Sashe 51
Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
seen wat happened dazu?" Kin magana Hamad yayi, ahankali Hameed yace "Allah baku zaman Ipy, l'm very worried about you, zo muje muyi salla" saukowa Hamad yayi suka wuce masallaci batare daya kulashi kan maganan dayayi ba yana idar da sallan yafice kafin Abba ko Hameed su tsaresa. Mamie shigowa falon tayi tace "Asiya ku kaita dakina" wucewa da Asmeey sukayi dakin Mamie, Mamie biyeda su abaya dakinsu Hamad dayake abude ta shiga babu komi adakin anyi fentin dakin fari anyi mopping floor tun ranan auren Mustapa yasa gateman yabude ma masu aiki, akai moving kayan dakinsu zuwa dakin dake kusadana Abba, yanzu chan Hameed zai koma, bai kamata Hamad da matarsa su zauna adaki next to nasu Abba ba saisa akai maintaining first room idan ka hayo saman asalin dakinsu nada, an gyara dakin, anyi fenti, anyi mopping, dakin ya bushe, murmushi kawai Mamie tayi idan tace she's not proud of yaranta she lied cus they contributed money sukai fentin nan ragowan kudin sunje sayo gado da carpet da study table and chair na Ham ad and small stuff na daki da kuma curtains masu kyau for just door and window, dakinsu ta shiga matan mai gadi da yar aikinsu ta gyara ko'ina tsaf tsaf kuma kamshin turare Asmeey suka zaunar agado Mamie tace "Masha Allah" Asiya tace "meza'a dafa Mamie" ahankali Mamie tace "kome kuka dafa, sa akawoma Asmeey akwatinta nan tayi wanka tarage kayan nan tayi amai dazu" Mamie tawuce tafita .tashiga dakin Abba dantai salla, Asmeey na wajen zaune tai lamo tanabin dakin da kallo Anty Kady matar Faisal tashigo mata da akwatunan ta duka tana bude mata tace "muje kiyi wanka" gyadamata kai Asmeey tayi tamike tawuce ta shiga bayi da kyar tacire rigan sabida hannunta tadaura towel takira Anty Kady ta tayata unhooking bra, wanka tayi tai alwala tafito bakowa adakin shiryawa tayi cikin cikin wani riganta da aka ciro mata eyptain gown na curtain mai mayafi, dadduman dayake wajen tahau ta kabbarta sall , Anty Asiya ta shigo da gashashen kaza da yoghurt da biryani rice a tray takawo mata ganin tana sallah ta juya ta fita idarwa tayi tai shiru tana kallon abincin tanajin hayaniyan maza kaman ana shishigan da kaya ga muryan mazan gidan but bataji da Hamad ba, da kyar tadauki yoghurt takai baki takasacin abincin, kirjinta bugawa yake kawai, shigowa dakin Abba yayi da kansa yakalli abincin yace "Asmeey bakici abincin ba?" Akunyace ta sunkuya kai tana rufe fuskanta, Abba yayi murmushi he might consider matan su Doctor da sauran surukai but Asmeey har ransa he took her as daughter sabida yarsa ce da gaske, yar kanninsa dake binsa so Asmeey yarsa ce bazai taba kallonta kaman yanda yake kallon sauran matan yaransa ba bazaima iyabane, Abba yace "faracin shinkafan in ga" gyadama Abba kai tayi tasa spoon tafaraci saida tayi kusan 4spoons sannan Abba yace "to bari nadan fita bazanyi nisa ba idan kin gaji Mamanki na kitchen namasan yanzun nan zatazo wajenki, kisaki jikinki kinji gidan Abban ki kike kinajina" ahankali tace "toh, Abba ina Gwaggo"? Abba yace "wannan ai kafin a iso gida ta sauka wai taje duba takwaran da aka mata tabata barka da salla but nasan zata dawo yanzun nan" gyadamai kai tayi Abba yafita, bai wani jima da fita ba Mamie tashigo shigo haka ta tasata agaba saida taci shinkafan da dan yawa sannan ta barta tafitar tadawo babu su Anty Asiya sukazo sai hira suke suna bata labarai Mamie tabasu waje, hakan dasukayi sai bai bata daman tunani ba har akai magrib sannan Mamie takarasata tai wani wankan takawo wani sabon abaya mai kyau peach color tasaka, Anty Kady tadan shafa mata hoda duk suna murmushi aka fesa mata turare sannan aka yana mata veil din abayan akai kawai Asmeey saitaga sunhau wake suna tafi Mamie na murmushi tace "muje mu kaiki dakin mijinki" kawai sai hawaye Asmeey taji akahau dariya, they look so happy all of them harda Mamie sai waka suke suna rawa da tafi suka riketa suka fito da ita Mamie tabude dakinsu dake kamshin turaren wuta an gyara dakin tsaf, gadonsu mai kyau sosai wani english sweedish bed ga wardobe mai kyau mai madubi ansa carpet akasa mai laushe ga gefen wajen study Hamad da desktop nasa akai ga chair mai juyawa, gawani shelf na books dayake dashi na books dayawa dana larabci acikinsu, dakin kaman ba dakin Ya Hamadi da Hameed ke zama ba saiya chanza, yayinsa sun kashe kudi even the bed alone looks expensive kafin ayi maganar katifa, carpet, set na duvee, curtains study desk and chair, they spend nothing less than 500k above for the