Sashe 30
Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
tace hannu Mom ta daga mata hakan yasa ta hadiye magananan, Mom tace ni uwarki dana dauki cikinki wata tara na raineki kawowa yau zaki kalla ki zubar Asma u! Ina kwana, good morning bai hadani dake jiya ba rather you went and join my enemies Mom tayi wani dariya tana karkada kafa tana kallon Asmeey tasake dukan kirji da karfin gaske tace Asam u dangin Babanki da kikasan basa sona da akwai yanda zasuyi tundaga kan makiran tsohuwar dayake kira da uwarsa da yayinsa Abubakar da shi dayan Kawu da munafukar matarsa maman doctor da tuni sun fitar da ni, mutum daya ke sona kap dangin su itace Maman su Nana amman shine kikaje cikinsu aka rikeki ana kula da ke ana baki magani an saki cikinsu ana gulma dake, opportunity da basu samu jikin yarana na amana Aya da Aysha shine yanzu ke sun samu ajikinki, ubanki ma ya jonasu yau rana na biyu bai kulani ba baikuma shigo dakina ba hmmmm tasake murmushi tana kada kafafu tace wallahi wallahi kome zakuyi saidai kuyi kinga gidan nan zama daram banga uban daya isa ya fitar dani ba wlh nasha karfinku gabaki daya ai ba tun yau akeso a kadani ba tun kafin ahaifeki to nasha karfinku kinganni nan nan gani nan bari, dake da su kuma karo wasu su jona jam iyyan ku baku isa kuja dani ba, na taka inda kaf dinsu babu wanda ya take ke kin sani! Kinsan the kind of people I deal with, me suke da shi? Shi Abubakar din dayake fama da kasuwancinsa na kayan hatsi dayake surviving da kyar jari yakare? Koshi dansa Mustapa da ke aikin likita surgeon? Nawane salary nashi? Cus naga shine ai abin alfaharinsu agidan abin tunkahonsu kenan, koko shi Abdullahi dayake aiki a wani NGO yana fama ana turasu kauyuka koyama yara ABCD? Ko shi Faisal dake kirari yazama lawyer yana fama har yau baitaba cin case daya ba, ko shi Hameed dake fama da bank dinsa da ake biyansa baikai 150k salary ba, koko shi Hamad din da har yau ba aiki? Sis baida shi sai abinda Yayinsa da ubansa suka tsammai? Yana saida data online tama Asmeey dake girgiza kai tana goge hawaye da hijabinta wani kallo, Mom tace shi Kawun naki ma ba a sashi a lissafi saisa nakeba matarsa kudi nasaka su Aya suna matarsa zakka cus she s loyal to me to tell me saisa takejin dadi, me zasu nunamin? Me sukeda shi? Waye su kap dinsu? Ke I handle case na vise president I won! Da na yarda na karbi appointment na Abuja da tuni Allah kadai yasan mena zaba but bansan Babanki na nan ni ina wani waje, bar ganina haka Babanki dakikaga ina zama dashi sabida mijinane danakeso amman ubanki baida kudin dazai nunamin Asmeey, inada mazan dasuka fisa, so fara tundaga kansa da dangin nasa Billahillazi ni Salima nafi karfinsu, nasha karfinsu, kuma babu abinda wani shege ko shegiya ya isa yamin ke kin sani! Mom tayi maganan tana dukan kujeran datake kai a zaune saida yayi kara Asmeey ta manne da kujera tana kuka Mom namata wani kallo tace the only reason dayasa bazanci ubanki da durun uwar ubanki ba sabida mijinki zaizo yau da mamarsa ne amman wlh wlh saina gwada miki ke karaman yar iska ce Asama u, zan kuma nunamiki ke yar kiyashi ce agaban Giwa, zan takeki na wuce batare danasan nayi ba, Shegiya wulakantacciya, kaskantacciya, Allah yahanaki farin ciki arayuwanki! Dasauri Asmeey ta kalleta, Mom tace Wlh bazaki tabajin farin ciki ba har abada yar bura uba sainaci ubanki wlh jaka kawai karuwa! ?Wani irin kuka Asmeey tafashe dashi tana kallon Mom duka zagin nan da addu in nan babu wanda Mom bata saba mata ba, she keeps saying this prayers, goge idanunta tayi gwanin ban tausayi hawaye still na zubowa tace dan Allah kiyakuri Momy kiyafe mini kinji Mom haukacewa Mom tayi tadauki journal na gefenta tawani wurgo mata amman bai sameta ba Mom ta zabura ta mike tana dunkulle hannu tace ke zan kasheki fa na huta Asmeey na tsaneki, na ganki jinake kaman na halakaki, karatu yau kwana nawa bakiyi ba? Kuma bazance kiyi ba ki koma wajen yan uwan ubanki zaki sha mamakin abinda zan miki wuce kifita ki shirya karfe daya mijinki zaizo gidahuma kawai jaka kasa tashi tayi sabida yanda Mom take a tsaye rarrafe tayi tawuce saida takai wajen kofa ta iya mikewa ta tashi tabude kofan tafita tana share fuskanta tawuce dakinsu Munir daya labe abayan wani kujera awajen yataso dan yaji komi cus yazo ya gaida Mom ne shima yaji magananta. UWA KO UKUBA?