Sashe 45
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *Page 46* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 "Zo nan" kamar saukan aradu haka taji muryarshi ya dira a kunnenta sum sum sum kamar mara gaskiya ta juyo ta karasa ta zauna kan kujera, cikin rawar murya tace "Ina kwana" "Lafiya kalau! Ya school har kun tashi?" "Alhamdulillah! Eh dake yau lecture daya garemu" Kai kawai ya jinjina. Ganin Aesha yasa kunya ta kara kamata tayi saurin mikewa ya maida ita zaune, ta bude baki zatayi magana suka hada ido dashi ganin kallon dayake mata yasa taja bakinta tayi shiru dole ta cigaba da karbar abincin, ita dai Aesha tayi kasa da kanta se wasa da yatsunta take jinta take kamar a kan kaya da tasanin zuwanta ta shigayi bata taba tinanin zata sameshi gida ba, taci abincin babu laifi ganin tana kauda Kai yace "Heebbah! Kin koshi ne?" Kai kawai ta gyada. Mikewa yayi da ita ya ajiyeta gefen Aesha ya juya ya tsuguna da niyyan dauke tray din Aesha ta karasa dasauri ta tattare kayan ta dauki tray din ta nufa kitchen. A gefen kujeran ya zauna ya gimtse hannunta cikin nashi "Heebbah! Ya jikin yanxu meke miki ciwo? uhmmmm!" "Kafata" tafada tana marai raice fuska" "oh sorry ze dena kinji ko?" Kai ta gyada "In dan fita tunda Aesha tazo ta kulamun dake?" Jin jina Kai tayi ta dan yi murmushi jin yadda yake tambayarta wai ya fita kamar wani yaro "Yauwa habeebtee bazan jima ba zan dawo, Aesha zata kula dake, idan kafar ta takuraki ki kirani" batace kala ba ita dai binshi kawai take da ido kamar bakon halitta zuciyarta fal mamakin shi jin abun take kamar film. Aesha ya kwala ma kira tunda ta kai tray kitchen taki fitowa gudun ta takura musu tabarsu su sarara Jin muryar Fu'ad na kwada mata Kira yasa tafito da dan sauri "Zaman me kike tun dazu a kitchen" "Babu komai" ta furta a sanyaye. "Zan fita bazan jima ba zan dawo ki dafa mata abinci, ki kula kafarta na ciwo idan zata tashi ki dan taimakamata idan kinga bazata iya ba just give me a call" "Toh Yaya seka dawo" Kai kawai ya Jinjina "Sweety I'm going bakya bukatar komai? Zan iya tafiya? Ko zakiyi wani abu na kaiki toilet? Uhmmm" runtse ido tayi wani abu yazo ya tokare zuciyarta sweety daya kirata dashi se taji kamar Mukhtar dan sunan da yafi kiranta dashi kenan duk inda taji sunan seya fadomata a rai shedan ta kora tayi murmushi "Yayana katafi abinka idan ina son wani abu ma ga sister nan, Allah yatsare yadawo da Kai lafiya" "Ameen! Me kike so na tawo miki dashi?" Seda ta dan rausayar da Kai kan tace "Kanka! idan kayimun haka kagama mun komai" ta fadeshi tana sauke boyayyiyar ajiyar zuciya dan daker ta tattaro jarumta ta iya fadan kalaman. Murmushi me sauti yayi "Indai nine bakida matsala in Sha Allah, Amma ban dani ki fada me zan tawo miki dashi" Yaji dadin kalmarta bancin Aisha na nan da sun koma gado ya nunamata zazzafar kauna, ji yayi yana bukatar Koda iya runguma da kiss ne yamata. Dan kallon Aeshan yayi yaga ma hankalinta na kan wayarta, amma duk da haka baze iya ba. Kamar bazatayi magana ba can tace "Chocolate" tafada a takai ce Jan hancinta ya danyi "Sha zumamiya kedai bakya