← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 69

Sashe 9

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Muhibbah* Kwance take kan bed tanata kwasar dariya, tace wllhi shalele kana bani dariya dayawa zakasa cikina yayi ciwo Uhmmm dama burina Koda yaushe naganki cikin farin ciki ai nafi so naga kinata dariya Kuma yazamana nine silar dariyar naki, tace kafara dadin bakin naka ko Murmushi me sauti yayi yace ohh nine ma nake miki dadin baki ko baby itama dariyar tayi tace nidae banfadaba, toh waya fada kenan, "a shagwabe tace bafa ni nafada ba ni na isa aljanuna ne fa suka fada" Ai Kam zanyi maganin aljanun nan zanmiki rukiya nacire su dariya tayi tace ai bazaka iya ba kayi shiruma kar sujika suzo maka da dadare Shima dariyan yayi yace Allah yashirya mun keee my princess. Kukan shagwaba tasa mai, subhanallah meya faru? "Uhmmm tom bakai bane" Ni Kuma menayi? Ba Kai bane kake cemun princess wato ban Kai matsayin queen agurin kaba, Kai ya girgiza Yana mamakin rikicin muhibbah a gafarceni ai kinfi karfin queen agurina "you are my life" Idan kika haefomun baby a lokacin zaki tashi daga princess ki koma queen babyn mu Kuma ita zata koma princess dinmu "Fuska ta rufe kamar Yana ganin ta tace har kasa naji kunya" murmushi yayi ya gyara zamanshi yace dear ya batun zuwana gurin daddy kince na bari kugama exams yanzu me zamu jira, Hmmmm ajiyar zuciya tasauke ya mukhtar bada daddy zaku hadu ba da Abba ne saboda shi ze bada aurena tunda gaba yake da daddy idan muka gama exams yace nakirashi, toh abinda yasa ban kirashi ba Kai na ne ya kulle bana so a taso da maganan auren mu yanzu bazan iya hada school da aure ba nafiso se nan gaba idan nayi graduation tukunna Hada giran sama da kasa yayi yace bana son wata magana muhibbah na fahimta dama ni nake sonki ni nadamu dake amma ni baki damu dani ba "girgiza Kai tayi kamar tana gabanshi ba haka bane dear kaima kason ina kaunarka" katseta yayi bakya Sona da kina Sona da bazaki fada haka ba my Zahra ribar soyayya aure, ta ina kika taba ganin aure ya hana karatu? Aure baya hana karatu haka karatu baya hana aure nayi miki alkawari zan barki kiyi karatu har se kince kin gaji nida kaina zan nema miki Admission nayi miki wannan alkawarin, akanki babu abinda bazan yiba akanki zan iya sadaukar da farin ciki na in dai hakan ze sanyaki farin ciki my zahraaaa "Wasu hawaye ne masu dumi suka silalomata tasa hannu da sauri ta dauke su tace babu abinda zaka roka a gurina banyi maka ba, Kai din farin ciki na ne ya mukhy" Idan har da gaske ne abinda kike fada ina so idan muka gama waya ki kira Abba ki sanar mishi kun kamalla exams dinku, numfashi taja kafin tace alright zanyi haka in Sha Allah, murmushi yayi yace "LUV YOU" "LUVS YOU TOO" daga haka sukayi sallama ta ajiye wayan gefen bed side drower. Kwanciya tayi ta rufe ido kamar me bacci tinanin yadda zata kasance idan aka rabata da mukhtar dinta take wata zuciya na karamata kwarin gwiwar cewa hakan ma ba ze taba faruwa ba Hannu ta Kai ta dauko wayanta ta kira numbern Abba amma har ya tsinke be daukaba ta runtse idonta takara shiga duniyar tinani, Karan wayarta ne yasa tayi firgi git ta mike zaune tareda manna wayar a kunnenta "Abba ina