Sashe 33
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
batareda ta Kalle inda yake ba. Gefen Muhibbah taje ta zauna ta riko hannunta "Lafiya kike kuwa?" "Ummi yunwa nakeji" abinda kawai ta iya fada tana kwanto da kanta kan cinyar ummi. Mairo ta kwalama kira tace ta kawo abinci kana ta Kai dubanta ga fu'ad tace "Lafiya naga kabaro asibiti tun yanzu?" "Lafiya kalau Ummi, Muhibbah ce batajin dadi na kaita hospital akasamata drip" Cikin ladabi tazo ta ajiye abincin tana ma Muhibbah sannu, tashi kici abincin, babu musu ta zauna ta karba plate din da Ummi ta zubamata abincin ta shiga ci da sauri dan yunwa takeji sosai tun dare bataci abinci ba rabonta da sa wani abu a cikinta tun custard din data Sha da rana. Cikinta ne ya kulle ta yatsina fuska ta ajiye abincin "Ya akayi, ko a dafa miki wani abincin ne?" Ta tambaya cikin kulawa. "Aa Ummi na koshi" "ki fada ko wani abin kike so yanzu se mairo ta dafa miki" "Babu abinda nake so" "Sannu, ko zaki je daki ki kwanta ne?" Kai kawai ta gyada ta mike ta nufi dakin Aesha Dining aka Kai mai abincin yace a dawo dashi parlour, center table din dake parlourn ta janyo ta ajiye abincin. Aesha na ganinta tace "Matar Yaya Lafiya kuwa?" Yatsina fuska tayi "Banajin dadi ne" "Ya Salam meke damunki?" Tafada tana Kai hannu kan goshinta. "Zazzabi" tafada tana zama gefen bed din. Hannu ta Kai tashafa cikin Muhibbah tana 'yar dariya tace "Anya kuwa Muhibbah kodai Yaya yayi ajiya ne" Bige hannunta tayi ta watsamata harara "Gaskiya ban yarda da keba" tsaki tayi tace "Dadin abin da mijina dai ko" tayi maganan tana kwanciya. Dariya Aesha tayi "Kyaji dashi dai mudai fatan mu Allah ya inganta" tanaji tana tsokanarta tayi banza da ita har bacci ya sureta. "Gobe mairo zata koma gidanka tana kama ma Muhibbah 'yan aikace aikace tunda ga laraba idan yaso da yamma se driver yaje ya dakkota ta kwana nan". "Ummi sanin kanki ne bana son takura, da an bar maganan mairon nan please" Bata fuska tayi "Wane irin takura, kaida tun safe kake fita kafin ka koma gida ma ta tafi, aiki yanama Muhibbah yawa ga zaman kadaici babu dadi, musamman yanzu da batada lafiya tana bukatan me taimaka mata" shiru kawai yayi dan ya fahimce inda ummi ta dosa can Kuma yace "Tom shikenan ummi Allah ya kaimu goben lafiya" "Ameenna! Ameenna!!. Se bayan magrib suka nufa gida a masallacin unguwar su yatsaya yayi sallahn isha'i kana suka karasa gida. Tana shiga daki wanka kawai tayi ta nufo parlourn ta zauna kan kujera tana zaman jiran shi se faman duba time take, har ta fidda ran ze sauko ta jiyo kamshin turarenshi. Be kalla ko inda take ba yace hadomun coffee, ba musu ta shiga kitchen ta hada mishi zuwa yanzu ta fahimce abubuwan da yake so a zuba mai ciki. Mika mai tayi da yatsa ya nunamata center table a Kai ta ajiye ta koma ta zauna tana wasa ya yatsun hannunta. "Yaya" ta kirashi a darare "All ears" abinda yace kenan batare da ya kalleta ba. Dama maganan school dina ne, bece komai ba ta dora "Dama nafi son (AUN) ne makarantar da aka nema ma Aesha admission. "Okay zanyi tinani" ya fada can kasan makoshi "Idan babu matsala nace kozan koma kd ne se a nemamin admission a (KASU) Kaduna state university, idan akayi hutu se indinga dawowa yola, idan kasamu time seka dinga kawomun visit" ta Kai karshen maganan cikin rawar murya. Wani Kallon bakida hankali ya watsamata ya mike ya barta nan zaune Tana ganin ya mike itama tayi saurin mikewa tayi tinanin gurinta ze nufo se taga ya nufa stairs. Ganin tsayuwar baze mata ba itama tayi bedroom dinta jiki a sanyaye ta rufo kofar da karfi......... *Banyi editing ba bacci nakeji kuyi hkr dan Allah* *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 38* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Tun safe ta tashi wanka tafarayi ta shirya ta sauko down stairs har ta nufi hanyan kitchen taji ana danna door bell ta nufa kofar, tana budewa taga mairo tsaye, murmushi tasakarma ta tareda bata hanya tashigo. "Ina kwana madam" murmushi tayi har hakoranta suka bayyana tace "sorry ni yakamata na fara gaisheki, Ina kwana" "Lafiya kalau, ya jikinki?" "Naji sauki" "Allah yakara sauki" "Ameen, Nagode". "Hajiya tace nazo na dinga miki aikace aikace ina dan tayaki zama" "Allah sarki Ummina eh munyi maganan da