← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 140

Sashe 94

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga kasuwa duka suka wuce kasa harda Gwaggo dasu Munir, wajen Munir Asmeey taje ta zauna kusada shi tana kallon TV an fara program din kawai gabanta sai faduwa yake, Ya Hameed yatashi yana sassauke labulen window yakashe wuta, falon yayi duhu tv kawai ke haske duk kallon TV ake Gwaggo tace suwa Allah su nunamin Hamadi na nagansa Faisal yace an kusa Gwaggo, yanzu wannan dake magana shine mai Microsoft din Yana gama magana yakoma sit dints dake kusa da Billgates daidai mai hosting wata British woman dake sanye da suit mai kyau tace Ladies and gentlemen! Let s welcome the star of night! Microsoft Talent Hunt Winner who design, create and invent the SOFT AI! Mr Hussein Hamad Abubakar! Bugawa kirjin Asmeey yashiga yi wani chills na sanyi na ratsata tundaga kan yatsun kafafunta har brain nata, aka fara wani irin tafi camera na hasko Hamad dake zaune kan wani kujera sanye da black suit da tie awuyansa yasaka wani earplug a kunnensa guda daya wanda kaman a wajen aka basa sabida speech dazai bayar, yayi bala in kyau yawani mike tsaye! Asmeey ta tsaresa da idanu kaman yau tafara ganinsa Ya Allah! Tanason mijinta! Bata tabajin tanason abu aduniya kaman Ya Hamadi ba, see tanason Ya Hamad kaman taita ihu tana screaming she loves him, butterflies taji suna tafiya acikinta bana wasaba takai hannunta ta daura saman cikin kozai rage motsi, Gwaggo tace ku kalli jikana wlh uwa bature baida banbanci dashi, Hamadi ne haka? Yazama bature Murmushi Mamie tayi sosai ganin danta looking damn handsome hawaye na zuwan mata idanu Abba yakama hannunta yarike yana murzawa yana kada kafafu proud parent kenan! Anatse Ya Mustapa ke kallonsa shi kadai yasan yanda yake alfahari da kaninsa, Hameed yaciro wayansa yana daukan hoto daga tv yace status status lets pepper the haters Faisal yace look at my Hamadi! Looking classy and rich, wlh ya chanza gabaki daya Ya Abdullahi yace jibi yanda bill gate ke kallon Hamadi karya kwacema Microsoft shi ko numfashi Asmeey bata iyayi da kyau sabida yanda take kallon Hamadi daya mike walking to the stage calmly babu wani gara gara ko garaje a tafiyan, one step at a time yake while presenter na bada short biography na rayuwan Hamad wani soft low plane music na tashi. Mr Hamad is Nigerian born and brought up in Kano, the northern part of Nigeria! He s 33yrs old has a bachelor degree in computer science engineering and MSc in software engineering and Inovation, he s into Tech, acquired different certifications from the likes of Azure, AWS, Oracle, CSM, Sensor flow developer, Artificial Intelligence Practitioner, etc... Daidai Hamad na karasa hayowa stage din looking handsome, poised, charming and damn charismatic, gashinsa da coils nasa na kyalli ya tsaya elegantly ya kallo hall din, tamikamai hannu, karba yayi gently suka gaisa ta matsamata gefe ana tafi ba kakkautawa saida raf n ya tsagaita yace good day ladies and gentlemen zokaji tafi sabida yanda voice nasa yayi a mic din, turencinsa is very sweet, rich and simple, bawani kakalen banza da wofi, speech zai fara badawa dangane da winning dayayi da dedication sai presentation na software anatse yace I want to thank God Almighty for making my dreams come true, I wanna Microsoft team for looking beyond where I come from, rather they look at my potentials, my skills, my dedication and hardwork .. I want to dedicate this win to my family! Yadanyi shiru ana tafi yace My Dad Abba did everything for me if you are watching this thank you Abba! Akahau tafi saida aka tsagaita Hamad yace you know I have a second Dad Yadanyi shiru kadan yana kallon audience din yace he happens to be my brother Ya Mustapa! He s my everything! Yafadi asanyaye kafin ahankali yadan fuzar da iska yace without his support I wouldn t have been here today yayi shiru cus baiso yayi kuka akahau tafi bana wasaba to lift his spirit, Ya Mustapa yayi shiru yana kallon Hamadi daga tv idanunsa nada ciko da kwalla kadan, haka kowama na dakin, ahankali yace My Mom! Mamie is my comfort zone, my peace, my encouragement and my strength! I have the world best mother yafadi ahankali dayasa Mamie tashare hawaye dasauri, anatse yace to the rest of my family, my nosy brothers, my twin they all contributed and made me who I m today I wish everyone have brothers like mine yadanyi murmushi kadan, sai akuma ahankali cikeda wani irin natsuwa ta daban yana kallon mic dake gabansa daban daban yace and my wife! Yayi shiru hall akai tsit jin ya ambato mata yace s is my sunshine that made my life brighter and colorful! And she s my lucky charm, my better half! su Hameed suka kalli Asmeey sukace awwwwwwwnnnnn Asmeeeyyyyyyy boye fuska Asmeey tayi akunyace zuciyanta na mata kaman an watsa wani sugar mai sanyi tana wani kara crushing on Hamad tanajin mahaukacin sonsa