wuni" lafiya kalau maamana, ya makaranta? Lafiya kalau Abba ai mun gama exams next week Sunday zamuyi graduation, Allah yataimaka maamana Allah yasa a fito da kyakkyawan sakamako Da Amin ta amsa Hmmmm maamana na fahimta Kiran ina nan zuwa next week Saturday in Sha Allah Murmushin farin ciki tayi tace Allah yakawo ka lafiya Abbana, Amin maamana Amma Abba da Aisha zaka tawo ko? Uhmmm this week Saturday zasuyi graduation dinsu zamu tawo da ita harda umminku da suhaila in Sha Allah Ihun dadi tayi tace "can't wait to see you Abbana" Murmushi me sauti yayi yace albishirinki? Cikin Jin dadi tace goro Ammar yadawo, zaro ido tayi kamar yana gabanta tace serious? Se Kuma tayi shiru Jin magananta yayi kama da karyatawa tayi saurin cewa Allah yakawo ku lafiya, Amin Ince dai yanzu yayanki Fu'ad yadena takuramiki? Ya mutsa fuska tayi har yanzu be dena ba Abba kace mishi yakoma garinsu, kyaleshi zanzo garin duk abinda yake miki sena ramamiki, dariya tayi tace Allah yakawomun Kai lafiya Abba amsawa yayi da Amin kana sukayi sallama ta ajiye wayan tana murmushin Jin dadi Cire kayan jikinta tayi tadaura towel ta nufa bathroom, wanka tayi tareda dauro alwala Jin ansoma Kiran magrib, pray mat ta shinfida tagabatar da sallah bayan ta idar tashiga jero addu'o'in maraice Bata tashi ba seda ta idar da isha'i kafin ta tsaya gaban mirror ta gyara gashin kanta ta bude wardrobe ta dauko doguwar riga captain ta zira ta kashe dauri ta feshe duka jikinta da turare ta nufo parlourn, tun kafin ta bayana parlourn ya dauki kamshi "Daddy sannu da dawowa" tayi maganar tana Jan kujera tazauna yauwa maamana fatan angama exams lafiya Allah yafito da kyakkyawan sakamako Amiin daddy na tafada tana zuba abinci jallof din shinkafa ne se pepper soup din naman rago, bismillah tayi tafara ci cikin nutsuwa Ji tayi alamun ana kallonta tana daga kai suka hada ido ta daga mai gira tare da maida hankalinta kan cin abincinta ranta fess tanajin wannan takuran nashi yazo karshe tunda Abba yakusa dirowa kd Ya Anas, miye ne magananniya? Allah yabaka hakuri dama mun dade bamuyi ba ai "dama albishir zanmaka" wane irin albishir ne? Nafasa fada ai, toh kar Allah yasa ki fada din Toh kun fara ko dama an rabu dayi, mummy wai danzan ce mai ya Ammaar yadawo shine yafara cemun wata magananniya Dan Allah da gaske kike, tayi Mai banza, haba shalelen daddy yi hakuri please se lokacin tayi murmushi tace Allah dagaske nake dazu mukayi waya da Abba yake cemun tare zasu tawo next week Saturday tareda su ummi da Aisha harda Aunty suhaila murna yashigayi Jin abokinshi zezo Wanda suka jima basu haduba tsawon shekaru Mummy ma farin ciki tayi sosai duk da ta wani bangaren guiwanta ya mutu kasancewar tasan dalilin zuwan na su Mummy da daddy ne suka tashi suka koma parlour su Kuma Anas da muhibbah suka shiga firarsu Suhail yace Kai doctor kamanta da patient dinka ne? Uhmmm ina ruwanka korata kakeyi ne Aa ni babu ruwana nasan aiki na can ya tarunma ne, harara aka ya watsa Mai kafin yace saboda ni kadai ne doctor idan babu ni se akace baza'a kula da patient ba Ni ba haka nace ba, amma babu komai na fahimta akwai wacce ta rike mana Kai saboda ban yarda da Kai ba kullum tun safe ka dauki mota kafita se Muna