Sashe 106
Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwaggo tabi ta gayyato da yammatan layin duk sukazo da anko da Gwaggo taraba musu kyauta cus nasan Asmeey ba kawa aka fara event na sa lalli aka shirya Asmeey cikin wani atampa mai kyau sai kallon kowa take chan kawai ta hango Aya da Aya sun shigo kunga wani zabura da Asmeey tayi tai wajensu tarungumesu sai kuka la ikaha illallah bata taba sani zasuzo ba she was so so so happy sai kawai suka kamata suka shiga filin suka kama hannunta suka fara rawa DJ nasa waka Aya taciro yan 500 tana manna mata hakama Aysha for the first time ever sai Asmeey taji yes yau tana aure ana bikinta, Mamie ma tafito da su Mamie da Mama da Mamie bata wani kulata duk sukahau yima Asmeey manni sai kunya takeji aka gama Aysha ta zaunar da ita tace acigaba da lallen bari muje mu gaida kowa ta gyadamusu kai suka wuce cikin gida ana shiga da akwatinansu, ciki chan dakin Asmeey sukakai aka kulle dakin suka fito aka dawo compound yammata na rawa Aya tace yaushe kikai ashobe girls haka ? Akunyace tace duk yaran Gwaggo ce bansan u ba Aya na kallon Asmeey tace ciki gareki? Akunyace Asmeey ta sunnar dakai. EPISODE 8 BONUS Ya Aysha tace is obvious mana Ya Aya bakiga sugar a bakinta ba datazo mana oyoyooo kin kallonsu Asmeey tayi, Ya Aya tace ahhhh lallai Ya Hamadi anyi sharp shooter yanzu har ya lodama yar kanwata ciki murmushi Ya Aysha tayi Asmeey sai kunya takeji rannan har yamma anama kowa lalle yau shine rana na farko da Mamie step back daga kula da Asmeey sabida yanda sisters nata take over cus Ya Aya saida tazo har kitchen dinma ta dafa mata indomie da kanta. Baba da Kawu suka iso da yamma, su Aya na lurada yanda Hamad yakirata yafi akirga they were happy and at peace da yanda Asmeey build her love life koba komi mijinta loves her, go mota ya siyamata, ga waya ga MacBook ga, ga ga Alhamdulillah is all they can say. Da daddare suka duba akwatinan da Hamad yamata sun tsorata zinarori har sun kasa kirgawa harda diamond, like Hamad shows yanason matarsa wlh aka ciro kayan da zata saka gobe ga makeup artist available wanda Hameed yayi wannan cus Hamadi baisan yanda ake komiba. Wuraren 9 wayanta yahau ringing Aysha tace wai Ya Hamadi ya kosan Hameed ne kadai ango yana abu sai kace baima yarinya ciki ba kaman wani sabon ango dariya Ya Aya tayi tace mehaka ina ruwanki? Amarya da Ango ne wlh tunda yanzu za ayi biki, dauki wayanki Asmeey ahankali ta dauki wayan takai kunnneta duk yayyin na kallonta, murmushi sukaga tayi ta gyadamai kai ahankali tace toh Yayaa tazare wayan tadan juyo ganin kallonta suke da gudu tarufe fuskanta tashiga mikewa tadauki hijab tasaka lallenta yayi kyau sosai Aya tace adawo lpy Suka cigaba da ciremata kayan data zaba sauran duka za a kyautar da credentials dinta da komi. Falonsu makeel da jama a surutu kawai ake Mamie ta tsareta da ido hakan yasa taje wajenta adan kunyace tace Yaya na kirana Mamie naje? Dan hararanta Mamie tayi tace nabaki 2min da idanunta awajen kaman nawa murmushi tayi tana kulle fuskanta tamike tafito Hamad na zaune cikin motanta tashiga tahowa sai kallonta yake bude kofan tayi tashiga motan ahankali ta zauna taki kallonsa hannunsa yasa ahankali yakama hannunta yarike ahankali yace how are you ? Murya chan kasa tace fine? Ahankali yace kinsha pregnant care dinki? Gyadamai kai tayi ahankali tace yanzun nan nasha hannunta yakai bakinsa ya manna ma kiss yana kallon lallin dayamai kyau ja da baki yamika hannu yace muga dayan tamikamai hannunta yarike duka yana kallo yace this is the most beautiful lalle I ve ever seen in my life murmushi tayi ya rungume hannunta kaman dan yaro yayi wani iri ahankali Asmeey tace menene ? Dan ijiyan zuciya yasauke yace m tired all I want is you and Mamie tahana, I just want my wife I don t mind taking you gidanmu yanzu haka all this al adun ni banso tundadai u are my wife already he sounds extremely pissed, hannunta daya ta karba daga hannunsa takai fuskansa ta shafa cikeda so dakuma tausayi tace kayakuri today is the last day dan lumshe idanu yayi wlh yagaji kwanan sa nawa baiyi komiba yanzu yadawo still baiyiba, shekaran jiya yadawo baiyi bacci ba, jiya kwata kwata yakasa runtsawa in that house yauma haka how will he cope ijiyan zuciya yasauke ya maida kujeransa baya ya kwanta ya kwantar da nata ma haka sai kawai ya matso yakama bakinta very deep kiss yamata yana sauke ijiyan zuciya kaman zai mutu da kyar yasaki bakinta yadan fuzar da iska yace kije i will see you tommorow but wlh tell Mamie nace babu wanda zai kwanan mini agida saidai akwana agidansu Hameed harsu Aya tell them dariya abin yabata Hamad is seriously angry fa bata taba ganinsa yana bori haka ba, hakan ya bala in bata dariya, ganin tana murmushi yace i