi yakalli Ya Mustapa daya kawo maganinshi Ya Mustapa yamai wani kallo yace eat my friend maida kanshi kasa yayi Abba yabashi spoon dayakecin tuwon dashi ya karba ahankali shi Abba yasa hannu yace oya bismillah ci zakasha magani ahankali yafara ci Mamie na kallonshi yaci kusan 5spoons ya ijiye spoon din ahankali, Abba yace ka koshi? Gyadamai kai yayi Abba ya wanke nashi hannun tsaf yadauki ruwa yasha ya ijiye cup hakan yasa ahankali Hamad ya mika hannu zai dauki plates din da Abba yagama cin abinci dasu yakai kitchen Abba yace barshi bakada lafiya sai kawai Abdallah yatashi ya dauka dan yaran sunada tarbiya da kyau, yana dauka Hameed yazo da sauri ya karba yawuce kitchen, Abba ya tsare Hamad din da idanu da kansa ke kasa anatse yace meke maka ciwo yanzu eh Hussain? Kanshi na sunne akasa yace bakomi Abba naji sauki Abba yakalli Ya Mustapa bawasa kan muryansa yace meke damunsa likita ance kaduba sa dazu? Tell me menene matsalan? Ahankali Ya Mustapa yace Abba he got infection, rashes sun fito wajen stitches dinsa, I think maybe from ruwan wanka or sabulu or it could be anything, nayi dressing wajen dazu I will still do it yanzu sai yasha maganin Abba ya maida dubanshi ga Hamad da kansa ke kasa, cikin murya mai tsauri yace bakaga kuraje a wajen ba da bazaka fada ba eh Hamadi? Bazaka iya kiran Yayanka ka gayamai ba ko Mamie ko ni? Kana kallon ciwo jikinka kaki magana kai yaro ne wai? Inda wajen ya rube fa? Halaka kanka kakeso kayi? Bazaka dena abubuwan nan ba ko mutuwa kakeso kayi kahuta mesa kake haka ne ? Murya chan kasa kanshi akasa yace kayakuri Abba dan ijiyan zuciya Abba ya sauke yace tashi muje Doctor yamaka dressing din aka gama saikasha maganin, tashi ahankali yatashi ba musu bai kalli kowa na dakin ba yawuce stairs Mustapa yawuce yadauki jakar dake kan kujera daya ijiye yawuce sama Abba yabisu bayan ya dauki ledan magungunan. Yana shiga dakinsu kwanciya yayi akan gadonshi ahankali daidai Doctor na shigowa dakin yazo wajen gadon yana kallonshi yace how are you? Ahankali yace Yaya key the door pls wani kallo Dr yamai sannan yabude jakan yashiga ciro hand gloves nashi daidai Abba na shigowa dakin da sallama. Assalamu Alaykum Hamad ya sauke kanshi kasa kaman yayi disappearing yakeji, ahankali Abba yazo wajen gadon ya tsaya yana kallon Hamad din dayaki kallonsa yayi folding hannuwansa a kirji, Mustapa na hada komi sannan yazo gadon yakai hannunshi zai dage riganshi Hamad yadan rikemai hannu sabida Abba, Abba dake kallonsu yace wai mehaka Hamad sakin hannun Ya Mustapa yayi ya runtse idanu kawai, Dr yadan dage t-shirt nashi sama zaija wandonsa kasa kadan Hamad yarike hannunshi yadan kalli Abba daya haderai yace sakenmai hannu yayi aikinshi kadade bakaji kunya ba shirmen banza da wofi, kunyan ai shi yasaka a wannan condition, da tunda kaga abin kabi Yayan naka asibiti yabaka magana da tuni anyi an wuce wajen, cikamai hannu nace sakin hannunshi yayi ahankali, Ya Mustapa yaja wandonshi kasa maranshi yafito har zuwa wajen walls nashi ga hair kadan akwance ana gani ya runtse idanunshi sosai kunya kaman zaiyi ihu, Abba dayaga ciwon cikin bacin rai yace look at wat he did to kanshi bakasan kunya na halaka mutum ba, kuraje na fitowa haka ajikinka ka kasa fadama kowa alhalin kanada Yaya likita, ga sauran yan uwanka, ga mahaifiyar ka, gani duka, wannan wani irin abune wandonka za a cire gabaki daya dakake irin halin nan kaniyanka da abinda kake boyewa daidai Ya Mustapa yafara goge ciwo mugun ijiyan zuciya ya sauke dayasa Abba yayi shiru da fadan dayakeyi ganin abin namai ciwo sosai yadena fadan yahakura, Doctor ahankali yace sorry daidai lokacin aka bude dakin duk yanda yakejin zafi saida yakai hannu yaja wandonshi zai rufe Abba yace wai mehaka Hussaini eh ? Abdallah ne yashigo dakin sai Faisal biyedashi tareda Hameed suka maida kofan suka rufe, cikeda masifa Abba yace cigaba da aikinka kaji sun ganshi din ba yan uwansa bane da kyar cikin karfin hali yace sufita! I want my privacy dan murmushi Ya Mustapa yayi kana ganin Hamadi haka kaman ka samai y ata baisan yanda ake ta unawa ba silent rigimamme ne wlh, Abba da ranshi yagama baci yaci kaci me garinku da privacy, babu inda zasu hukuncin ka kenan, next time wani abu yakara samunka kaki fadi haka duk zamu taru akanka idan kuma bakason haka kabi yayanka asibiti kuyi abunku ku biyu sai kawai Abba ya zauna abakin gadon yana karbe hannunshi daga wandon yarike yace bude ka cigaba Mustapa ahankali Ya Mustapa yaja wandonshi da boxer nashi kasa but this time sai baija kasa sosai ba ganin yanada kunya and yan uwan shi are there, dudda Abba ya lura da abinda Mustapa yayi sai baice komiba hasalima hakan yamai dadi tunda haka Allah yayo Hamad da shegen kunya, cigaba Mustapa yayi kowa tsaye daga yanda Hamad keyi da kafa kasan da zafi Hameed yayi wani iri da fuska idanunshi sukai jaaa, yana kan gyara stitches din sai kawai ga hawaye sun fito daga idanunshi na azaba dasauri Hameed yajuya yafita daga dakin idanunshi sunyi ja, hannu Abba yasa yakai yasharemai fuskanshi, saikuma ya sassauta murya cikeda so yace ya isa kadaure Mustapa ka kusa gamawa ko ? Gyadama Abba kai yayi yana karasa dressing din su Abdallah na kallo, Faisal ma yakasa daurewa yajuya kawai yafice, Abba yakara sharemai hawaye sannan aka gama idanunshi sunyi jaaa, Mustapa yamai allura aka bashi magani yasha Abba na zaune dashi ahaka yace sannu kadena rufe wajen da wando dan Allah Hamad ciwon ya warke, dagakai sai yan uwanka agidan nan kumama duk aiki suke zuwa kai kadai ke wuni so kafinga bari yanashan iska gyadama Abba kai yayi Abdallah yace sannu Hamadi gyadamai kai yayi duk suna tareda shi ahaka bacci yayi awon gaba da shi sabida alluran Abba yace yatashi yayi isha Mustapha yace kada kadamu Abba nan da 3 days ya warke gyadamai kai Abba yayi yace kuwuce kuma kutafi gida bargo Ya Mustapa yasa ya rufamai sannan suka kashe wuta suka fice. MOTHER OR CURSE?
Chapter 5 · 0% Book details