Sashe 93
Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
driver yakaisa wani delivery company yatura kayan Nigeria kano to Hameed danya karba yakaimata yawuce yakoma gida. Yau Asmeey tadanji sauki Alhamdulilllah, saidai tayi zuru zuru ta rame, everyone is taking care of her agidan nan, ganin Munir kuma make her extremely strong at least ba ita kadaine karama a gidan ba, tana zaune a dinning itada Munir suna gyarama Mamie wake yana bata labari Mamie kuma na kitchen tareda mai aiki waya Asmeey dake wajen yahau ringing Snapchat call dan Munir yamata komi, dasauri ta kalli wayan dan Ya Hamad kadai ke kiranta kafin tamayi wani abu Munir yace Oga ya kira iyyeee see blushing dasauri ta dauki wayan tana hararansa tawuce dakin Gwaggo tabude kofa tamaida tarufe tadauki wayan takai kunne da yar karaman murya tace hello EPISODE 7 Dan ijiyan zuciya Hamad ya sauke jin muryanta tun rannan nan sai yau yake kiranta, cikin daddaddiyar murya yace my baby gyadamai kai tayi ashagwabe tace ina kwana ahankali yace lpy lau, how are you? Murya chan kasa tace fine tai shiru chan tace Ya aiki? Ahankali yace Alhamdulillah! Kinci abinci? Gyadamai kai tayi tace eh kaifa? Ahankali yace nima naci shiru suka sakeyi, murya chan kasa Asmeey tace inaso naje nai kitso Yaaya dan shiruu yayi chan yace okay i will asked Ya Hameed yakaiki saloon on Saturday, yace yanaso yakaiki wajen Zee, do you want to go? Gyadamai kai tayi tace anatse yace tom kije na yarda ahankali tace Ya Faisal ya karbi passport dina dazu da safe gyadamata kai yayi yace okay murya chan kasa yace i miss you Asmeey sorry ban kiraki jiya ba hawaye taji yazo mata da sauri tashare tai shiru batace komiba, murya chan kasa yace an biyani jiya wani murmushi tayi sosai tace congratulations Yaaya Allah sa albarka murmushi yamata yace Ameen write everything kikeso and send to me okay ? Gyadamai kai tayi ahankali tace bayason yagayamata she s going for Umara, or car or her laptop is suprise maybe gifts din suyi cheering nata up and lift her mood, ahankali yace I have to go now, saina kira anjima take care ko ? Ya Hamad baida yawan magana idan yakira tanaso suyita hira kaman karya kashe but Ya Hamad bai iyaba, highest 2min-3min yagama magana, bayan hannu takai tashare fuskanta tace tom bye ta katse wayan saikuma tafashe da kuka kaman taita ihu she s missing him sosai but it seems shi baya missing nata ta aikinsa yake. Mom takoma Kano but as usual bata kula kowa ta lura Munir baya gudan kuma tasan sunyi hutun school girman kai yahanata ta nemesa kota kirasa dudda taga calls nasa kwanakin baya datana Kano but bata dagaba yau tanaso taje gidan Hajiya Ramatu da Yamma ta nemi Fawaz cus fadansu is turning into another thing damuwa yamata yawa sai rama take ga BP dayaki komawa yadawo daidai tana zaune adaki akai knocking tai shiru Gambo kadai ke shigowa side dinta gyaramata itakuma sallama take bude kofan akayi Baba ne yana sanye da faran shadda yaci Babban kaya ya tsare Mom da idanu dayaga ta ramemai a idanu she looks sick ma has been sick all this while saisa bata gida, dudda kalan laifuffukan datamai saiyaji tabasa tausayi. Dudda ta karbe gidan the fact that duk haukanta batace subar gidanba shows da ragowan Imani a ranta, maida kofan yayi yarufe yashigo falon Mom dataga Baba yamata wani kyau tadauke kai daga kallonsa batare data gaidasa ba tana tuna marin daya mata da aurar da Asmeey dayayi without gayamata, zama Baba yayi kujeran dake facing nata yace ina kwana Salima? Shiru Mamie tayi kaman bazata amsaba tadaure tace Ina kwana Baban Aya Dan murmushi kadan yayi yace lafiya kalau dafatan kin tashi lpy gyadamai kai tayi tana kallon gefe duk sukai shiru sai chan Baba yayi dan guaran murya yace tunda kinfi karfi kizo kibani hakuri nina biyoki inaso mu ijiye fadan nan na maidaki yanzu dakinki dudda kina ciki but nadai maida aurenmu dan boyayyen ijiyan zuciya Mom tasauke dan tana son aurenta amman azahiri tace bayan kagama cimin mutunci, ka mareni a bainar jama a, ka aurar da diyata batare daka sanar dani ba Mom tashiga kada kafa, Baba yayi shiruuu yana binta da kallo shi tausayima take basa aure Rahama ne wlh dukko kudinta duktai wani iri cikeda tausasa murya yace kinfi kowa sanin dalilin dayasa na aurar da Asma u, ba gardama nazo muyi ba face sulhu amman idan kina ganin namiki ba daidai ba bari na miki tambaya daya kacal inaso kibani amsanta Mom ta kallesa ahankali Baba yace mesa kika tsani Asma u diyar da kika haifa da cikinki? Wani iri Mom taji taso kartai magana amman zuciya ya debeta tace sabida Asmeey bad luck ce! Tun cikinta nadena ganin daidai arayuwana ba, na haihota the only dalili dakesa kai fada dani is Asmeey kawowa har yau sabida Asmeey ka sakeni nika saka sabida ita! Saisa na tsaneta Baba yakalli fuskanta yana ganin tsana sosai he guess there s nothing he can do only time can heal this hatred