look funny ko? Ni meruwana dawani biki watana uku da aure an hana mutum matarsa sabida kawai anga inada hakuri toh Allah kaimu gobe sanda wani zaiyi gigin cewa zai kwana a flat dina zasuga different Hamad wlh cus tommorow is for myself and my wife with our little Baby murmushi Asmeey tayi tace yes My Zaujee, Allah huci zuciyan kyakkywan mijina kitse da tsokan zuciyata wani shafa kirjinsa yayi yana kallonta kallon so kalaman sun gama dashi, yawani yi murmushi ya yunkuro kawai tabude motan da gudu tafice tana dariyan kunya tamai bye ta tafi ya tsaya sai kallonta yake yanda malamalan bombom dinta ke karkada ta hijab gidansa yawani mike, yakama gabansa dake masa bala in ciwo yace ahhhhh not again please kabanni haka nahuta! Gobe ne ya tada motan da kyar yayi reverse yatafi. Da asuba Asmeey ta tashi tafara amai bana wasaba dan har saida Aysha tafito takira Mamie, Mamie itama takira Musty yace gashinan zuwa salla tayi da kyar dayazo saiya mata allura dan jikinta har yayi zafi yace nan da 10 zata tashi lpy lau abarta tai bacci Aya tace wai Allah sa ba irin laulayin danayi zatayi ba mai bakin wahalan nan Aysha tace kaman ma nata tafi naki ke baki ganta ba Asmeey bata tashi ba sai wajajen 11 amman da karfinta wanka tayi dan makeup artist tazo since, abinci aka bata taci tukunna, karfe dayane daurin auren Hameed kuma immediately zasuzo nan gida sabida ayi family pictures wuraren 12 dai aka fara makeup na Asmeey anan daki ga kayan dazata saka hadaddu idanba su dasukasan Asmeey nada ciki ba baby Wanda xaice Asmeey nada ciki dan bawai yafito bane kunga yanda Asmeey tai kyau kuwa haka aka gama aka shiryata cikin white dress nata dawata IG designer tamata men! The dress is giving makeup artist din tamata gyale tasaka sarka sannan aka yafa mata net aka fesheta da turare Ammi ta shigo tace an gama? Mamie tace afito da ita tazo ta gaida jama a aga Matar Hamadi hakanan kawai Asmeey taji gabanta nata fadi Ya Aya tace Ammi zoki kaita bari mu shirya muma mufito cus basu saka ashobin su ba sai Ammi tazo takama hannun Asmeey suka fito tundaga staircase jama an falo suka fara guda bana wasaba ganin Amarya aka tashi masu waya na ciro waya anama Asmeey hoto Mamie tafito daga dakin Gwaggo itama taci gayu sosai kawai saita tsaya hakanan taji kuka yazo mata dasauri ta juya yan falo sukace Maman ango na kuka taga amaryanta mai kyau dasauri Mamie tajuyo tace karku samin yarinya kuka ba kuka nakeba zo Asmeey takai hannu zara kama Asmeey sai kawai Asmeey ta rungumeta she always love Mamie but zama da Mamie made her to love the woman beyond son data taba mata da she learned so much from Mamie ciki harda tarbiyan yara da yanda ake zamanda yara agirmammasu dudda una yara, muryanta na rawa Asmeey tace Mamie ina sonki ina sonki Mamie sosai you are the best mother I ve ever had in my life sai Mamie da Asmeey suka fashe da kuka, Mamie tadago tana kuka tana magana. Baraki dena kuka ba akwai jama a a waje basu ganki ba zaki bata gayunki Ammi da sauran mutane sukace ai kema kukan kike dasauri Mamie ta tsayar da kuka ta sharema Asmeey fuska sama sama tace ya isa ko gyadamata kai Asmeey tayi Mamie tace kaita ta gaida mutanen nan a kaita tsakar gida adanyi wasa kawayenta duk suna waje Mamie tace Mamie takoma dakin Gwaggo dan wani magana ake kan gidansu Zee akan zasu kwana Hameed ya rantse baza a kwana ba Gwaggo tace sai an kwana shine fa Gwaggo tahana Mamie sukuni Ammi na fita da Asmeey waje DJ yasa kida ashobe girls sukazo suka karbe Asmeey daga hannun Mamie sukace abamu Amarya Ammi tace ai shikenan takoma ciki abinta dan itama bata chanza kaya ba sukai fili da Asmeey akasa ciki aka fara rawa makeup artist data gama hada kayanta tafito tana murnushi tana kallon Asmeey dake rawa tafice daga gidan da gate yake abude. Ko 2mins batayi da fitaba tashigo gidan ta taho filin wajen Asmeey takai bakinta saitin kunnen Asmeey sabida Asmeey taji tace wata mata tana waje she looks like you tace nakiraki she s your Mom wai security sun hanata shigowa and she wants to give u gift she s going back to Bauchi now now Hakanan gaban Asmeey kawai yafadi sai kuma ta gyadama makeup artist din kai tace toh! Makeup artist tawuce abinta, dan juyawa Asmeey tayi tabi kowa na compound din da kallo babu su Ya Aya duk suna sama suna shiryawa Ammi ma haka but can Mom do anything to her today with all this people around? Tasan su Baba na grin nan Kawu ma haka, Ga security ma awaje? Could Mom actually come here tayi wani abu ko to congratulate her da gaske? Koma menene mahaifiyarta ne and today is her wedding bari ta shigo da ita ciki, takalli wacce tazama kaman babban kawar yar makotansu tace ina zuwa Fadila ana nemana awaje Fadila ta gyadamata kai Asmeey tayi gate tana tafiya ahankali tafito