aranta hawaye na fitomata daga idanu, anatse Hamad yace this win is not for me alone, is for my family! For my state! For my country Nigeria and for African in whole! Aka fara tafi sannan sai ya shiga bayanin soft AI yana nuna musu a screen da yanda yake aiki, ba yan hall din kadaiba harsu dasuke kallo daga tv knows Hamad was made for this! He s the definition of a talented genius, this is his thing he killed it, he ate and left no crumble, gaban Asmeey sai bugawa yake yanda ake nuno yan hall din na kallonsa, abubuwa na mata yawo a zuciya Ya Hamadi zai sota again? Idan wata ta kwacesa fa? Look at yanda maza ke sonsa ballema mata, kowafa yasan mijinta kenan ko? Tai shiru tana tunani daban daban gabanta na faduwa tsoro na shiganta, deep deep down she prefers Hamad dinta dasuke tare koda yaushe adaki daga ita sai shi, karya shagala yaga matan dasuka fita komi ya manta da ita, har aka gama ta tashi ta sulale sama ganin su Ya Hameed na tsokananta, yace gobe yace na kaiki saloon daganan zamuje gidansu Zee Munir yace Yaya nima zani saina dawo dakai Hameed yace okay tom EPISODE 7 Saida aka gama program din tsaf a falo Baba dake kallo da Ammi da Ramla dan sauran yaran na school yayi murmushi yataso dan yazo yaga fuskan Mom, bude kofan yayi da sallama ganin Mom sandare kan kujera tarike kirjinta bata numfashi yasa yayi wajenta da gudu yace Salimah! Salimah! Ina Mom bata motsi kokarin dagata yayi yakasa ya kwalama Ammi kira sai gata yace tayani mu kaita mota zuwa tayi tace Subhanallahi meya sameta ? Baba yace I don t know kaita mota sukayi Ramla takawo hijabi da slippers na Mom, Baba yaja motan da kansa suna kaiwa asibiti aka karbi Mom Baba yasami waje yazauna yana dafa kansa saikuma yaciro wayansa yakira Yayanta ya sanar dashi ya katse wayan yayi shiru Chan saiga Dr yace come with me binsa Baba yayi, suna shiga Dr yace ya akayi BP Madam yayi raising haka? And tanada Cardiomegally which happens due to hypertension Baba yace mekenan likita? Dr yace zuciyanta ya kumbura sabida hawan jini, yanzu I will put her on heart drugs dazata sha for a month tadawo, dudda haka I will still refer her to see a cardiologist, please please Madam tai avoiding damuwa dawani tashin hankali da sauransu, zuciya muke magana anan is dangerous is not something to be taken likely Baba yayi shiruuu yau daya ganta tabbas yaga ta rame sosai me Salima keso ne? Kin tsani yarinyar sannan kuma an aurar da ita an cireta daga gabanki kince a a baki yardaba, wani kalan concoction kalan damuwa ne wannan da fitina da bala i dahar tana samin kumburin zuciya sabida damuwan? Yadawo mata da Asmeey and watch her kill yarinyar dabata mata komi ba? Shine abinda zai kori BP da ciwon zuciyan ko me? This life is funny fa, like wani kalan irony ne wannan, baki sami daman cin zali ba damuwan hakan kuma haryakai gayasa miki hawan jini da kumburin zuciya? Ikon Allah! Yadai lallaba yace to ya take yanzu? Dr yace ve given her all the necessary help we will wait ta tashi mugani Baba yasauke ijiyan zuciya yace tom nagode yatashi yafito yazauna awajen yayi shiru yana kallon gaban dakin datake ciki saiga Alhaji Mahmoud yana zuwa suka gaisa da Baba yace tana ina ? Baba ya nuna dakin yace a ce nashigo ba tukunna ganin yanda Baba ke magana ba karfi a murya da yasa yazauna gefensa yace meke faruwa? Shiru Baba yayi saichan yace enlargement of the heart sabida hawan jini, damuwa yamata yawa Baba yadanyi shiru dan son Mom Allah yasani yanayi, ahankali yace Alhaji narasa yanda zanyi da lamarin Salima bantaba ganin mata mai bakin naci da kwallafa rai akan abu kaman Salima ba, yarinyar nan ta tsaneta bata kaunar ganin Asma u na aurar da ita nacireta agabanta shima ban huta ba, tace ba a kyauta mata ba ita bata yardaba saita dauko diyarta Baba yadanyi shiru yace nakiraka ai na sanar dakai abinda taje tayi a kano takusan kashema yaran nan mahaifiyarsu, Asama u kuma ta barbadeta da burkono, wani kalan maita ne wannan? Sabida burinki bai cika ba kashe kanki zakiyi hawan jini haryakai ga zuciya na kumbura yazanyi Alhaji Cikeda bacinrai Alhaji Mahmoud yace wace kalan tambaya ne wannan yazakayi? Yako zakayi? Idan mutuwa ta zaba ai shikenan Allah ya jikanta yarinyar zaka dauko kabata takashe tunda ita batada lafiya akai? Da ace haka iyayenmu suka mana danace okay gado halin mahaifiyarmu tayi amman wlh mun taso cikin kauna, iyayenmu na sonmu kafin Allah ya dauki ransu, mahaifiyarmu da mahaifinmu basuda zafin Salima bansan a ina tadauko nata ba bansani ba, tun wuri gwara ta sassautama zuciyanta tsana da ki data saka aciki ko ta mutu abanza a wofi Baba yayi shiru duk suna wajen akace zasu iya shiga suka shiga Mom ta farfado bata da karfi amann tana ganin Baba da Yaya ta hade fuska tamau duk suka kalleta suna mamakin Salima. Takalli Baba kur kaman wacce ba yanzu ta farfado ba zuciyanta na radadi idan ta tuna kudin da Hamad yayi tace ina
Chapter 94 · 0% Book details