gajiya da Shan zaki, natafi karkiyi kuka kinji take care please" ya fada in a low voice "Adawo lafiya" Peck yabata a goshi da hannunta yafice yana murmushi, Kalmar sha zumamiya daya fada yakara tina mata da mukhtar dan baya so take Shan zaki kullum complain dinshi kenan Kuma baya gajiyawa da kawomata kayan zakin duk dan tayi farin ciki hawaye ne yaso zubowa tayi saurin mai dashi tabi kofar parlourn da kallo tana murmushi jinta take kamar a wata sabuwar duniya tanaji duk duniya babu Wanda ya kaita farin ciki. Seda ta leka taga fitarshi daga gidan kan ta dawo da sauri "Oh ni matar Yaya irin wannan kauna haka har Ina ya ilahi wllhi kun tashi kaina Omo see love" "Sa ido mutum na cikin shan soyayyarshi kinzo kin katse mai Jin dadi" tafada maganan da zolaya. Dukan wasa ta kai mata "Ah ni na hanaku Jin dadinku ne duk soyayyar da kukayi a gabana zakice na hanaku kiji sharri" "Toh ai kinsan wani abun ba'ayin shi gaban yara" tafada tana dariya "Toh me ganin idona yasa kuka fasa yi zaku lalatamun tarbiyyar ido da kunne" "Kyaji dashi dai" "Kai yau Allah ya taimakeni da Yaya ya fasa bakina na shigo Ina miki tsiya kuma nasan kunji ni kawai sa'a naci" "Ai da kinzo kinyi test din gabanshi, shidai wannan ciki da kike fadarshi da dagaske ne da zuwa yanzu kin ganshi da idanunki tunda dai kinsan ciki dan duma ne, Kidena ma mun bakin fata ina fama da school kike mun zancen wani ciki yazanyi dashi" Ta karashe cikin jimami dan ita bataga ta yadda za'ayi tayi rainon ciki bare na baby tana zuwa school ba "Eyyeeee kiji sister cikin ne bakin fata ai abin farin ciki ne, nidai ina so ki haifomana beautiful baby". "Ki bari idan kikayi aure seki haifa zanma dinga tayaki raino idan kinzo school" Dariya tayi tace "Naji Yaya yace kafarki na ciwo me yasa meki, kodai tun glass din da kika taka ne be warkeba" "No! Turgudewa nayi ne" "Eyyyaaa sorry, kema tunda kinsan kashin kafarki ba kwari ba ai se kidinga bi a hankali" ta kai karshen maganan tana kyal kyala dariya "Lallaima yarinyan nan kinci abinci a kaina kashin kafar tawa ne beda kwari" dariya tayi suka shiga firan school "Ina su Ramlat" "lafiya kalau sunce gobe idan baki shigo school ba zasu zo, shine ma nake tinanin toh ina zan kaisu kince bakya so su san kinada aure kuma Umaina tasan gidanmu idan na kawota nan zata gane" "Gobe ma in Sha Allah zani" "Kema sister banga abin boyewa a aure ba aure fa shine martabar ko wane dan adam se me idan sunji kinada aure kiji mata" "Bana son sa ido ne duk ku hudun nice kadai matar aure haba kedai a barshi a banida auren idan tayi tsami a ji" Ajiye zancen sukayi suka dauko wani, se 1 tashiga kitchen tasama musu abinda zasu ci ta ajiye food flask din a dining ta dawo inda Muhibbah take. Hannunta tarike muje kiyi alwala, barni kawai zan iya tashi idan bana karfafa kaina ai sena zama gurguwa, mikewa tayi ta dan taka kafan da mamakinta se taji ba yadda tayi tinanin zataji ba taji dama dama kadan take Jin zafin dakinta suka haura sukayi alwala suka gabatar da sallahn azuhur kan suka sauko zuwa dining Aesha ce ta bi bayan Muhibbah tana kallon yadda take tafiya tana dan