room, an shimfida zanin gado mai kyau da bargo, curtains nasu yayi kyau black and white masu kauri sosai, har lightening na dakin an chanza, da kafar dama aka shigar da ita aka zaunar da ita kan gado. Kawai Asmeey is feeling emotional, hawaye kawai take sai yanzu ta yarda da gazken gaske tayi aure, yanzu dama haka aure yake? Ana zaunar da ita Mamie tace "ku kawo akwatin ta mujera mata kaya" haka suka kawo jera mata kayan aka shiga yi tasss dukansu sukaji muryan Gwaggo daga kasa. "Kuzo ku hayo dani naga dakin jikokina Hamadi da Asmeey" kwashewa da dariya akayi Asiya tafice ta hauro da Gwaggo tana zuwa dakin tace "keeee ni Madinah yaushe dakin gardawan nan yadawo haka? Kaga daki kaman sanda naje saudiya wannan dakin hotel din nan, Billahillazi wannan ma yafisa kyau" Asiya tace "bayan baki zauna anyi jere dake ba Gwaggo keme takwara" Gwaggo tace "kinga Areef nake nemawa takwaran nan ina zuwa zan bari kiga naga amaryata" Wucewa gadon Gwaggo tayi ta zauna tana duban Asmeey tace "yanzu me kikema kuka iyye? An rabaki da jaraba da wannan ukuban matan ubanme kikema kuka? Babu mai kara jibgarki ko kokkoda miki mari anan? Jibeki har kin fara haske kwana biyu bakisha mari ba, jibe matan yayyin mijinki yanda suke sonki, jibesu kaya suke jera miki a drawer, karki damu idanma biki kikeso yanzu munakai kudin auren Hameed duk sai ahada amuku taron biki lokaci daya, dena kukan kinji, kowa na sonki anan bagani ba, ga Mamie ku, ga Abba, to wah kike nema? Gida fa kika bari kikazo Gida kuma dena kukan hakanan Asama" Gwaggo tai maganan tana share mata hawaye ta rungumota Asmeey tai lamo ajikinta tana tsagaita kukan sai bayan isha'i suka gama gyara komi tsaf tsaf akasa tai salla sannan suka fice, Gwaggo ta zauna da ita aka kawo mata abinci tanaci tanama Asmeey surutu. Kowa na falo banda Mamie da Abba da suka bama yaran nasu waje sun musu sallaman saida safe, yayyin kuma Hamad suke jira yazo sukaishi daki su tafi gidajensu, Hamad kuma tunda sukai azahar da Hameed ya gudu ko la'asar baiyi a masallaci ba an nemesa an rasa lamba bata shiga, hamma Hameed yayi yana kallon agogo yace "Ya Doctor bazafa kuga Hamadi ba yagudu cus yasan duk sai an jirasa yazo ku kaisa daki ni bacci nakeji" waya Ya Mustapa yaciro yayi dialing number hoping zai samesa yanzu, luckily wayan yashiga yana gab da katsewa Hamadi ya dauka strictly Ya Mustapa yace "kana ina?" Murya chan kasa yace "masallacin bayan layinmu" Ya Mustapa yace "toh come home ina jiranka" shiru Hamad yayi bai amsaba, Ya Mustapa yace "bakaji bane"? Ahankali yace "naji" katse wayan yayi Ya Abdullah yace "zaizo ko?" Gyadamai kai Ya Mustapa yayi matan suka tashi suka wuce sama Hameed yace "kar wacce ta tambayeni kudin siyan baki ba bakin wacce zan saya" Matan sukai shewa Asiya tace "aiko bazamu bama kanninku matarsa ba" Ya Mustapa yamata wani kallo tai dariya tawuce, saida Hamad yakara bata kusan 1hr sannan yashigo gidan yakai kusan 5min tsaye gaban dakin da kyar yabude kofa ya shigo sai kuma yayi kaman bai gansuba zai wucewan sa tsabagen iskanci Ya Mustapa yace "zonan" kasa juyowa yayi su Faisal da Hameed kowa yadaura hannu a baki ya danne sabida dariya, ganin yaki motsi ya Mustapa yamike da kansa yana zuwa inda yake ya kama masa hannu suka shiga hawa bene sukai corridor yaga sun wuce dakinsu sunje dakin dake kusa dana Abba yaga Ya Mustapa yabude dakin gadajensu da komi nasu nada duk yagani aciki ga wata sabuwar dinkakiyar yadi akan gado da turaruka yace "go and shower ka shirya in this clothes nabaka 5min wih ko ranka saiya baci" yajuya yarufomai kofa yafice, kaman zai bude kasa ya shiga haka yakeji da kyar ya daure yadauki kayan yashiga bayi yayi wanka ya chanza yayi wani kyau yafito daidai Ya Mustapa da kannenshi na shigowa haba zokaga ihu sabida yanda kayan sukamai kyau. "Ango! Ango! Ango" Faisal yace "yausai kashe arna!" Tashi Hamad yayi azuciye zai wuce kofa suka wani taresa, Ya Faisal yace "tsaya kaji dalla zaka fara, akwai different holes in the place akwai na sex dana pee" dukawa Hamad yashigayi suka fashe da dariya suka kara binsa kasa suka dudduka, dasauri yamike yarasa inda zaisa kansa ya cika yayi fal, Ya Abdullahi yace "she is a small girl karka tearing nata fa Hamad please" kaman wanda zai kurma ihu juyawa yayi zai koma bathroom suka kara rikosa. "zo Hameed zai maka kiss" kawai sai hawaye sharrrr yasauko daga idanunsa yasauke kansa kasa not knowing what to do da brothers dinshi, cikeda fada Ya Mustapa yace "wai mesa kuke haka ne? Yanzu kunsashi kuka are you happy"? UWA KO UKUBA?