Sashe 65
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dariya suma suka mike suka nufi bedroom. Da sallama akan lips dinta tashiga dakin, tazauna gefenshi takai hannu ta karbi babyn tafara feeding dinta. "Firan me kukeyi haka kika barni tun dazu ina zaman jiranki?" A dan tsorace ta kalleshi, a ranta tace kar dai ace yaji maganganun da mukayi dasu Aunty. "Ina magana kinyi shiru" murmushi tayi tace, "Firan rayuwar duniya mukeyi, kasan idan 'yan uwa aka hadu se aji kamar kar a rabu" "Toh sannu me 'yan uwa, yanzu Kam lokacina ne, gobe seku daura daga inda kuka tsaya" dariya tayi tace, "bazaka tafi gida bane?" Tayi maganan tana duba wayanta taga 5 minutes after 10. "Uhmmm yau anan zan kwana" bata ba maganarshi muhimmanci ba ta kwantar da yarinyanta ta fara shirin kwanciya. Daukan babyn yayi, ya dauki dabino ya tauna ya lasamata a baki yamata kuduba. Seda tagama shirinta tsaf ta hauro bed din, ya dauramata yarinyan kan kafafunta ya kai hannu ya shafa kumatun babyn yace, "My little zahrah" kallon rashin fahimta tabishi dashi, dama tun tuni take so taji sunan yarinyan amma ganin beyi mata maganan ba yasa tabari zuwa ranan suna tasan dole zataji. Kai ya jinjina yace, "Fateema, kuma Ammin Fateema" shiru tayi, dan duk tinaninta sunan Ummi ko na mummy ze sa, ajiyar zuciya tasauke tace, "Amma hearty ya akayi kasa mata fateema, bancin suna na ne, kuma nima takwara akayima iyye" gira ya dage yana dan murmushi yace, "Nima masoyiyata nama takwara, kinsan dai bana wasa da alkawari" Kai ta gyada "Kintina ranan da kika rokeni alfarman nayi miki alkawari, ko bayan mutuwarki zanyi miki takwara?" Murmushi me sauti tayi tace, "Uhmmmm, amma ai cewa nayi idan bana raye, Amma yanzu ai ina raye, Meyasa kayimun takwara?" "Saboda ina kaunar me sunan, Kuma haka zalika ina kaunar sunan ta dalilin me sunan. Idan duk 'ya'yana zan samusu fateema sunan baze taba gundurana ba, saboda sunanki ne habeebtee" yayi maganan yana jan hancinta. Jikinshi ta fada tana dariya hade da hawayen farin ciki, yasa hannu yana ya rungumeta yana bubbuga bayanta, kana ya dagota ya rungumeta ita da babyn, yasa harshenshi yana sharemata hawaye. "Banaji akwai macen data kaini dace, samun miji kamar ka sai wacce ta taki sa'a, ina alfahari da kasancewar ka miji a gareni kuma uba ga Little, ina taya kaina murnan samunka matsayin abokin rayuwa, Anta Hayateee wa farhatee, uhibuku hubban kaseeran, I LUV YOU WITH ALL MY HEART" "LUVS YOU TOO MY ONE". Daga haka ya karbi babyn ya kwantar kan bed dinta, ya koma gadon ya janyota jikinshi ya matseta yashiga yawo da hannunshi a jikinta yana wasa da gashinta, yasa hannu ya tallabi kanta ya daura lips dinshi saman nata yana kissing dinta cikin kwarewa, hannunshi ya tura cikin rigarta yashiga yawo dashi, tayi saurin rike hannunshi ta sabule bakinta daga nashi tana sauke ajiyar zuciya tace, "Yaya katashi ka tafi gida, dare yanayi" "Anan zan kwana" yayi maganan yana kara matseta a jikinshi Kamar zatayi kuka tace, "Dan Allah hearty nidai katafi kar wani ya kamamu mun kwana tare muyi abin kunya, idan ma bazaka gida ba ko dakin ka na nan gidan ka tafi ka kwana please" "Kamarya kar wani ya kamamu, wani sabon muke aikatawa ne? Ko ba ma'aurata bane mu??" "Uhmmm nasan mu