hardewa. "Me yasame ki haka sis duk ciwon kafan ne kike tafiya wani iri" tafada suna zama a dining "Uhmmmm" abinda ta iya fada kenan. "Ni banga Aunty mairo ba Kuma da na fito parlourn nan naga alamun tazo" "toh maybe yaya ne yace kawai ta tafi tunda yana gida" "Hakanma ze iya faruwa" Asibiti ya je ya sallama patient din dayaga sunji sauki kan ya biya gidan ummi duk 30 minutes seya kira yaji jikinta "Sannu da hutawa ummi" "yauwa ya Muhibbahn" "Lafiya kalau" "Masha Allah dan Allah ka kara kiyayewa ka rike ta da Amana nasan kana kokari ka kara" "In Sha Allah ummi Nagode, amma ita ce ma batajin dadi Aesha ta biya gaisheta shine nace ta zauna da ita kafin nakoma gidan" Murmushi tayi "Eyyyaaa Allah yabata lafiya" "Ameeen" Wajen 6 ya nufo gida seda ya tsaya wani mall yayi siyayyan kayan zaki leda biyu daya karami daya babba kan ya nufo gidan. Be gansu a parlour ba Jin kamar magana yasa ya nufa kitchen din Suna tsaye suna girki kamar ance ta juyo ta hangoshi suna hada ido ya sakarmata murmushi itama fadada murmushin nata tayi takarasa takarba ledojin hannunshi "Yaya sannu da dawowa" Se lokacin Aesha ta juyo ta kallesu da sauri tace "Sannu da zuwa" kallon daya ke mata yasa gabanta faduwa "Ba aikin kula da ita na baki ba, zaki daukota ku nufo kitchen haka mukayi dake" ya fada cikin daga murya Saurin kara matsawa tayi a tsorace tama kasa magana se kai kawai data Jin jina dayan hannunta tasa ta rike Hannunshi, tana marai raice fuska "dan Allah Yaya karka ga laifin Aesha tayi tayi na zauna nice naki nace ta bari na tayata, laifi na ne" tayi maganan a shagwabe Hannu ya kai yataba jikinta yaji babu dumi "Ya jikin ki? Kinsha magani da rana kuwa? Ya kafan? Hope bakiyi kuka ba?" Ya jeromata tambayoyin cikin kulawa Murmushi tayi "Duk ni kadai zan amsa wannan tambayoyin? Ai se bakina yayi ciwo" dariya mara sauti yayi "Ki amsa iya Wanda zaki iya ni Kuma zan cinka sauran, oya Ina jinki" "Jikina dasauki Alhamdulillah, da naji babu zazzabin shiyasa bansha magani ba, kafa Kuma kadan take mun zafin" "Kinyi kuka kenan tunda shine baki amsa ba" Dariya me sauti tayi "Ah wllhi Yaya baka cinka dai dai ba banyi kuka ba ko Aesha" tafada tana juyawa ta Kalli Aeshan Jinjina Kai tayi tana dan murmushi "Uhmmm bakiyi ba" abinda ta iya fada kenan ita dai tun dazu tana kallonsu sunyi mugun birgeta tuni suka sata a shaukin kauna, ta wani bangaren Kuma hankalinta yafi karkata ga satar kallon Fu'ad yau ga dariyar Yaya tana gani a sama kamar bashi ba tabbas mace kan sa namiji ya durkusa mata duk kudinshi duk izzar shi duk mulkinshi duk ji da kanshi yakan ajiye su ne a gefe yayinda yake tare da matarshi. "Muje Kisha magani" suka fita rike da hannun juna tabi bayan su da kallo tana murmushi ta juya tacigaba da girkinta Suna fita ya karba ledojin ya ajiye kan dining bata ankara ba se ji tayi yayi sama da ita be direta ko ina ba se tsakiyar gado ya kwanta ya manneta da jikinshi ya hade bakinsu guri daya a zafafe yashiga kissing dinta sabule bakinta tayi ta binne a kirjinshi "Je kayi wanka bari na sauka kar Aesha taji shiru" tana kai nan ta dira da sauri ta fice. Ajiyar zuciya