← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 140

Sashe 7

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace shikenan Alhaji ta shigo Baba yakalli Asmeey dake gefenshi data share fuskanta da sauri tanamai murmushi mai bala in kyau yace da idanunta awajen kaman na mutanen da wuce kishiga murmushi tayi ta shiga tana ballama kannenta harara dake kallonta barinma su Yusra. Dan saurayin dake 20yrs yana kama da ita sosai yajuyo yakallota yamata gwalo kirne fuska tayi Malam yadawo ya zauna kowa ya natsu suka cigaba da karatu. 7:00 daidai na safe aka tasosu duk suka fito dayake almost dukansu yaran suna zuwa school Asmeey ne kawai da Ramla basa zuwa su sun gama university Ramla NYSC zata yanzu ita kuma Asmeey law school duk suka wuce cikin gidan, zama all the children sukayi anan babban falo su Gambo da Ammi na bama kowa breakfast, Asmeey tawuce sama da sauri dakinsu tawuce taje tai wanka tai brush tafito tai shafe shafen ta sannan ta dauko wani white shirt mai boturi tasaka sannan tadauki black skirt daidai ita tasaka tadauki black veil tai rolling daya mata kyau ta dauki wani LV bag mai kyau ta hada yan abubuwa da wasu books da jotter ciki ta feffesa turare sannan tafito daga dakinsu, gidansu is big flat da akwai 2more flat ciki, flat din dake left and right sai dakin Baban su at the center sai dakinsu na mata agefe na maza ana dayan gefen babansu, right flat din tawuce da saurinta da dan kunne a hannunta tabude kofan ahankali ta shiga ciki. Gambo ce kadai a falon tana goge goge ansaka turaren wuta dakin na kamshi sosai, ahankali tace ina kwana Gambo murmushi tamata tace Asmeey an shirya gyadamata kai tayi da saurinta tawuce bedroom na Mom tai knocking ahankali kusan 1min akace come in bude kofan tayi ahankali ta shiga ciki, dakin Mom yahadu iya haduwa komi nata is well organized, ga bango guda da duk books ne acikin shelf, Mom ce zaune kan wani couch mai bala in kyau taci gayu sosai tasaka wani lace mai kyau hadadde, ga glass akan idanunta tana aiki dawani iPad dinta, harta karaso wajen kanta na kan iPad bata dagoba, dukawa tayi agabanta cikin muryanta mai sanyi and very fresh tace Mom Good morning dagowa Mom tayi tabita da kallo daga sama har kasa fuskanta ba walwala, wani irin murmushi mai kyau tama mamanta tace Mom bazan kara makara ba sorry karki fushi dan hararanta Mom tayi cikin muryan kasaita da iko tace kinyi breakfast? Girgiza mata kai tayi tana mikama Mom dan kunnenta tace Mom samin karba Mom tayi tanabin dankunnayen da kallo dasauri Asmeey ta tashi tahau kan kujeran ta daura kanta ajikin Mom tana shakan kamshin da mamanta keyi mai dadi tawani sauke ijiyan zuciya kaman irin yaron dayayi shekara baizo jikin mahaifiyarsa ba, tai lamo ajikinta, dan kallonta Mom tayi for few seconds sannan tasamata dan kunnen, cikin kakkausan murya tace dagani dasauri Asmeey ta dago daga jikinta Mom tasake kallon yarinyar saikuma takai hannunta ta daga black veil nata tana kallon gaban white shirt nata tace banace anytime kikasa white shirt haka ki dinga sa singlet ba aciki can t u see yanda bra naki ke showing dan komawa baya kadan tayi da mahaifiyar tata gabanta na faduwa hankali kaman mai tsoron magana tace Mom duka sunyi datti ne but yau duk zan wanke wani kallo Mom ta mata hakan yasa tasake matsawa daga kusa da ita dasauri, girgiza kai na takaici tayi tace be very very careful Husna or you will not like me kikai provoking din kinsanni very well stand up open that drawer ki dauki sabon singlet tashi tayi dasauri ta tawuce wajen drawer tajawo sabon singlet taciro tabude shi daga leda black ne mai kyau sai kawai ta cire rolling na gyalen tabude shirt nata tadan kalli Mom ganin bata kallonta yasa tacire rigan ta ijiye kan gado zata dauki singlet tasaka authoritatively Mom tace zonan Husna dasauri Asmeey tajuyo takalli Mom dataga ta tsareta da idanu saikuma tadan kara singlet din gaban kirjinta cikeda kunya ta taho ahankali har gaban Mom, muryanta har rawa yake tace gani Mom Mom irin iyayen nan ne masu lura da yaransu sosai, masu sa ido, ga basu tarbiya, yaranta must do abinda takeso ne dukansu haka ta rainesu har yarage saura biyu gabanta yanzu da Asma u da Munir, wuyanta Mom takai hannu ta taba tace yaushe eczema yakamaki? Zaro idanu Asmeey tayi cus ita bama tasani ba tace ni Mom an ina ? Wuyanta gabaki daya Mom tashiga dubawa zuwa bayanta saikuma ta juyo da ita hannunta tasa, tashi daya ta karbi singlet datake kare kirjinta dashi ta ijiye a gefe, Asmeey tadan sunnar da kanta kasa, ahankali Mom tabi saman kirjinta da kallo tace stand up tashi tayi dasauri agaban Mom, Mom tabi cikinta da kallo sannan da masifa tace eczema ko ina a jikinki dame kike wanka? Ina soap naki? Murya chan kasa gabanta na faduwa tace yakare Mom aharzuke tace tun yaushe ? Gaban Asmeey faduwa yake bana wasaba tace the 3rd day dakika bani