Sashe 50
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
keda mijinki amma seki dinga bada mata ke yanzu bakisan yadda zaki rarrashi mijin ki ba ashe ma karatun da hajiya hawwaye da Wanda Auntyn su ya mukhtar din ki sukayi miki ya tashi a banza kenan" "Bansaniba ni se kin koyamun, karki Kuma cewa ya mukhtar dina kijimun yarinya ya mukhtar din wacce ze aura dai" Baki tasaki "Yau Kuma?" "Yanzu da dah ai ba daya ba yanzu ni matar wani ce, dan Allah mu ajiye maganan shi abinda ya wuce ya wuce mu manta baya mu fuskanta gaba" Murmushi tayi taji dadin yadda ta cire mukhtar a zuciyarta Ashe akwai wannan ranan da Muhibbah zataki a danganta mukhtar da ita "Eh yanzu ana shan love da ya Fu'ad ai dole a mance mana da ya Mukhtar din mu" "Ai kema macece zaki iya aurenshi, ni inama so muyi wata magana amma se mun hadu" "Toh shikenan Mrs lover ai ranan nan kwana nayi tinaninku irin wannan kauna haka ko kunyar idanuna bakuji ba daga ke har yayan" "Kai Aesha wllhi kin faye sa ido ai ko zan cema me gadi yadena barinki shigowa gidan nan tunda gulma ke kawoki" Dariya tayi kan sukayi sallama ta ajiye wayan. ********* Tana kwance ta takure da kaganta kasan tana cikin damuwa karar wayanta ne yasa ta Kai hannu ta janyo ta batare da ta duba me Kiran ba tayi picking ta kara a kunnenta "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" Jin muryarshi yasa ta saurin tashi zaune muryarta har rawa yake tana saurin cewa "Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh, Barka da safiya my d" "Kintashi lafiya?" "Alhamdulillah" "Sorry karki ga inata miki yawo da hankali wllhi madam ce jiya jikin ya tsananta amma yau in Sha Allah zanzo na sameki gida muyi magana" Batasan lokacin da tasaki murmushi me sauti ba "Allah ya kawoka lafiya my dr" "Ameen" daga haka ya ajiye wayan Jingina tayi da jikin gadon ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na suya shidai Koda yaushe uzurinshi matarshi matarshi anya ko gidanshi ta shiga zataji dadin zama kuwa yadda yake kaunar matarshi din nan Wata zuciya tace me wuyan ki mallakeshi ne kema ze zo yafara kaunarki Kuma dole ya sauke duk wani haki daya rataya a wuyanshi Wayan yabi da Kallo yana mamakin kanshi beta ba ganin yarinyar da ta birgeshi bayan matarshi kamar zeeee ba shidai yasan beta ba Jin digon sonta ba. Numbern Suhail yashiga dialing seda ya kusa tsinkewa kan yayi picking "Barka da safiya my in law, tunda burinka ya cika kasamu kanwata ai dole kadinga mantawa damu" Tsaki yayi "Wllhi kaida Jafar matsala ne, kun cika sa ido" Dariya sosai yayi "Kai dama baka son gaskiya ai, ya akayi? Tunda naga kiranka da sassafen nan nasan da dalili" Seda yashafa kanshi kan yace "na ajiye ma sako baka duba ba, fatan zakayimun alfarman dana nema" "Haba Fu'ad ai kafi karfin alfarma a gurina in Sha Allah indai be gagareni ba zanyi ma, bari na duba sakon" daga haka ya ajiye wayan. ******** Ummi ce ta fito ta sameta zaune kujeran dake kusa da ita ta zauna "meyafaru yau bakije school ba?" "Hmmmm ummi Ya Fu'ad ne yace bazamu kara zuwa school ba" "Dama nace jiya laifi kukayi ai se kuyita zama tunda bakwajin magana" "Akan sauban ne Kuma wllhi Ummi tunda kika ce karmu kulashi ban kara cemai komai ba dama Muhibbah