ma'aurata ne, amma kaga be dace ba ko ummi idan taganmu zata iya yin fushi tace da anyi suna na tattara na barmata gidanta" "Kinga ni da zatayi haka ma wllhi da naji dadi, koke nasan a ta kure kike, bamusamun sakewa, ni dama dan babu yadda zanyi ne shiyasa kike zaune gidan nan amma banaji zan iya bari har kiyi 40 days a nan" shiru tamai saboda ta fahimta ta matsa da koranshi fada zasuyi kuma taja ya kafe cewa a dakin ze kwana. Little zahrah ya dauka ya maidata ya kwantar kusa da mamanta yaja blanket ya rufesu, ya musu addu'a ya rage AC tareda kashe hasken dakin ya rufe musu kofa ya fice, bedroom dinshi na gidan ya wuce ya kwanta. Tana Jin fitarshi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta janyo little ta rungume a haka har bacci ya dauketa Da safe bayan Ummi tama little wanka ta shiryata cikin hadaddun kaya riga da wando navy blue, ba'a samata kayan sanyi ba se socks da hula saboda yanayin garin babu sanyi, an nadeta cikin swaddle me taushi Shima navy blue, se tashin kamshi take. Ummi na gama shiryata ya karbeta, yana dan sosa keya yace, "Ummi taci sunan mamanta" fadada murmushi tayi cike da farin ciki tace "Masha Allah, Allah ya rayata akan sunna" dan murmushi yayi ya fice, A kofar dakin Abba yayi knocking aka bashi izinin shiga, ya tura kofar bakinshi dauke da sallama, kan carpet ya zauna yashiga gaishar da Abba. Ya amsa cikin kulawa yana mika hannu ya dauki babyn dake bacci hankalinta kwance. "Fu'ad har yanzu baka sanyamata sunaba? Kana jiran mene??" Kasa yayi da kanshi yana sosa keya yace, "Abba nasanya mata, Fateema" murmushi yayi yace, "Masha Allah, me babban suna. Kace na Kuma samun mamana, Allah ya rayata akan sunna ya albarkaci rayuwarta gaskiya naji dadin wannan suna". Gida yafara cika ana 'yan aikace aikace duk da abincin ma order aka bayar, har su snacks din duk ordern su aka bayar se dan aikace aikacen da baza'a rasa ba, Rufaida da summy ma sun hallaro yolah, Muhibbah tsabar murna har tarasa inda zatasa su, daki suka shige ana ma me jego lalle suna fira, sun tina rayuwar makaranta lokacin da suke secondary school sunata kwasar dariya, ita kuma Rufaida tana tino musu lokacin dasuke islamiyya irin dramar dasuke sha, daganan aka gangaro labarin duniya Muhibbah na musu tsiyar suyi aure suka mata ca suna raddi kamar zasu cinyeta, nan suka wuni suna abu daya har aka gama mata lallen itada Aesha suma akayi musu a hannaye. Washe gari da safe, gida yasoma cika se hayaniyar 'yan suna kake ji 'yan uwa da abokan arziki an hallara kama daga mutanen yolah har na KD ba'a barsu a baya ba baby taga kara kai kace biki ake, umman mukhtar da Aunty zahrah ma sunce baza'ayi babu su ba. Murna gurin Muhibbah ba'a magana kamar ta daukesu ta goya. Tare suka jero yana rungume da little zahrah da suke kira da unaisah, hannunsu gimtse cikin na juna. Yana sanye cikin dakakkiyar shadda me maiko fara kal anyi mai dinki zamani ya kafa hula yakawo babban riga yasa kamar wani ango, takalminshi baki haka ma agogon dake daure a damtsen hannunshi. Itama tana sanye da irin shaddan dake jikinshi anyimata hadadden dinkin doguwar riga, takalmanta bakake, hakama mayafinta black, agogon dake daure a damtsen hannunta kuma golding abin hannunta da zobunanta na gold suma