Mom namata wani kallo tace mesa baki gayamin ba ? Dasauri tace Mom ai munada sabulu dayawa a bathroom dinmu anyone nagani sainai wanka dashi shiru Mom tayi saikuma chan cikin kakkausan murya tace re very stupid, wawiyan yarinya kawai mara wayau, shashasha sauke kanta kasa Asmeey tayi ahankali hannunta yahau rawa, Mom tace wani irin stupidity zaisa ki kasa gane cewa you ve always had a sensitive skin? Waya cemiki u can use just anything kika gani kiyi wanka dashi eh? Why do I waste my money ina saimiki separate abubuwan skincare batare da bari kinyi using sabulan da mayukan da Babanku ke kawo muku ba, If you ever made that kind mistake again saina sabamiki shashasha kawai, bacemin daga gani ki wuce ki maida kayanki kizo kiyi briefing dina on case file dana baki last lemme see idan kinyi wannan gyadama Mom kai tayi asanyaye duk tayi wani iri tawuce ahankali tasaka singlet din sannan tasaka shirt dinta, bata maida veil dinba tazo wajen tabude jakanta taciro file da Mom tabata jiya tabude tadago kanta takalli Mom kirjinta na dukan uku uku, Mom tace bani distinction na case din but I prefer persuasive brief, inason statements of facts, then give me substantive issues and procedural issues gyadama Mom kai tayi hannunta nadan rawa tasake bude jakanta tadauko wani book nata datai jotting komi, tabude zata karanta, Mom tamata wani kallon uku saura kwata tace kikaje law school haka zaki dingayi? Reading from book? how many days nabaki case din nan nace kiyi reviewing? Murya chan kasa irin na mara gaskiya tace 7days Mom tahada fuska tana karkada kafa tace idan kikamin shirme awajen nan ranki zaiyi masifan baci Asma u, drop that book I m listening gyadama Mom kai tayi saita ijiye book din gently and calmly tafara briefing Mom voice nata narawa, tun tana yi Mom na aikinta harta juyo ta natsu tana kallonta she really tried, saida takai procedural issues ne takakare Mom tamata wani kallo hakan yasa hawaye yafado daga idanunta tace sorry Mom Mom tace okay wat is procedural issues? Anatse tace Procedural issues shine irin wat is the appealing party claiming the lower court did wrong example kaman ruling on evidence, jury instructions, granting of summary judgment, etc Mom ta gyadakai cikeda gamsuwa tace okay if you know this then a case file dana baki menene Procedural issues na wajen shiru tasakeyi cus bata karanta yakai wajen ba, Mom na karkada kafafu tace 7days but bakiyi going through this case file dana baki ba sabida kwana biyu nadan daga miki kafa! This should be the last time you will try this wlh kika kara ranki zaiyi masifan baci! I want you to be the best lawyer in this entire Nigeria, I want you to pass bar exam naki, you re my daughter no body a Bauchi can mention law ba akira sunana ba Mrs Turaki and kece magajiyata my successor, you just have to work hard you have no option, you must study Asma u dole ne ba negotiation am I clear? Ahankali Asmeey tace yes Mom Mom zata sake magana aka bude kofan tareda sallama Baba ne ya shigo yana sanye da wata lafiyayyan gizna datasha aiki yabi Asmeey da kallo dake zaune akasa kan carpet gaban mahaifiyarta idanunta sunyi ja kaman ma tai kuka yace kinyi breakfast Ma Girgizama Baba kai tayi ahankali tace agogon hannunshi ya kalla sannan yazo wajen yasa hannu yadagota yace wuce kije kiyi kari, je Ammi tabaki abinci Ma u na murmushi tayi sosai Baba daban ne kawai he s very sweet, caring, and very affectionate, ahankali tace toh Baba wucewa kofa tayi yabita da kallo tafice shikuma yakaraso wajen ya zauna gefen Mom, cikeda nuna rashin jin dadi yace why are you so hard on this girl? Jibeta kaman ba Hamda na yar bakutu ba duk ta rame haba! Kin addabeta, finally tagama makarantan at least let her rest, all this damuwa yanzu na menene ita da ko list nasu bai fito ba rufe iPad nata Mom tayi tadauki Hermes bag nata tanasa iPad din ciki tace Alhaji I don t know why you are saying all this now! I ve always been like this to all yarana and Alhamdulillah kai karan kanka you are proud of my upbringing, Asma u is my daughter, no one loves her better than I do anatse Baba yace of course I know that Barrister and ina alfahari da tarbiyan da kika bama yaranmu Aya is a Nurse, Aisha is a journalist working with BBC, ga Asma u kice dole saitazama lawyer irinki while Munir na MBBS, my point is all yaran nan baki samusu pressure dakike sama Ma u ba, kwata kwata baki la akari da she s still a small gurl, burin dakikasa akanta yasa I don t even know wat you did dahar Asma u tayi WAEC at 14yrs tafara university at 15yrs she s 21 yanzu wai harta gama LLB, please go easy on her, stop pressuring her, karatu is a gradual process all this things dakike forcing nata takoya yanzu she will learn it gradually a law school, karatun dakike sata da menene menene sukesa idan tayi bacci da kyar
Chapter 7 · 0% Book details