bata taba mai magana ba" nan ta kwashe abinda ya faru tafada mata har pretending din da Muhibbah tayi Dariya sosai ummi tayi "Allah yashiryaku ku bari yasan abinda kukayi zaku bama 'yan garinku labari" "Nifa ummi babu ruwana bansan ta shirya abinta ba seda ga baya take bani labari" "Yanzu se kusan yadda zakuyi kusamu ya sauko" "Toh ummi ai wannan aikin Muhibbah ne tunda mijinta ne" "Kwaji dashi daga ke har ita nidai nawa ido" Se 5 ya tashi gidan ummi ya nufa suka gaisa Yana zaune har Abba ya dawo dan sun jima basu hadu ba se dai su gaisa ta waya seda suka gaisa kan ya mike ya musu sallama Masallaci ya tsaya yayi magrib kan ya karasa gidan su zeeee Bata yi zumudin zuwanshi kamar na kwanaki ba saboda zuciyarta fal yake da fargaban abinda ze sanar mata Seda ya fara shiga ya gaishar da Ammi ya ajiyemata kudi tanata sa mai albarka kan ta mai masauki dakin baki Bata wahalar da kanta tayi girki ba dan tasan baci zeyi ba, snacks da drink ta kawo mishi kan ta zauna suka gaisa duk jikinta a sanyaye "Ina wuni" "Kina lafiya?" "Alhamdulillah" tafada a takai ce "Zainab" saurin dagowa tayi ta kalleshi Jin ya kira ta dan bata tabaji ya ambaci sunanta ba "Nasani kina so na, kin kaunace ni duk abubuwan da namiki na shariya da sauransu be tabasa kin sauyamun ba ko kiyi fushi hakan ya tabbatar mun da kina mun hakikanin so na gaskiya, kinsani kowa nada kaddararshi a rayuwa ki dauka Sona kaddararki ne sannan kisa a ranki duk abinda kikaga baki sameshi ba toh ba rabonki bane, kamar yadda na fadamiki inada mata Kuma bamu jima da aure ba sannan Koda ma mun jima banida ra'ayin auren mata biyu, banki aurenki saboda wani dalili ba ko daya hasalima nayaba da tarbiyarki dattakun Ammi yayimun hakan yasa nake so ki kasance cikin family na ki daukeni matsayin yayanki duk abinda dan uwa yake yima kanwa nayi alkawari zanmiki shi duk abinda kike bukata karkiji komai just call me, kinsani bazan zaba miki abinda ze cutar dake ba akwai cousin brother na yayan madam dina ne Ina nema mai alfarmar ki bashi matsugunni a zuciyarki inada yakinin ze baki kulawar data dace kiyimun wannan alfarman please" Tunda yafara magana tayi kasa da kanta hawaye na bin kuncinta Jin kalaman shi na karshe yasa ta dago kanta dasauri ta Kalle wasu sabbin hawaye masu dumi suka shiga kwararo mata................ *Gobe idan nadawo ban gaji ba zanyi update Nima na kosa na kammala munzo gangara amma is under probability kar ajini shiru aita kwadamun kira Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD Aminiyar ango* *Page 50* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 "Bazan miki dole ba Karki Kalleni ki amsa abinda ranki be so ba kinada right din amincewa ko akasin haka, dan baki amsa tayani ba bazan taba rikeki a zuciyata ba amma zanji dadi ne yayinda kika mun alfarma kika sama ma dan uwana guri na musamman daga zuciyarki" Seda taja majinar kuka kan tace "kafi karfin neman alfarma daga gareni kaifa kace zaka zaman mun wa, wllhi na amince har cikin zuciyata Allah yasa haka shine mafi alkhaeri" ta karashe maganan tana kuka me tsuma zuciyar me karatu Jingina bayan shi yayi jikin kujera yana jin kukanta na hawa kanshi amma be hanata ba saboda yasan idan bata fitar dashi ba