← Book details Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 140

Sashe 58

Uwa Ko Ukuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

M SHAKUR EPISODE 3 Kayansu yaso yaje ya dauka but Hameed dake falo yasa bai iya zuwa ba yakoma sama dakinsu yabude yashiga ahankali da sallama Asmeey na zaune kan gado takallesa saikuma ta dauke kanta dasauri tana murmushi without reason Hamad yaje yazauna, kaman bazatai magana ba sai kuma ahankali tace "bakaci abinci ba Yaya" ahankali yana aiki yace "I will eat later" gyadamai kai tayi sai kuma ta kwanta a gadon tana kallonsa bacci na neman fizganta tana lumlumshe idanu, kaman daga sama yace "don't sleep ice cream and wara Babe" bude idanu tayi suka hada ido ganin yajuyo gabaki daya yana kallonta kaman wata laptop dinshi sai kawai taji kunya yakamata dasauri ta rufe fuskanta da hannayenta biyu jin sunan daya kirata dashi wai Ice cream and wara Babe, Babe fa Ya Hamadi yace. Tashi yayi daga kujeran yabude kofa yafice, sauka kasa yayi daidai Gwaggo na shigowa gidan yawani balla mata harara baitaba ganin tsohuwa mai shegen yawo irin Gwaggo ba wuni take gidan mutane sabida an mata takwara, tana tahowa tace "bansan kanayi bai naga kwayan idanunka akasa makiri, ni zakasa Asmeey taki bina? Toh wih muzuba ni da ku agidan nan za'aga wazaici wannan fadan" wucewa yayi backyard kafin tazo wajen ma, kayansu ya kwaso yasa na Asmeey a tsakiyan nasa yanda babu wanda zaimasan da nata yadawo yashigo flat din Gwaggo yagani da Mamie tana ganin Hamad tace "cimini mutumci yayi banda yahana Asama bina, nadawo bakiga kallon banzan dayakemin ba" wucesu yayi abinsa Mamie tace "bari Baban su ya shigo Gwaggo saiki gayamai" dakinsu yabude yashiga ahankali * Asmeey na kwance but idanunta biyu daga fitansa taji she's bored, wajen gadon yazo yazuba kayan dasauri ta tashi ganin nata zatakai hannunta yamata wani kallo dayasa ahankali ta maida hannunta kayan yashiga dauka yana folding zai goge gobe idan yasami time kayanta ya dauka yashiga folding Asmeey tadan saci kallonsa saikuma tamaida kanta kasa zuciyanta duk yayi melting, kwashe komi yayi zuwa wardrobe nasu Asmeey tasake binshi da kallo bangarensa taga yabude ya ijiye komi a side daya kawai zuciyanta yabata gogesu zaiyi yajuyo suka hada ido dasauri ta maida kanta kasa murya chan kasa tace "thank you Yaya" juyawa yayi zaiyi kofa yace "I am going to the mosque sai after ishai zan dawo" ahankali tadago kanta ta kalleshi, haryasa hannu a handle din saikuma gently yace "we have karatu a mosque" gyadamai kai tayi yabude kofan yafice itakuma tai shiru tana zaune awajen taji Mamie na kiranta. "Asmeey" dasauri tace "na'am" saita taso tafito Mamie tagani anan falon sama rike da kaskon wuta tasa turare aciki Asmeey tayi wajenta Mamie tace "kullum ko bana nan safe da yamma ki dinga sa turare a daki saiki kara tsaftace dakin sannan kiyi wanka kinji" gyadama Mamie kai tayi ta karba tajuya Mamie tace "sa kifito ki amsa abincinku ban kara nemanki awaje kuma sai gobe" ahankali tawuce daki ijiye turaren tayi waje daya tafito Mamie rikeda kula mai kyau da tray da plates ke ciki takalleta tace "zama ki iya daukan abubuwan nan" ahankali Asmeey tace "Mamie ki shigo" murmushi Mamie tayi tace "nida shigowa dakinku saikin haihu" akunyace Asmeey ta sauke kanta kasa Mamie tayi dariya ta ijiye mata komi akasa awajen tace "dinga