Sashe 23
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dukiyarshi. Sunada yara biyar Maza biyu mata uku, Salamatu ce babba se Haruna, Abdullahi, Bilkisu se Kuma Mariya itace karama. Sun samu gata a wajen mahaifinsu duk cikin kauyen sun fita daban abincin gidansu ko wasu 'yan birnin basa cin irinshi Koda yaushe abokansu suna gidan safe da yamma saboda sun san iyye seta cika musu tire da abinci sunci sun koshi sannan da yamma idan baba yadawo duk seyabi kowa da tsarabarshi baya banbance tsakanin yaran makota da yaranshi. Yasa su a makarantar gwanati dake cikin kauyen sannan ya dauko musu me lesson a gida mutanen gari nata gulman yaki aurar da yaranshi mata saboda yadda ake kawo musu harin da sunan soyayya duk da wasu kwadayin dukiyan mahaifinsu kesa su zuwa neman auren yaran, ba iya karatun zamani ba hatta na addini seda ya dauko musu malami inda yake koyar dasu a gida hade da yaran makwafta, yayi kokari sosai wajen ganin ya basu tarbiya Kuma mahaifiyar su ma ta taimaka mishi sosai wajen ganin sun gina yaran akan hanya me kyau duk kudin mahaifinsu besa su wulakanta Wanda bashida shi basa banbance kansu a cikin abokansu, ranar da babu makaranta yana tafiya da mazan gona suna taimaka mai. Bayan mazan sun gama secondary school ya yafara koya musu kasuwanci inda ya bude musu babban shagon hatsi a cikin kauyen har ya Kai sukan bi kasuwannin kauye, Ranar lahadi da laraba suna zuwa kasuwar badume, Ranar juma'a suna zuwa kasuwar BICHI, Ranar alhamis Kuma shuwaki, Ranar litinin Sha nono se Kuma Ranar talata Dan zabuwa, Ranar asabar kadai suke hutawa kasancewar ranan babu kasuwa. Suma matan suna gama secondary ya aurar dasu Salamatu da Mariya suna zaune nan cikin kauyen ita Kuma bilkisu aka kaita wani karamin gari Rimaye dake makwaftaka da kauyensu. Rayuwa nata tafiya ciwo ya kama baba ga shekaru noma ya fara gagaranshi ga sha'anin kasuwa baya barin su Haruna kama mishi tun yana iya yi har ciwo yaci karfinshi ya Kai baya iya komai, kwana dayan da suke hutawa ya koma ranan zuwa gonansu ana haka Allah ya karba ran baba sunyi kuka kamar ba gobe, hatta makwabta sunyi kukan rashi kowa kyawawan dabi'un shi suke fada iyye har kwanciya tayi a asibiti itama kamar bazatayi rai ba. Tun bayan rasuwar baba ragamar gidan ya dawo hannunsu gaba daya, iyye ta fara Sana'ar kuli kuli duk yadda suka so hanata fir taki tace zama hakan babu dadi ba yadda suka iya dole suka kyaleta, suna iya bakin kokarin su hatta 'yan uwansu mata duk da sunyi aure basa karkashin kulawarsu hakan be hana su yimusu Sha tara ta arziki su aikama ko wacce har gidanta, tun bayan rasuwar baba Haruna ya koma siyar da kaji da tumakai kasancewar dama tun baba na da Rai shi yabar ma ragamar kula da dabobin saboda yanada son kiwo, shi kuma Abdullahi yaci gaba da siyar da hatsi. Kasuwancinsu nata bun kasa Haruna na zuwa Abuja Saida tumakai da kaji musamman lokacin sallah dakuma lokacin Christmas. Shawarar ciga da karatu sukayi saboda ilimi shine gishirin zaman duniya, dan idan bakada ilimi ko kasuwanci kake se a cuceka, Koda suka samu iyye da maganan bata hanasu ba tayi musu addu'a da fatan nasara, ana fara registration jamb suka biya Aiko sunyi sa'a sun fito da results me kyau Nan suka fara