Sashe 64
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya koma bakin gado ya zauna, dole ta tsaya Ummi ta gaggasamata jiki babu daman raki se hawaye kawai ke bin kuncinta. "tashi ki shiga cikin ruwan" dan waro idanu tayi, a zuciyarta tace nashiga uku na yau dai so ake sena mutu za'a kyaleni, ganin ta tsaya taki motsi ta kyaleta bata Kuma magana ba ta fice, ta turo Fu'ad ta bar dakin. Bataji zuwanshi ba sai ji tayi yayi sama da ita, be direta ko ina ba se cikin ruwan ta zabura zata mike ya maidata, yana shafa bayan ta, ya tsuguna ya tallabi kanta ya sauke lips dinshi saman nata yashiga aikamata da french kisses, ya tura hannunshi cikin gashinta yana ya mutsawa, Tuni tamanta tana cikin ruwan zafi ta biyemai, Sun jima a haka kafin ta sabule bakinta tana binne kanta a kirjinshi, yayi dariya tareda nadota a towel suka fito. Shida kanshi ya shiryata ya kwantar da ita yaja blanket ya lullube iya chest dinta, yayi pecking goshinta ya fice tabi bayanshi da kallo tana murmushi, ta runtse idanunta baccin gajiya yayi gaba da ita. Har su Ummi suka shigo dakin akama baby wanka aka shiryata bata san wainar da ake toyawa ba tayi nisa a baccinta tsabar gajiyan daren jiya Ba ita ta farka ba se 1 brush tayi ta nufa parlour, kan kujera ta zauna ta gaisa da mutane anata mata barka sedai ta danyi murmushi. Baby na hannun Aunty Maiminatu, ta kuramata idanu a zuciya take mamakin hakurin yarinyan tun safe da tayi feeding dinta bata karajin kukanta ba, su kuma basu kawomata ita ba Kallon da taga tanama babyn yasata yin murmushi tareda dauramata yarinyan kan kafafunta, kasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta. "Muhibbah ni kike Jin kunya? Rike 'yarki itama tana so taji dumin mamanta ai tamayi kokari, na kai miki ita na ga baki tashi ba" murmushi ta danyi tasa hannu ta rike baby. Ta gefen ido ta Kalli Aunty Maiminatu, ganin hankalinta baya kanta, ta mike da yarinyan a kafada tashige daki. Kan kafafunta ta ajiyeta tana kare mata kallo tanajin yadda kaunarta ke ratsa jini da jijiyarta bataji ko kuda zata bari ya tabamata diya indai ba bisa kuskure ba. Hannu ta kai ta shafa kumatunta ta saki murmushi tanajin sanyin dadi, yarinyan na shirye cikin kayan sanyi masu taushi pink color se tashin kamshi take. Mutsu mutsu ta farayi, ta dan jijjigata aiko ta bude idanu dan dama ta gaji da baccin, pecking kumatunta tayi tana dariya tace, "baby na kintashi? kinajin yunwa?? zaki sha nono???" Tayi maganan tana Kai hannu ta zuge zip din rigarta, tashiga feeding dinta tareda runtse idanu tana Jin azaba amma ta daure saboda tasan tanajin yunwa kawai dan batada rigima ne. Tana koshi ko ta koma baccinta, tana kokarin kwantar da ita su Umaina suka shigo da murnarsu, sukayi hugging din ta ta saki dariya tana gyara zamanta. Ramlat tace, "Da safe Aesha ta kira take fadamana kin haihuwa, dah kamar zamu tawo, Umaina tace mudai bari a tashi ma tawo" tayi maganan tana daukar baby Umaina tace "kinga baby 'yar lukuta, tubarkallah masha Allah, Allah ya rayamana ita akan sunna" Ameen duk suka amsa dashi Ba Muhibbahn ba, ba Aesha ba duk su hudun suka shiga shirme, nan ciki aka kawo musu lunching suka hadu suka ci suka dora daga inda suka tsaya, Umaina kam sunki ajiye baby data fara bacci se sun san yadda sukayi suka tasheta wai sunfi son suga idanunta a bude saboda ta gane su da kyau a school karta dinga yimusu kiwa, ita ko kamar tayi satikai se binsu take da kallo da ta gaji tasa kuka su kuma su shiga rarrashi amma sunki bada ita, se yamma suka wuce Aesha ta rakasu compound tasa driver ya maidasu gida. Kwanaki nata tafiya har jibi suna, mutanen KD sun hallara gidan Ummi................ *Dan Allah kuyimun uxuri idanuna sun sani gaba, kunburin ya rage amma zugi yakemun sosai, ga kaikayi, bana jure kallon hasken screen, wannan page dinma inayi ina ajiye wayan a hk dai na lallaba nayishi sbd jira bb dadi* AMINIYAR ANGO *[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD* *AMINIYAR ANGO* *Page 59* Suna zaune a halin gidan suna fira cike da so da kaunar juna, Aesha naba Aunty Asma'u labarin darun da akayi da Muhibbah wajen feeding baby da dramar da akasha wajen wanka, anata dariya. Asma'u tace, "Ai nasan za'a rina, indai raki ne daga kan Muhibbah an gama, Allah kadai yasan dramar da akayi da ita wajen labour, saboda sanin ragwantan ta da mummy tayi kullum hankalinta na kanta, tunda Muhibbah tashiga watan haihuwan ta batada magana se na autan ta" baki ta tura tace, "Aunty! Bakiji azabar dana keji bane, har yanzu idan ina fedding dinta inajin zafi dauriya kawai nakeyi, Amma baki ga dauriyar da nayi bane wajen labour, ki tambaya hearty kiji ko kuka ma banyi ba". Tun dazu dasu ke firar su be ko dago Kai ya kallesu ba, se da yaji Muhibbah tace ko kuka batayi ba a labor room, hada idanu sukayi ya mata kallon babu kyau karya. Murmushi ta sakarmishi ta kauda kai gefe. Dariya sosai sukayi, Aesha ta harareta ta tabe baki kana tace, "Wllhi idan duk jikina kunne ne bazan yarda ba, kedin ce zakice kin haifo yarinyan nan ko tarinki ba'a ji ba? Ah gaskiya ki canza wata maganan amma wannan bata Karbu ba". Aunty Asma'u tace, "Ai bama se kin rantse ba Aesha, wacce gurin feeding seda aka kwashi 'yan kallo da ita inaga Kuma labour, Allah kadai yasan abinda ya faru" "Wllhi Aesha kin rainani, kinga gadon baccina, ko kin manta ni yayarki ce?" "Tafdi yayata a ina? 3 months fa kachal kika bani, ta ina kika zama yayata" "Ko da yini daya ne dai na rigaki shan iskan duniya, Kuma yayanki nake aure kinga karewan yayama, Auntyn ki ce nii" tsaki taja tace, "Kyaji dashi" Ganin Ummi ta mike ta musu seda safe, shima ya mike yana duba agogon dake manne a bangon parlourn, 30 minutes after 9, kallonta ya danyi yace, "Bakijin bacci ne?" Ya fada yana daukar baby ya nufi bedroom. Bata kulashi ba tace, "Aunty ko hauka nayi a lobor room kar kuga laifina, Ashe haka akeshan wahala wajen nakuda? Wllhi da ace yara sun san abinda iyaye ke ji tunda ga daukar ciki har zuwa haihuwa, da ko wuta iyaye sukace yaro ya shiga bazeyi musu ba bare ya tsaya jayayya dasu, Ya Allah tukuicin aljannah firdaus ga mahaifiyar da tayi silar kawomu duniya, sannan tukuicin aljannah firdaus ga mahaifin daya sha wahalar rayuwa sabodamu ya hayyu ya qayyum". Dariya sosai sukayi harda rike ciki kana suka amsa da Ameen ya rabbi, Suhailat tace, "Muhibbah fa anci kwakwa, haihuwa yakin mata" tayi maganan tana cigaba da kyalkyala