she has for that poor girl, yunkurawa Baba yayi zai bitterly Mom tace kadauki y ata ka aurama wani jakin dabban yaro mai matsalan kwakwalwa uwa uba jobless boy mara aikinyi yasamin yarinya a daki daya wanda ko nan dakin dasuke na gidan nan yafi wanda suka sata girma ciki sai hudu, look at room nasu mana yana daukan king size bed guda biyu nata da Ramla damasu Yusra but look at bukka room da aka sata akano itada miji na zama iyaye suna ciyarda su. Murmushi Baba yayi yadan cije lips yace Salima kenan ba ama Allah isgili sannan ba ama bawa gori, Allah daya baki can give Hamad much more anjiman nan, and been quiet and shy doesn t mean you have mental issue Baba yadan fuzar da iska yace tune into ko CNN kowani international news channel today or watch Microsoft broadcast today na new AI din dasuke ya talla this days I have a suprise for you, 2PM anjima don t forget Baba na maganan yabude kofa yafice. Mom tabisa dawani kallo ganin sabida tayi maganan yarsa ma komar da itan dayace zaiyi baimayi maganan ba yafice kawai zuciyanta yafara tafarfasa saitaji kanta na sarawa dafa kan tayi ta gyara zamanta tahayo da kafafunta kujera tahau tana kwanciya she s really sick, mesa Fawaz ke mata haka? He s the only cure to her rashin lpy wayanta ta daga tai dialing number sa bayama shiga at all kaman yayi blocking dinta ko baya Nigeria ne? Ijiyan zuciya ta shiga saukewa me zafi idanunta na fito da hawaye masu dumi ta gefe batajin dadin rayuwanta karfin haline kawai dawata ce da tuni ta mutu cus a tsaitsaye a tsaitsaye ciwo take tana wajen ahaka bacci yayi awon gaba da ita wuraren 2 na rana tabude idanunta. Wayanta ta dauka tana dialing number Fawaz again but baya shiga ijiye wayan tayi ta shiga sauke kafafunta ta yunkura zata tashi saitaji kanta ya sara komawa tayi ta zauna tamika hannunta tadauki bottle water dake wajen tabude takai bakinta ta kurba maganan Baba na fado mata dazu yanada suprise for her PM menene menene ma yace? CNN? Remote na tv ta dake nan kan table tasa hannu tadauka tana ijiye bottle water ta danna power button tv ya kunnu, TV ya kunnu tadauki remote na DsTV decoder ta chanza zuwa CNN daidai ana program din CNN da ga turawa dayawa ciki harda bill gates, Elon musk, Ambani, da other top world richest people hall din an cika makil, Mom tadan yatsine fuska tace me mutumin nan yasa nake kallo ? Daidai mai hosting wata British woman tace Ladies and gentlemen! Let s welcome the star of night! Microsoft Talent Hunt Winner who design, create and invent the SOFT AI! Mr Hussein Hamad Abubakar! Aka fara wani irin tafi camera na hasko Hamad dake zaune kan wani kujera sanye da black suit da tie awuyansa yasaka wani earplug a kunnensa guda daya wanda kaman a wajen aka ba a sabida speech dazai bayar, yayi bala in kyau yawani mike tsaye! Mikewa tsaye Mom tayi tana zaro idanu tana wani kama kirjinta tana kallon Hamad na walking to the stage while presenter na bada short biography na rayuwan Hamad wani soft low plane music na tashi. Mr Hamad is Nigerian born and brought up in Kano the northern part of Nigeria! He s 33yrs has a bachelor degree in computer science engineering and MSc in software engineering and Inovation, he s into Tech, acquired different certifications from the likes of Azure, AWS, Oracle, CSM, Sensor flow developer, Artificial Intelligence Practitioner, etc.. Daidai Hamad na karasa hayowa stage din looking handsome, charming and damn charismatic, gashinsa da coils nasa na kyalli ya tsaya elegantly ya kallo hall din, tamikamai hannu, karba yayi gently suka gaisa ta matsamata gefe ana tafi ba kakkautawa . Dawani irin sauri Mom ta dauki wayanta har duhu duhu take gani ganin kaman karyane abinda tv ke nuna mata tashiga Google tay typing Microsoft talent hunt winner kawai taga hoton Hamad da kudin dayaci kimanin 500 million dollars kudin Nigeria 777 billion naira kawai waya ya kufce daga hannun Mom kanta na juyawa tana ganin duhu duhu, kirjinta nawani irin bugawa na bakin ciki da azaban hassada ta tafi luuuuuuuu ta zube kasa bata sake sanin inda kanta yake ba jini ya buga. EPISODE 7 Wuraren 1 Asmeey ta tafi sama dakinta danyin salla azahar, she s extremely missing Ya Hamad, tun shekaran jiya dasukai maganan zuwa saloon bai kara kiranta ba, she guess he s busy sabida yaune akace za ayi lunching AI din, tana zaune akan dadduman akai knocking dakinta tareda sallama jin muryan Ya Mustapa dasauri tamike tsaye bude kofa tayi tadan sauke kanta kasa akunyace tace ina yini Yaya? Gyadamata kai yayi yace ya jikin wat are you doing inside? Dadduma ta nunamai tace salla nazo nayi gyadamata kai yayi yace okay muje downstairs Hamadi app lunch is in few minutes gyadama Ya Mustapa kai tayi ahankali yawuce saita biyosa abaya tana rufe kofan, muryansu duka taji a kasa itama Mamie tabude dakin nata tafito dan itama salla tazo tayi hatta Abba yadawo