neman Admission, A Kaduna polytechnic suka samu admission department of Business Admin. A kasuwan kawo suka bude babban shagon hatsi, Ranan talata suci kasuwan kawo, ranan laraba suje kasuwan laraba can cikin gari, Ranan sati suje kasuwan sati dake unguwan dosa. Kasuwancinsu be hanasu karatun su ba sun fita da kyakkyawan sakamako. Sunji dadin rayuwa a kd saboda kasuwancinsu na tafiya musu daidai hakan yasa Koda suka kammala school basu koma kano da zama ba sedai suje ziyara ana haka Haruna yasamu matar aure acikin kauyensu Khadija anan garin ya barta tareda iyye se dai yazo yayi sati ya koma Shima Abdullahi yazo yaga gida ya koma haka suka dingayi, shekara na zagayowa Khadija ta haefo santalelen saurayi kyakkyawa murna wajen a halin ba'a magana sati na zagayowa yaci suna Fu'ad Khadija da jaririnta suna samun kulawa sosai wajen iyye. Wata Rana Abdullahi yazo ziyara kauye washe garin daya sauka ya tafi gurin abokinshi lawal nan wani kauye *tudun wulli* dake dan gaba da kauyensu sedai yafi kauyensu girma da Kuma wayewa a hanyan dawowa ya hadu da wata budurwa hafsat daga nan suka kulla soyayya ba'a dauki lokaci ba iyaye suka shiga magana aka daura aure, itama nan gidansu ya kawota suke zaune da iyye dakuma Khadija. Suna zaman lafiya sosai, Fu'ad Koda yaushe yana hannun hafsat ko fita zasuyi ita take goyashi, suna girmama iyye kamar mahaifiyar su tare suke aikin kuli itama ta daukesu tamkar 'ya'yanta na cikinta, shekara Daya da auren Abdullahi hafsat ta haifo Mai 'ya mace kwana Daya tayi a duniya ta koma seda shekara ta zagayo kafin ta kara haifo da namiji ranan suna yaci suna Suhail. Arziki ya bunkasa har ya Kai ga sun bude companynsu Haruna & Abdullahi Mill Rice. Companyn dasuke sarrafa shinkafa susata a inji, ya cire tsakuwa ya gogeta a zuba a buhu a dinke ta koma Nigerian foreign rice sutura gari gari, sunada ma aikata sun Kai 30, sunada direbobi sun Kai 10, su kawai sa ido sukeyi akan aikin gudun ma aikatan suyi aiki mara kyau se Kuma rubuce rubuce akan in come & out come, da Kuma ware profit da loan. Ganin ayyuka ya musu yawa basa samun dawowa gida akai akai iyye tace su gina gida su maida matansu can zasufi samun nutsuwa. Haka ko sukayi cikin kan kanin lokaci suka gina gida dan madaidaici a unguwar sarki gidan part 3 ne kowa ne part 3 bedroom ne da kitchen se single room a tsakar gida da toilet acikinshi. Part Daya na iyye Daya na hafsat Daya Kuma na Khadija lokacin da zasu dawo fir iyye tace bazata biyo su ba sunyi magiya amma a banza dole suka kyaleta, duk da hafsat ta haihu amma har lokacin tana tare da Fu'ad daga karshema dakinta ya koma da kayanshi Yana da shekara 4 akasashi makaranta shikuma Suhail yanada shekara 2, Fu'ad na nursery 3 Suhail Kuma na nursery 1. Kullum companyn su kara bunkasa yake hakan yasa suka yanke shawaran bude wani branch a Adamawa haka ko akayi Haruna ya gina tankame man gida a Adamawa ya koma da iyalinshi Mummy da Ummi sunyi kukan rabuwa da juna, Shima daddy da Abba ko wanne ka kala kasan basa cikin mood me dadi dan dai komawar tazama dole ne a rayuwar nan babu yarda indai baka tsaya akan dukiyarka ba bazakaga dai dai ba nan suka bar Fu'ad saboda sun San idan suka karbeshi zasu tauyeshi dan yafi sabawa