← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 69

Sashe 37

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su uku suka fito daga class Aesha da Umaina se zuba suke ita kam maganan su ya dameta amma batace musu komai ba suka cigaba da tafiyansu. Kallon Muhibbah ta danyi cikin kulawa tace "Lafiya?" Yatsine fuska tayi "Kaina kemun ciwo, amma nasha magani" "Eyyyaaa sorry, Allah yabaki lafiya" "Ameen tnx" "Aesha dazu naga mutumin Fateema Allah yasa be gannin ba" cewar Umaina. Dariya Aesha tayi "Dan anace ba, yanzu ke ze nacemaw...." Bata karasa magana ba ta hangoshi ya yo inda suke. "Amincin Allah yatabbata ga sarauniyar kyawawa" Tsaki tajaa tanajin kamar ta kwada mishi mari. Umaina ya Kalla "Ya ake ciki?" "Indai zan baka shawara toh kayi hakuri shine zancen gaskiya dan ba samun zuciyarta zakayi ba". tana fadan haka tabi bayan su da sassarfa. Bayan su yabi da Kallo yama rasa mezeyi wata zuciya na cewa ya hakura wata zuciya Kuma na zugashi akan karya gaza yayi iya iyawarshi wajen ganin ya mallaketa. Sun danyi gaba ta hango malam mukhtasir yana washe mata baki kara hade rai tayi kamar an aikomata da mutuwa da sassarfa ya taddosu duk su biyun saurin gaishe shi su kayi ya amsa yana tambayarsu karatu. Can kasan makoshi tace "Ina kwana" "lafiya kalau, ya karatu ana kokari ko?" ya fada yana kara washe baki. " Alhamdulillah" ta fada a takaice. Ganin tana kokarin wucewa yayi saurin cewa "Ina alkawari na?" Ya mutsa fuska tayi "Ya Salam kaga ko na sha'afa kayimun afuwa zuwa next week idan Allah ya kaimu" tana kai nan ta wuceshi fuuuuu. Kallo yabita dashi har suka bace ma ganinshi. Gidan Ummi suka nufa gaba dayansu har Umaina a parlour suka yada zango a 3 seater ta baje tun tana Jin firar su har bacci ya kwasheta. A parlourn Ummi ta samesu Umaina ta risina ta gaisheta cikin girmamawa ta da kulawa tana tambayarta mutanen gida "Aa ya akayi ta kwanta nan batashiga ciki ba?" "Wllhi Ummi nata tashin ta taki tashi" karasawa tayi taba goshinta taji babu dumi. Bacci sosai tayi dan dama ita indai tana period wuni take bacci bata gajiya. Bata farka ba se 2 ta iya sa'a tana tashi taji ciwon kan ya sauka Baccin datayi yakara sa Ummi tabbatar da zarginta. Dakin Aesha taje ta wanke baki da fuska tazo sukayi lunching se 3 Umaina ta tafi ummi ta cika mata leda da abubuwa tanata godiya har compound suka rakota sukasa driver ya maidata gida. Se 5 tama Ummi sallama Aesha ta rakota compound din gidan sukayi sallama. Tana shiga gidan jaka kawai ta ajiye ta shiga kitchen seda ta musu dinner ta haura sama dakinshi ta shiga ta gyara ta canza bed sheet tasa turare ta janyo kofar ta fito ta koma dakinta. Wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigan abaya ta zauna bakin gado ta janyo wayarta gabanta na faduwa tafara dialing numbern Mukhtar har tagama ringing ta tsinke beyi picking ba seda tayi 3 missed calls ana hudun yayi picking. Cikin rawar murya tace "H..he...llo ya Mukhtar" shiru ya danyi kan yace "kina lafiya?" "Lafiya kalau, fatan kaima kana lafiya" ta kai karshen maganan hawayen idanunta na tsiyaya. "Ina lafiya, akwai wata matsala ne?" "Aa, dama nace bari na kiraka ne mu gaisa na Kuma yimaka godiya naga sako" "Masha Allah, se