aiki a company da rana seka dauki key din mota kafita, harara yakuma wurga mai yace Kai wane irin dan sa ido ne ina ruwanka da inda nake zuwa kaima idan kaji haushi kayi budurwan mana Seka fadama wanda bashida budurwan, kafada ya daga Mai alamun kai kasani Mikewa tayi tama Anas sallama ta bude fridge ta dauki goran ruwa ta nufi bedroom........... *Yau dai na danyi kokari ko [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 17* *Aisha* Zaune suke a parlour sunata fira, "tace ya Ammaar na kosa Saturday tazo mu tafi kd". "Hmmm! ai dole ki kosa saboda ku hadu da muhibbah ku ishe mutane da rashin Ji ko?". "Aa ya Ammaar kasan mun dade bamu hadu bane, munyi missing din juna, Kuma ina so muje naga graduation dinsu". "Toh Allah ya kaemu, Nima nadade ban hadu da Anas ba over 5 years" "tace ai ya Ammaar bancin Muna video call muma da yanzu mun manta kamaninka". "yace nima ai da nashigo gidan nayi tinanin bakuwa ce, seda mummy tacemun autanta ce kafin na gane yafada Yana dariya" "itama dariyar tayi" Juyawa wajen Abba tayi kafin "tace Abba har yanzu ba'a kai ma tailor dinkina dana muhibbah ba Wanda zamusa ranan graduation dinta" Aisha keda muhibbah rigimar ku iri daya "nakira tailor din yace gobe ze kawomiki na graduation dinki se kibashi sauran kayan" Ummi ce tayi murmushi "tace ba dole rigimar su tazama daya ba tunda sun fito daga a hali daya" dukansu sukayi dariya "Ai danma bamu taso guri daya b... Karar wayanta ya katseta, dauka tayi ta kara wayan a kunnenta tace 'yar halak yanzu muke maganarki dasu ya Ammaar". "tace no wonder shiyasa naji gabana nata faduwa ina tauna harshe Ashe gulmata kikeyi." "Harara ta watsamata kamar tana ganinta tace gulmanki ke awa?" "Dariya tayi tace matsayina na Auntyn ki mana" "Tafdi wllhi Allah ya kiyaye kizama Aunty na, kwata kwata da wata nawa kika girme ni". "Tabe Baki tayi kamar tana gabanta, oho dai koma da second ne dai na girmeki dole kicemun Aunty". "Kefa se a hankali mubar wannan maganan cewar Aisha" "Abba yacemun Saturday kuna nan zuwa" "In Sha Allah Saturday zakiganmu harda Aunty suhaila ma dasu ummi" "Can't wait to see you dear, Allah yakawomun ku lafiya, Nima naso nabiyo flight yau natawo graduation dinki se mu tawo tare Kona huta da takuran ya Fu'ad amma daddy yace aa". "Dariya ta kwashe dashi tace dama nace muhibbah na can cikin ukuban ya fu'ad, aini kwana nan na huta ji na nake kamar tsuntsuwar da tasamu ta kufce daga keji." "Uhmm! kedai bari ina cikin yanayi, shiyasa har nakosa kudiro garin nan ko zan huta." Da haka suka cigaba da firan su sannan tace "ki gaisharmun da ummi." "Zataji, good night" Abba!ummi!ya Ammaar "good night, ta fada tana daga musu hannu". "Shima Ammar sallama ya musu ya wuce". "Ajiyar zuciya me nauyi tasauke tace nidai Alhaji daza'aji ta tawa da kun hakura da hadin nan da kuke Shirin yi, har ga Allah bawai bana son hadin bane itama muhibbah diyata ce dukansu ina kaunar su, kawai ina tinanin abinda ze je yadawo ne duba da yadda suke takun Saka hankalina be natsu da lam..." "Ya isa ya katseta, bana son nakarajin bakinki kan abinda ya shafi auren nan idan ba haka ba zakiyi mamakina babu abinda ze faru se alkhaeri" "Kayi hakuri ban fada
Chapter 9 · 0% Book details