dauka one bye one kina kaimu ku ciki" Mamie tawuce tasauka kasa Asmeey tashiga daukan komi one one harda ruwansu takai daki tai arranging bangare daya sannan tawuce bayi bayan tacire kayan jikinta zatasa a basket saitaji tana kunyan yamata wanki kuma but ina zatasa kayan dattin? Ahankali tacire tai folding ta ijiye da pant dinta saitaji ta kasa kawai ta dauka tawuce wardrobe tabude side nata ta ijiye kayan bangare daya daban sannan tafada bayi brush tafara yi tayi wanka da shower gel datai amfani dashi da safe na dove mai kamshi tadaura towel tafito daidai wayansa na vibrating dake kan desk. Wucewa tayi wajen ta tsaya ganin number ne is a miss call sai taga watsapp message ya shigo. "Dan kanada mata is not restriction, I love you wallahi" shiru tayi saitakai wayan ahankali zata ijiye mistakenly ta danna watsapp yabude yakaita direct chat na yarinyar nan all messages data mishi na rannan suna nan almost 50 agabaki daya chat din magana daya Ya Hamad yayi "I'm married, I wish you the best!" Tundaga nan bai kara reply ba amman haushin da Asmeey taji yakamata sai taji kaman zata kama da wuta wayan ta dauka dudda kirjinta na bugawa samin kanta tayi da blocking number on watsapp tai deleting chat din sannan tadawo calls tai blocking number sannan tai deleting tana hararan wayan sannan ta mai wayan ta ijiye tajuya tawuce wardrobe mai ta shafa a gurguje ta fesa bodyspray da turare kayan bacci ta dauko vest da short farare masu kyau vest din v neck garesa da siririn hannu sai short din iya cinya mai kyau is not sexy but it looks damn sexy ajikinta nata wani damuba dan tasan hijab zata saka tai bacci tasa hijabi tazo tai salla tasake dago kai ta kali wayan nasa ta harari wayan ranta sai baci yake saikuma chan Mom tafado mata arai mikewa tsaye tayi ahankali tawuce ta dauki wayanta dake kan table din tadawo ta zauna tana bude wayan gabanta na faduwa contact nata ta shiga but saitaga babu number Mom just na yan gidansu Baba ne ya goge? Tafadi ahankali, tanada number Mom aka saita shiga saka number zatai dailing number saita kasa sai hannunta yahau rawa gabanta na faduwa sosai ijiye wayan tayi tai shiruuu tuna Mom har yasa numfashinta yasoma destabilizing ahaka har aka kira Isha'i ta tashi tayi tai shafa'i da wuturi tana addua hannun nan ya warke tagaji yana hanata yin so many things, tashi tayi tai folding dadduman ta maida wayan ta ijiye kan table sannan ta zauna bakin gado tana jin hayaniya a falo. Shigowa gidan Hamad yayi around 9 duka yayyinsa na falon banda Ya Mustapa duk kallonsa sukayi sunnar da kansa kasa yayi yazo yasami waje kusada Hameed yazauna yace "Abba barka da zuwa" Abba yace "yauwa Hamadi ya iyalin naka kuma? Ya hannunta?" Murmushi yayinsa sukayi sai wani kallonsa suke sauke kansa kasa yayi yace "fine" Abba yakalli su Ya Abdullahi da Faisal dake zuba uban murmushi suna kallon Hamad yace "gobe Aysha zatazo tareda mijinta sun kirani" gyadamai kai sukayi Mamie tace "nima ta kirani" Gwaggo dake fitowa daga dakinta rike da charbi ta e "Allah yakawota zanji dalilin dayasa ni bata kiran ba idan kuma uwarta ce ta shiga tsaknainmu sai in sani" duban Gwaggo Abba yayi yace "Gwaggo gobe kada ki fita daga gidan nan" baki Gwaggo tasaki tana kallonsu tace "Au daman zaman nan da akayi gulmana akeyi? Ni kazace ko zakara da za'a kafe agida ahanani fita? Takwara fa Zakari da matarsa