anjima". "Ya mukhy" shiru yayi bece komai ba "Yanzu da gaske mun rabu?" Saurin tarar numfashinta yayi "Dan Allah Muhibbah kar ki dawo da hannun agogo baya abinda ya wuce ya wuce ki dauki haka matsayin kaddarar rayuwarmu" be jira Jin abinda zata fada ba ya yanke wayan. Babu zato ba tsammani taji an zare wayan daga hannunta dasauri ta dago kanta suka hada ido mugun kallon dake watsamata yasa tasha jinin jikinta. Bakinta ne yafara rawa tana kokarin yin magana kafin ta bude baki taji saukar lafiyayyen Mari a kuncinta a zabure ta mike tareda sakin kara tana ja da baya. Binta yake har suka kai karshen bango. Kankame jikinta tayi tana bashi hakuri "Dan Allah Yaya kayi hakuri bazan sake ba nayi kuskure". Wani yawu me zafi ya hadiye idanunshi sun kada sunyi jajir wani abu me daci ya tokare mai kawon zuciya jikinshi har rawa yakeyi hannu yasa ya fisgota ya kuma kwada mata lafiyayyun maruka har 3 kana ya tureta ta fadi. Kuka me sauti ta saki "Kiyimun shiru, wllhi ko tari kika Kuma yi sena shakeki kin mutu kowa ya huta, gardi kike kiramin acikin gida na" ya Kai karshen maganan cikin dacin rai yana nunata da yatsa Da sauri ta rike kafafunshi "wllhi Yaya tunda aka kawoni gidan nan ban taba waya dashi ba se yau natuba bazan kara ba nayi nadama" kallon da yake aikamata yasata saurin sakinshi "Bance ko tari kar ki kuma yi ba? Yaushe nafara wasa dake?" Kai kawai take girgiza wa tasa hannu ta toshe baki gudin kar tari ya kufcemata ya shaketa ta margaya kamar yadda ya fada. "Ki Kuma magana kiga idan ban buga kanki a bangon nan ba ya tawarwatse, nadama Kuma bakiyi ba tukunna". Yana kai nan yafice yana wuci. Durkushewa kan guiwowinta tayi tasaki kuka me sauti tana fadin tashiga uku. Tsoro ne ya kamata tasan baze barta haka ba gashi ya kwace wayanta bare takira Abba yakawo mata dauki can dubara yazo mata ta mike daker ta zira hijjab ta dauki kudi cikin sanda ta sauka daga stairs din. Sauri sauri ta karasa ficewa daga parlourn ko driver bata nema ba ta fice daga gidan me gadi yabita da kallon mamaki Anya kuwa lafiya madam ta fito hankali tashe cikin dare, maida gate din yayi ya rufe ya koma ya zauna. Napep ta tara tashige a bakin gate din gidan ya ajiyeta ta mika mai kudi tana ji yana ta tsaya ta karba chanjinta daker ta iya cemai ya rike tabarmishi chanjin, bubbuga gate din takeyi da karfi tana waige da sauri me gadi yazo ya bude dan dajin wannan bugun bana lafiya bane a hankali ya dan leka ganin Muhibbah yasa yayi saurin bude mata tashigo da kallo yabita a ranshi yana tambaya to wannan ko lafiya?. A sukwane ta shiga parlourn ta fada jikin Abba tana kuka, dago ta yayi dasauri "Mamana lafiya? Meke faruwa?" "Abba na shiga uka Yaya" "menene ya samu yayan?" Hankali tashe a halin gidan suka kara so gurin Muhibbah suna tambayar lafiya amma se kuka take "Meyasamu Yayan naki?, bashida lafiya ne? Ko mutuwa yayi?" Ummi ta jero mata tambayan a kidime cikin kosawa da Jin amsanta. "Yaya kasheni zeyi nashiga uku na wllhi nasan baze kyaleni ba, na kade Abba ummi kuyimun rai dan ku boye ni innalillahi wa inna ilaehi raji'un". Dago fuskanta yayi yaga shedar yatsun Fu'ad kwance. "Mamana shine yayi miki wannan dukan? Me kika mishi?" Ita dai takasa magana se su