da hafsat da suke kira da Mummy. A can ya bude katon gidan gona. Shikuma Abdullahi yacigaba da Jan ragamar kula da companyn na kd, Shima ya gina tankame man gidanshi a unguwan rimi low cost suka tattara suka koma. Komawar su ummi Adamawa keda wuya tasamu juna biyu kamar hadin baki itama Mummy Allah ya kawomata rabon, Ummi ta haifo diya mace Maiminatu babu nisa a tsakaninsu itama Mummy ta Haifa mace Asma'u, bayan shekaru Ummi ta Haifa Suhailat, Mummy ta Haifa Anas ba nisa tsakaninsu ummi ta Haifa namiji yaci Muhammad sunan baba shine ake kiranshi da Ammar seda suka dan jima kafin Mummy ta Haifa mace akasamata Fatima taci sunan iyye ake kiranta da Muhibbah shikuma wata uku tsakani ummi ta Haifa Aesha. Bayan Fu'ad ya kammala secondary school dinshi aka turashi karatu India shikuma lokacin suhail yana SS 1 yana kammalawa Shima yabi Fu'ad, saura shekara 2 suhail ya kammala Fu'ad yagama nashi karatun inda ya dawo Nigeria a babban doctor baban Asibiti ya bude. After 2 years Fu'ad yadawo Nigeria inda shikuma ya Karanta business Admin hakan yasa yake Aiki a companyn su daddy, Shima Anas business Admin ya Karanta haka ma Ammar. Tun lokacin da a halin suka shirya gaba daya sukama Kano tsinke Iyye tayi farin ciki tarasa inda zata sasu tsabar farin ciki itama su Abba sun rushe mata gidanta sun mata ginin zamani 2 bedroom da bayi harda kitchen, yayarsu da kannen Suma sun rusa gidan mazajensu sun musu ginin zamani, ta dauko yarinyan Baaba Salamatu tana tayata 'yan aikace aikace Suma su Abba sun diba fili a cikin gidan sun gina masaukin su, Kuma har yanzu basu dena noma ba se ma abinda yayi gaba suna biya ana yimusu sannan sun samu me kula da gonakin. Tun zuwan da a halin sukayi gidan iyye ta fahimta rashin jituwa tsakanin Muhibbah da Fu'ad dan Muhibbah ta tsani taji ko motsin shi zata hade rai ta tsuke baki tun zamanshi a gidansu take Jin haushin shi acewarta yacika ta kura tunda ta taso ta sanshi a gidansu dan ko Hutu yazo daga India gurin mummy ke sauka befi yayi 1 week a Adamawa ya dawo kd Kuma da tayi laifi yake sa belt ya zaneta shiyasa take Jin haushin shi se bayan gama school dinshi ya koma Adamawa saboda asibitin daya bude a can. Lura da rashin jituwansu yasa iyye zaunar da Abba da Daddy ta umarce su ko bayan mutuwarta su hada Fu'ad da Muhibbah aure. Abba yace "in Sha Allah zamu cika umarni" Daddy ya numfasa "in Sha Allah Iyye se kinga auren da idanunki". "Allah ya muku albarka yashirya xuri'a, Allah yajikan mahaifinku" "Ameen". Shiru sukayi suna kallon yadda ta tafi duniyar tinani, haka takeyi a duk sanda ta tina da rasuwar mahaifinsu. Bayan Muhibbah ta nuna bata son auren Abba takanas ya taso yazo yasamu iyye ya fadamata abinda ke faruwa tace "Au haka Fatsuman tafada, to kar Allah yasa ta soshi ai Muma ba zabinmu akayi ba aka auramana mazajenmu Banda yaran zamani mu a lokacinmu har a daurama aure da mutum bazaka taba ganinshi ba gurgu ne makawo ne duk bazaka sani ba se randa aka kaika gidanshi Kuma ka zauna lafiya da mijinka gashi yanzu har kukan rashin su muke" kawai seta fashe da kuka. Abba yashiga lallashinta "kiyi hakuri Allah yajikan baba". "Ameen, Ameen Haruna, Amma nayi rashi babba bazan iya dena kukan rashin malam ba har na koma