Sashe 19
Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
yajuya yakoma sama Ammi kuma tawuce tafita falon Mom yabude but bakowa ciki but yana jiyo muryan Mom daga ciki tana banbami, kai tsaye bude kofan dakin yayi dadan sauri Mom tajuyo ko kadan bata dauka yanzu Baba zai dawo ba sai chan anjima chak Baba ya tsaya yana kallon Asmeey dake zaune akasa gaban Mamanta ga uban files da manyan textbooks agabanta gadan jini daya gani gefen lips nata which yana shigowa akan idanunshi yaga tagoge da sauri but bata dago kai ta kalleshi ba, tashi Mom tayi tana sauke littafan dake kan cinyanta tace Alhaji kadawo ko kallonta baiyiba idanunshi nakan Asmeeey yace Husna dan dago kanta Asmeey tayi takalli Baba tareda kakalo murmushi asanyaye tace Baba sannu da zuwa wani irin faduwa gaban Baba yayi ganin idanun yarinyar sunyi jaa gashi kuncinta shaidan hannu dayayi ja abunka da fara lips dinta yadan kumbura Mom takalleta tace Babanki na kiranki kitashi kin zauna dasauri tace kokarin tashi tashugayi kafafunta sunyi sanyi sai Mom tashiga gaban Baba ta kareshi tana murmushi tace muje falo ta biyomu an kawomin kayan sallan dana maka muje kaga dinkin ko motsi Baba baiyiba kokarin kallon Asmeey dake kokarin tashi yake Mom tasake kareshi takai hannunta takama nashi tace muje kagani fizge hannunshi yayi yamata wani kallo yace t touch me yawuce gefenta yaje wajen Asmeey data tashi, ahankali yakai hannunshi yakama kuncinta yana kallon wajen strictly Baba yace meya sami fuskanki yayi ja haka washema Baba baki tayi tace faduwa nayi dazu Baba boyayen ijiyan zuciya Mom ta sauke, Baba yace to me kikeyi anan bakije kinyi kitso ba zo muje riketa Baba yayi yasata ajikinshi yashiga tafiya da ita ahankali sukabi ta gefen Mom suka fice dakinshi yawuce da ita kan kujeranshi ya zaunar da ita yawuce fridge dinshi yabude laban yadauko me sanyi yakawo mata yabude yabata ta amsa tana murmushi tace nagode Baba takai bakinta tadan kurba, gently Baba yasake kai hannunshi gefen kuncinta anatse yace tell me the truth Mamanki ne tadakeki haka ? Dasauri ta girgiza kai tace Baba faduwa nayi dazu Mom bata dakeni ba shiru Baba yayi yana kallonta ganin haka yasa tashiga shan madaran gabanta na faduwa, saida ta shanye Baba yace tashi kije waje wajen kitso da lalle kema amiki tashi tayi tace tawuce tayi wajen kofa tafice yayi shiru sannan yadauki wayanshi yasa a kunne kai tsaye yace meet me in my room a wani jimaba Mom tashigo sai kamshi take dubawa Baba yabita da kallo ranshi abace yace Salima nina sa aka kira masu lalli har gida da masu kitso sabida ama yarana mata akan wani dalili zaki ijiye Husna adakin ki bazaki barta taje tayi ba Mom na kallonshi tace au haka tace maka ? Ran Baba abace yace babu abinda Husna ta gayamin rannan nan I told you kibimin yara ahankali wai shi karatun nan dole ne? Law school zata iya zuwa aduk sanda taga dama akanme zaki tasamin y a agaba? This is the last time dazan miki wannan maganan ba dole bane Husna saita gajeki ba! Ni dan kasuwa ne mesa bance Munir dole sai yazama dan kasuwa kaman ni ba? Kibar yara suyu abinda sukeso, the next time zaki takurama yar nan wlh saina dauki mummunan matankin da saiya baki mamaki! Imagine yau baki zanyi mahaifiyata da yan uwana suna hanya ke e babba agidan nan amman bata ayyuka da abincin da zasuci kike ba, I will not say anything ku cigaba da halinki gida biyu maganin gobara kada ki komi ko yaya kikeso kiyi amman yarana kidena takura musu na gaya miki Mom na kallonshi tace shine kakemin ihu Wacece ke da baza amiki ihu ba yana maganan yawuce ya shiga bedroom dinshi ya barta nan tsaye. UWA KO UKUBA?