boyeta kawai take maimaitawa. Ran Abba bace ya dauko wayanshi yashiga dialing numbern Fu'ad. Be fito daga asibiti ba se gaf magrib a masallacin unguwar su yatsaya yayi sallahn magriba da isha'i kana ya karaso gida be shiga dakinshi ba ya bude kofa ya leka dakinta hango hawaye na zarya a kuncinta yasa ya karasa shiga dakin amma tayi nisa bama taji shigowarshi ba harta gama wayan seda ya Kai hannu ya karba wayan kana ta dawo hayyacinta Kwance yake kan bed dafe da kanshi dayake ji ya mai nauyi tinanin irin hukuncin dazema Muhibbah kawai yake karar wayanshi ne yasashi saurin mikewa zaune sunan Abba yagani yana yawo akan screen din wayan murya can kasa yace "Abba Barka da dare" "Ina son ganinka yanzu yanzu" yana Kai nan ya katse Kiran. Mikewa yayi yaje ya leka dakinta wayam bata nan har toilet dinta ya shiga bata ciki. Da sauri ya nufo gurin me gadi yana fada "Kai wane irine miye amfanin ka? Da ka bude musu gate suka fita, ina shi driver din?". "Me gida ba driver bane ya kaita nidai kawai naga ta bude kofan gate ta fita da sauri" wani kallo ya watsamai yayi kwafa ya wuce ya shiga mota, horn yashiga yi dasauri aka wangale mai gate yafita a guje. Tun daga nesa yake horn me gadi ya dan leko kana ya koma dasauri ya bude mai gate. parking lot be karasaba yayi parking ya fito daga motan yayi cikin gidan. A dake yashiga parlourn tana ganinshi ta mike tayi bayan ummi "Yaya kayimun rai nasan nayi kuskure ka yafemun" "ki nutsu babu abinda ze kuma miki kinji ko" kowa na tsaye cirko cirko Muhibbah kuka Aesha kuka kallon daya watsa musu ne yasasu shiga taitayinsu. "Ban gindayama sharadi akan mamana ba?, bance maka bazan lamunta duka ba?, ko wane irin laifi tama beci kamata irin wannan hukuncin ba jiba shedan yatsunka a kan kuncinta Ashe bamuda amfani da bazaka iya kawo mana kara ba" yayi maganan cikin daga murya har parlourn na amsawa. Gaba daya ran Fu'ad yakara jagulewa ze iya cewa tunda yazo duniya mahaifinshi be taba mai fada ba se yau "Kayi hakuri". Abinda ya iya cewa kenan dan daker yake magana tsabar bacin rai. "Aesha kawomun takarda da bairo" Gabanshi ne ya yanke ya fadi Jin an ambaci takada da bairo amma se ya dake. Bata fi minti biyu ba tadawo ta Mika ma Abba "bazan yarda nabar maka 'yata ba zafin zuciyar ka ze iya sawa wata rana kayimata dukan da bazan ganeta ba, karba ka rubuta mata takardan ta yanzu yanzu base anjima ba" Dasauri ya dago ya kalle Abba da rinannun idanunshi da suka canza kala tsabar tashin hankali, a zabure ta dago suka hada ido wani zazzafan hawaye ya silalomata bata taba tinanin Abba ze yanke wannan danyan hukuncin ba, itama ummi ba karamin girgiza tayi da Jin Kalmar saki da Abba ya ambata ba. Zame idonshi yayi daga nata ya runtse idon tashin hankalinshi na karuwa. "Bada kai nake magana ba? ka karba ka sawwake mata dama ai ba sonta kake ba umarnin mu kabi toh yanzu ma umarnina nake so kabi ka sallameta ka aure wacce kake so kaje can kaita nunamata zafin rai amma ba diyata ba" Kuka take sosai har ummi hawaye take tsiyayarwa, Aesha ma taya Muhibbah kukan take shi kanshi Ammar hawaye yake. Jiki a sanyaye ya karba takardan kallonshi take tana kuka me cin rai juyawan dazeyi suka hada ido
Chapter 37 · 0% Book details