ita jiya" "Shine nace kiyimun bayanin abubuwan da zan dinga yi, da inda zan dinga shiga kar in wuce gona da iri" Dariya tayi "Haba Aunty mairo ai ke 'yar gida ce kina iya shiga duk inda kike so indai a down stairs ne, up stairs ne kawai idan ba takama ba babu ruwanki da shi saboda kinsan halin ogan" murmushi kawai mairo tayi a ranta tace ni kam nasan halin baudaden mutumin nan, yanzun ma dan bazan iya ja da maganan ummi bane da bazan zo gidanshi aiki ba. "Aikin ki Kuma gyaran dakunan kasa ne se parlour da Kuma kitchen, dakina kuma dana oga ni zanji da aikinsu, girkima na safe dana dare duk ni zan dinga yi ke Kuma na rana kadai zaki ke mana, fatan kin fahimta?" "Eh na fahimta madam" "yauwa kije seki fara aikin ni Kuma zan shiga kitchen na hada break fast naso ma na makara". Da toh ta amsa ta wuce dan tafara aikinta. Tsaye tayi a kitchen din tana tinanin me zatayi Sharp sharp saboda yau bata shiga kitchen din da wuri ba can wani tinani yazo mata. Irish potatoe ta dauko ta fere ta dan sa salt ta soya, ta daura frying pan a kan gas ta zuba oil, tayi grating kayan Miya ta zuba ciki tadauko spices da seasoning ta zuba ta juya, ta dauko hanta ta zuba ciki takawo murfi ta rufe. After 15 minutes ta dauko soyayyen Irish din ta zuba cikin pan din tayi mixing dinshi ta rufe for 3 minutes ta kashe gas din ta juye Irish din a food flask ta dauko ta nufo dining. Koda ta fito har mairo tagama gyaran gidan dan dama ba wani dirty ke akwai a gidan ba "Sannu da kokari Aunty mairo, har kin gama?" "Nagama, se Kuma me yanzu za'ayi?" "Babu komai ki zaba dakin da kike so seki maidashi naki duk idan kinzo seki dinga zamanki ciki, idan Kuma kika gaji seki dawo parlour, feel free nanma kamar gidan ummi ne babu wata matsala" Kai ta jinjina tana yaba kirkin Muhibbah duk da batayi mamaki ba dan Sam family basuda matsala sunada kirki da son mutane shiyasa take mamakin inda Fu'ad ya dauko halinshi na miskilanci da Ji da Kai. "Nagode" "babu godiya bari na dauko miki burner kisamana turare idan kin gama seki je kitchen ki dauki break fast dinki" tafada tana nufan stairs Hannunta rike da burner ta nufo parlourn ta Mika ma mairo "Ga turaruka nan a show glass" tun kafin ya karaso kamshin turarenshi ya sanar da ita fitowarshi, juyawa tayi ta hangoshi yana taka staircase din a hankali kamar baze taka ba, seta tsinci kanta da kura mai ido, yayimata kyau sosai. Sanye yake cikin tsadadden yadi me taushi fari Kal Wanda yakara fitar da ainayin kyanshi kayan sun amshi jikinshi se suka fitar da asalin kalan fatarshi ta chocolate colour, gashin kanshi da kullum yake gyarashi kamar wata mace kwance luf kamar ba fulatani jikinshi ko ina gashi ne hatta hannayenshi gashi ne kwance luf, yanada tsayi dan idan suka jera bazata wuce kirjinshi ba. Ganin yakarasa saukowa tayi saurin dauke kanta, mairo tashiga gaisheshi hannu kawai ya dagamata ya nufa dining yaja kujera ya zauna, karbar burner tayi ta bar gurin ita kuma ta nufa kitchen dauko cup. Tunda ta fito kitchen din yake kallonta ta kasar ido tafiya take a natse cikin sanyin jikin da dama dabi'arta ne, Fara ce tass, tana sanye cikin doguwar rigan Karan miski me taushi maroon colour wanda yakara fitar da hasken fatarta anyimata dinkin straight gown kirjinta cike yake fam babu inda be ciko a jikinta ba bazakace 'yar 17 years bace fuskarta ce kawai ta dan nuna yarinta se Kuma idan suka hadu da Aesha suna shirme zaka tabbatar akwai yarinta tattare dasu, kasan rigan ta dan kamata seya fitar da shape dinta na coca cola, ta ja hulan kanta baya gashin gaban kanta da sajenta me santsi baki sidik kwance luf, a hankali ta cigaba da takowa inda yake duk taku se ko ina na jikinta ya motsa. Ganin ta karaso yayi saurin maida kanshi kan wayarshi. Serving dinshi tayi ta ajiye mai plate din gabanshi dagowar dazeyi idanun su ya sarke dana juna, zuba mai manyan idanunta tayi tana kara ganin kyawunshi sajen fuskanshi ta kurama ido seta ga ya birgeta kamar ta kai hannu ta shafa. manyan kaya na mishi kyau sosai duk da be damu da sasu ba se ranan Friday ko Kuma idan zeje wani daurin aure. Dauke idonshi yayi yaja tsaki yafara cin abincin shi. Kunya ne ya kamata ta zauna tana hada tea can kasan cup ta hada tafara Sha a hankali, sauri sauri ya kammala ya