sukamin" cikeda takaici Abba yace "toh Gwaggo akace kullum sai kinje daga safe har dare fa wih zasu gaji haba mana Gwaggo ni idan baki dena zuwa ba zan tattaraki na maidaki kauye" Hameed yadan shafa kai murya ciki ciki yace "game on"kallon Abba Gwaggo tayi sosai dan babu abinda ta tsana kaman ace za'a maidata kauye da zama takalli Hameed tace "muje dakina Hameedu ka saukomin da jakata da daddaren nan zan bar gidan nan bazan kwana ba ni Abubakar ke gayama zai maida kauye muje Hameed" ahankali Hameed yace "ni tsawo a bazai kaiba" fashewa da kuka Gwaggo tayi tace "yau kasaba saukomin da jakan, shikenan Hamadi daman ya tsaneni kaikedan mini mutunci yanzu gashi an rabani dakai, kun sani a tsakiya kunamin tijara Abubakar harda cewa zai maidani kauye to lokacin barina gidan nan yayi, kokuma ku kasheni kawai kuhuta" tashi Faisal da Ya Abdullahi sukayi sukace "saida safenku" Abba dake kokarin mikewa yace "saida safen ku" suka fice Hameed yatashi yayi sama yace "I get aiki gobe good night Mamie" Mamie tace "Allah tashemu Ipy" Abba yabi Gwaggo daki Mamie takalli Hamad tace "kaci abinci?" Mamie tadan nuna rashin jin dadi tace "wai bazaka dena abubuwan haka ba? Nakai muku abinci daki go and eat" gydamata kai yayi Mamie tace "namaka shayi" sake gyadamata kai yayi, ahankali yace "gobe zan tura abinda nai designing" gyara zama Mamie tayi tace "na Microsoft"? Gyadamata kai yayi, Mamie tace "ubangiji Allah yabaka sa'a yasa kaci, Ya Allah koma waye mai dubawa ka karkato da idanunsa yaga abinda d'ana yayi, in sha Allah kai zakaci" murmushi yama Mamie saiyasa hannu yarike mata hannu kawai he missed him Mamie this few days Mamie tayi murmushi da gasken Doctor ne Hamad da Asmeey sunada so much things alike Hamad na bala'in sonta even though bawai yana wani showing haka bane, same thing haka Asmeey ke son Mom she just wish ita Mom loves the girl back, ahankali tace "zakabar Asmeey taje law school? Naga sanda Faisal yaje kwana achan yake makarantan kwana ne, zaka barta"? Shiru yayi ahankali yace "saitaji sauki tukunna" gyadamai kai Mamie tayi ta shafa kansa ahankali tace "I am proud of you Hamadi! Nagode da yanda kake kula da Asmeey" akunyace yadan manna kansa a hannun Mamie, Mamie tayi shiru saikuma chan tace "make her a full matan aure as soon as possible" dawani irin sauri yasaki Mamie yatashi, baitaba kawowa Mamie can say this to him ba yajuya zai wuce hannunsa tarike ya tsaya chak batare daya juyoba, cikeda dan damuwa tace "nasan wacece mahaifiyarta sama da kowa Hamadi! Make Asmeey taka before you loses her! Salima is not the type to back down from a fight, shirunta ba alkhairi bane, Salima never gives up!" Tana maganan tasaki hannunsa, tsayawa Hamadi yayi saiya kasa tafiya, Abba yafito yaga Hamad tsaye ga Mamie zaune tana kallonsa yace "Hamadi" juyowa ahankali Hamad yayi kansa akasa Abba yakaraso yakallesa sannan yakalli Mamie yace "lafiya"? Ahankali yace "Abba gobe zan tura gasan dana shiga" kallonsa Abba yayi sai yakai hannunsa ya shafa kansa yace "da kyau Masha Allah, Allah ubangiji ya baka sa'a! Allah ya sanya albarka Allah kuma ya dafa maka Allah yasa muji alkhairi" Mamie tace "Ameen Ya Rabbi" Abba yace "muje mu kwanta Maman Doctor kulle gidan Hamadi"gyadamusu kai yayi Abba da Mamie suka wuce sama shikuma yawuce ya kulle kofa ya kashe wuta samin kansa yayi
Chapter 58 · 0% Book details