dariya. Numfashi ta sauke kana tace, "Bari kawai Aunty Suhailat, nidai kam nayi auta daya ta isheni, bana fatan na Kuma daukar wani cikin ina bazan iya ba" Harara maimunatu ta watsamata tace, "Ai indai ciki ne, kima shirya dan kafin kiyi arba'in kin dau wani" gabanta ne ya fadi ta waro idanu tareda fadin "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, Aunty wane irin kafin inyi arba'in na dau wani cikin?" tayi maganan kamar zatayi kuka duk ta rude kamar wacce akace tana dauke da cikin yanzu haka a jikinta. "Miye na salati, ba ke dadi miji ba ko suna ba'ayi ba amma koda yaushe Kuna nanike da juna, Ki bari yamiki wayau tun baki arba'in ba ki fara sabon laulayi, ni banga amfanin dawo dake gidan nan da Ummi tayi ba duk ta takuraku, nace mata da anyi suna ta tattara ta maidaki gidanki, tace saboda wankan baby da kula dake baze yuwu tabarki ke kadai da danyan jego ba ki cuce kanki kiki shiga ruwan zafi, zuciyarta bazata nutsu ba koda ta nema miki tsohuwa saboda tasanki da rikici, iyye Kuma tace se bikin ya Suhail zata zo" kafin tayi magana Asma'u tace, "Ki barta yaro be san wuta ba se ya taka, Muma ba duk hakan ce ta faru damu ba a farko, muna goyo muna laulayi, kuba Romeo and Juliet ba Allah yakara dankwan kauna, Allah yakawo twins nanda 9 months mu dawo suna". Idanunta ne suka kawo ruwa, cikin sanyin murya tace, "Wllhi Aunty babu abinda mukeyi, shi yake zuwa da kanshi bani nake kiranshi ba, kuma ma ai banida tsarki bare kuyi tinanin wani abu" tayi maganan hawayen idanunta na silalowa Kafadarta Aunty Maiminatu ta dafa "Ai kwanan nan zakiyi tsarkin wasu basa jimawa, ya danganta da yanayin ki, wasu matan basa 2 weeks jini be dauke musu ba, ki fahimce ni bance kunayin wani abu ba, ai ba laifi bane ma dan kunyi wani abu ina mata da miji ne keda dashi?" Kai ta jinjina. "Abinda nake so ki fahimta shi fa namiji babu ruwanshi, ya dinga miki dubara kenan har seya samu abinda yake so ya kunsa miki ciki daga karshe yabarki da wahala, befi yabiki da sannu ba, ba ina nufin daukar ciki wahala bane, amma kina da karamin goyo kina laulayi ya kike tinani kema kinsan lamarin is not easy". Seda taja fasali kafin taciga da magana "ni bance ki daga hankalinki ba, Kuma bance karki ba mijinki kulawa yadda yadace ba, amma karki bari yamiki wayau. Yanzu jikinki a bude yake zaki iya daukar ciki akoda yaushe, bance miki karkuyi romancing juna ba amma kiyi taka tsantsan, nidai shawara nake baki ba umarni ba". A kunyace tayi kasa da kanta tana wasa da yatsunta kamar zata ballasu, Asma'u tace, "Kibarta idan kunne yaji gangan jiki ya tsira, yanzu ba lallai ta gane yaren ba se tsautsayi ya hau kanta ga baby ga ciki, muna shagalin bikin ya Suhail ita kam tana kwance". Aesha na dariya tace, "Kuma wllhi bikinmu zamusha, se ma munso idan munzo wucewa mucemiki sannu, nayi miki mutumci ne ma na daukamiki baby" Duka ta Kai mata tana harararta, Suhailat tace, "Kinga Aesha! Allah ya kaimu aurenki kema bamusan abinda zakiyi ba" Muhibbah zatayi magana taji kukan babynta kafin tayi wani yunkuri tajiyo muryan Fu'ad yana kwada kiranta "Heebbah! Fateema!!" baki ta dan tura ta zira kafafunta kasa tana sa takalmi, ta mike tayi musu seda safe, suna mata