golding color, tasha make up, sunyi kyau har sun gaji dakyau bancin babyn dake hannunsu zaka rantse amarya da ango ne. Itama unaisah ba'a barta a baya ba anciremata nata wankan, tana sanye cikin wasu tsadaddun kaya Kai da ka gansu kasan sunja kudi, blawus ne white colour takalmin kafarta ma white, head band dinta white colour. Tun dasuka fito aka kafa camera's akansu aka fara kashe musu hotuna, compound din gidan akayi decoration dinshi an kawatashi harda su balloons ga wani katoton banner an rubuta sunan baby a jiki, hall yaso ya kama Ummi tace compound din ma ya isa, idan suka kama hall zasu wahalar da mutane. Nan suka tsaya camera man yashiga kashe musu hotuna suna canza style, sunyi tare da unaisah daga baya suka ba Aesha ita aka shiga yimusu su kadai, wani ta kwanto kan kafadarshi, wani Kuma ta juyo suna facing juna seta zira kanta wajen kafadarshi tana kallon baya, wani kuma ya tsaya a bayanta ya sakalo hannu ya daura a kan cikinta, wani kuma sun dan daga kafafunsu a tare kamar zasuyi tafiya aka dauka. Duk abinda basu samu yi a bikinsu ba seda suka fanshe, nan 'yan uwa aka dinga shiga ana hotuna tare dasu. Fu'ad daya gaji ya fice daga gidan gaba daya, Aunty zeeee bata zo da wuri ba seda aka kusa gama hotuna, itama batayi kasa a guiwa ba tashiga akasha hotuna da ita. Can na hango Suhail gefe da muradin ranshi zeeee sunata Shan kauna. Aesha da Mukhtar ma na can gefe jikin motarshi suna soyewa cike da farin cikin burinsu na mallakar junansu matsayin mata da miji ya kusa cika. dan Abban mukhtar yaje yasamu daddy yanema ma mukhtar auren Aesha har anyi fixing time inda aka barshi za'a hada bikin dana Suhail. Jafar ma da Rumaisa abin ba'a cewa komai, dan tun jiya daya raka Suhail fira gurin zeeee, yaga Rumaisa tun anan ya pola ya karbi numbernta wajen zeeee, tun a daren sukayi waya yana ta fitar mata da sirrin zuciyarshi ita kuma tanata basarwa amma yau dasuka hadu ta ware suna musayar kalamai cike da tsantsar farin cikin daya kasa boyuwa akan fuskokinsu, Kunsan dai yadda sabuwar soyayya take farkon haduwa, mutum jinshi yake kamar yana saman gajimare yanajin kamar yafi kowa farin ciki a duniya. Anci ansha an dan rausaya, anyi barin naira Abban unaisah ya barar da kudi, duk Wanda ze tafi se an bishi da jaka me dauke da hoton baby da sunanta, da uban abubuwa a cikin jakan. Taro ya tashi lafiya, little zahrah taga so da kauna, tunda ga kan Abba har zuwa Aesha da take karama a family kowa yayi bajinta kowa da akwatinshi, musamman Abba kam ya barar da kudi ba'a cewa komai saboda an ma mahaifiyar takwara. Daddy da mummy da suke can ma sun barar da naira, haka su summy dasu Umaina sunyi bajintarsu, Mukhtar ma ba'a barshi a baya ba dan akwati guda ya ciko da kayan baby da kudade masu yawa a cikin envelope, batasan lokacin da hawaye suka silalomata ba lokacin da ta shiga daga tsala tsalan kayan babyn da Mukhtar ya ciko akwati dasu, a zuciyarta take fadin, tabbas SO ba karya bane, tayarda mukhtar domin Allah ya sota, domin ko bayan aurenta be taba canzamata ba ko a fuska, ko lokacin da yake ja baya da ita yayi ne domin ta mance dashi ta rungume mijinta tayima iyayenta biyayya, a lokacin bata fahimta haka ba seda ga baya ta gane gata yamata domin da ya ciga