ze zo ya tokare mata kahon zuciya ne ya hanata sukuni. seda tayi me isanta kan ta tsagaita da kukan ta Koma tana sauke ajiyar zuciya hade da shassheka, itama da tayi kukan se taji nauyin dake zuciyarta ya ragu "Nagode da wannan alfarman" Kai kawai ta Jin jina har lokacin bata dena shassheka ba "Toh miye na kukan? Ya isa haka mana" ya fada yana mikewa Ajiyar zuciya tasauke tare da mikewa danyi mai rakiya Har wajen motarshi ta rakashi ya shiga seda taga ficewarshi daga gidan kan ta juya tashiga ciki. ********** Agogon dake manne a bangon parlourn ta kalla 5 minutes to 6 tsamm ta mike ta nufi kitchen Kayakin da zatayi amfani dasu wajen yin *Chicken yam porridge* ta fara fiddo wa seda ta tabbatar ta matso da duk abinda zata bukata kusa kan ta daura pot kan gas. Gyarariyar kazanta ta dauko ta zuba cikin pot din ta dauko seasoning, spices and onion ta zuba kan ta rufe pot din. Seda ya tafasa sannan ta kawo ruwa ta zuba cikin Kazan ta rufe. Doya ta dauko ta fere ta yankata 'yan daidai ta wanke taje ta bude pot din ganin kazar ta dawu sosai kan ta zuba doyan ta dauko kayan Miya da manja ta zuba ta rufe Seda doyan ta dawu ta juye a food flask ta juya wajen hada mango juice. Mango da pineapple ta dauko ta fere su ta yankasu kananu ta zuba cikin blender tazuba ruwa ta dauko banana da dan citta ta zuba tayi blending din su ta tace ta juye tasa a fridge. Dakinta ta haura tayi wanka tayi sallahn magrib tana zaune tana azkar bata tashi ba seda tayi isha'i kan ta mike ta nade pray mat din tareda zare hijjab din jikinta Gaban mirror ta tsaya ta shafa lotion da humra bata shafa komai a fuskanta ba ta nufi wardrobe ta dauko wata riga ta sa ta tsaya gaban mirror tana kare ma kanta kallo batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba se kuma kunya ya kamata tana kokonton fita da kayan amma ta fuske ta dauki turare takara feshe jikinta ta nufi down stairs. Fridge ta nufa ta ciro juice gudun yayi kankara ta ajiye a dining Parlour takarasa kan kujera ta zauna ta janyo wayarta ta shiga karatun novel Yaso ya rasa sallah yana shiga masallacin ana kokarin tada sallah Koda ya fito masallaci seda ya biya mall yayi siyayya kan ya karaso gidan Har ya tura kofar parlourn ya shiga ya karasa daf da ita bata lura dashi ba saboda hankalinta gaba daya na kan waya habarta ya dago cikin hannunshi a zabure tayi saurin daga idanunta suka fada a nashi boyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke dan ta tsorata tunda bata ji dawowarshi ba Hawayen dake bin kuncinta ya kai hannu ya dauke tareda zama gefenta ya dagota ya dorata kan cinyar shi ya zagaye hannunshi a kugunta ita kuma ta kwanto da kanta kan kirjinshi tareda gyara kwanciyarta kan jikinshi ta sakalo hannayenta ta bayanshi ta rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya Yana shafa kanta yace "Waya tabamun sanyin idaniyata?" "Babu kowa fa" tayi maganan a sanyaye dan novel din data karanta ya sanyaya mata jiki Kuma ya karamata ilimin rayuwa "Toh meyasamun Kee kuka haka uhmmmm" yayi maganan yana shinshinan gashinta Nannauyar ajiyar zuciya tasauke "Wllhi hearty wani novel na karanta *HAIHUWA DA HANJI*" "Shine yasakamun ke kuka?" "Allah Yaya book din akwai tausayi ne, a book