Sashe 42
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
lotion da humra se powder kan ta dubeshi "Dan Allah Yaya kadan jirani a waje nashirya" kallonta yayi na seconds ya dauke kai ya cigaba da danna wayarshi, ganin bashida niyyan fita ta shiga cikin hijjab tasa rigan ta zare hijjab din ta yafa gyalen abayan. "Muje ko?" Tafada tana kallonshi Maida wayan aljihu yayi ya sabeta har parlour yaja kujera ya ajiyeta. Kallonsu mairo tayi ta danyi murmushi ta shige dakinta da take zama idan tazo gidan. Serving dinta yayi kan ya zuba nashi ya zauna yafara ci hankali kwance, dan zaro ido tayi tana kallonshi girkin yamata dadi a ranta take mamakin ya akayi ya iya girki. Suna kammalawa ta mika mai hannu yayi kamar be ganta ba ya lura harda shagwaba a lamarinta "Yaya ka karashe ladanka ka maidani parlour ina so na mike kan 3 seater please". "Bari in zo inkara yi miki dressing ciwon" zaro ido tayi tina azabar datasha jiya wajen dressing din "Aa Yaya kabarshi kawai dasauki fa yama kusa warkewa" "Ni dai banga saukin ba tunda ko iya taka kafar bakya yi gara a kara yin dressing din namiki allura muga zuwa anjima ko zata takun miki" Saurin mikewa tayi tana dafe dining table din. "Rikeni mu karasa parlour" "bari na daukeki kar ki wahalar mun da kanki" "Aa bari na daure na dinga takawa kawai". Riketa yayi yana murmushi dama sarai yasan shagwaba ne, ita ko se cije lips take har suka isa parlourn. "Bari inje asibiti patient na jirana" "A dawo lafiya Allah yatsare". "Ameen" ya fada kana yamata peck a goshi ya fice. Lumshe ido tayi tana tino moment dinsu na jiya seta tsinci kanta da sakin murmushi me fadi. Gaisawa sukayi da mairo tace mata ta zuba breakfast tadawo tanaci suna fira har bacci ya kwasheta. Se 1 ta tashi ta haura up stairs dakinta ta nufa ta dauro alwala ta gabatar da sallahn azuhur tayi addu'a kan ta mike ta sauko parlour. Zamanta babu wuya taji ana danna door bell tana budewa ta fadada murmushin ta ganin Aesha, Aunty Suhailat harda Ummi. Hanya ta basu suka shigo cike da jin dadi tayi hugging din ummi "Sannu da zuwa Ummina" "Yauwa diyar kirki, ya jikin" "Naji sauki" Tabe Baki Aesha tayi tana neman guri ta zauna "Ummi kin ki zuwa gidan nan se yau" "Toh Muhibbah ai komai seda dalili yanzu da dalilin yazo ba gashi na zo ba" Murmushi kawai tayi "Aesha tadawo school take cemun bakida lafiya yau ko school baki iya zuwa ba, zasu tawo da suhaila nace muje naga ya jikin naki" "Allah sarki Ummina sannu da kokari, naji sauki glass cup ne ya subucemun ya fashe kawai na takashi bansaniba, amma dasauki" "Sannu Allah ya tsare gaba" "Ameen" tafada tana mikewa taje takawo musu ruwa da abin tabawa. "Zo Zahra, bakiga Aunty bane" washe baki tayi harda zillo ta rarrafa gurinta tasa hannu ta dauketa. "Aunty Suhailat ki bani yarinyar nan please" dariya tayi "Rufamun asiri da rashin tausayi na yayi yawa a situation din dakike ciki na baki zahra da kanki zakiji ko da ita, ki bari idan kika haihu dai sena baki ki hada biyu" Kallon Aesha tayi ta watsamata harara "Kai Aunty Suhailat kina biye ma wannan yarinyar, wllhi banida komai kinjima na rantse kawai maganarta ne". Tunda tayi rantsuwa ta yarda ita kanta ummi ta yarda tunda harda rantsuwarta fatan ta Allah yakawo me albarka A dan kunyace ta kalla gefen da Ummi take tana magana da mairo amma duk da haka tasan tana jinsu shiyasa taja bakinta tayi shiru. "Aesha ya school, ina su Umaina?" "Lafiya kalau, su Umaina sunce na gaisheki" "Ina amsawa". Se kusa da la'asar suka tafi harda mairo setaji gidan babu dadi. Shiru tayi se tinanin mijinta ya fado mata kodai ya tafi gurin budurwar tashi ce, shedan ta kora ta mike tayi sallah ta shiga kitchen. Bata jira dawowanshi ba tanayin magrib ta shige daki ta kulle ta kwanta se sake sake take isha'i tayi bata jima da kwanciya ba bacci ya saceta. ********* Girke girke sukeyi ita da Rumaisa sunyi abinci yakai kala biyar ga juice kala 3 Wanka tashige tabar ma Rumaisa sauran aikin ganin an fara Kiran magrib Gaban mirror ta tsaya ta kure basirarta ta caba kwalliya ta kafa dauri tashafa turaruka ta nufo parlour. Kusa da Ammi ta zauna "Sannu da hutawa Ammi" murmushi tayi "Yauwa Zainab duk wannan wankan na Dr ne" tafada da zolaya. Kulle fuska tayi da tafin hannunta tana dariya Karasowa inda suke Rumaisa tayi tasa guda "Ya ilahi ke kinganki kuwa Aunty zeeee, Amarya a gidan Dr wllhi kin hadu komin abin Dr yau yaga wannan wankan naki se ya rude" "Dagaske 'yar kanwata, komai yayi?" "Allah kuwa Aunty kin hadu saura haduwarki da Allah" tafada tana dariya suma duk sukasa dariya Har ranshi be son zuwa sedai ya riga yamata alkawari baze iya sabawa ba a rayuwarshi yana matukar girmama alkawari. Bayan ya fito daga sallan magrib ya kara duba Address din data turamishi kan ya dauki hanya seda ya tsaya yayi isha'i a masallacin unguwar kafin yakara a bakin gate din gidan yayi parking ya danna numbernta ringing biyu ta daga. Alama tama Rumaisa tayi shiru, kashe murya tayi tace "Hello Dr" "ina waje" abinda yafada kenan ya ajiye wayan. Kiran me gadi tayi tasa ya wangale mai gate ya danno motan ciki. Gyarawa takarayi tafito tana taku daya bayan daya sanye take cikin tsadadden leshi anyi mai dinkin straight gown yakama jikinta sosai ta yafa karamin gyale medium size white colour takalmin kafarta ma white. Yana jingine jikin motarshi ya harde hannunshi a kirji tunda ya kalle inda take tawowa ya dauke kai "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" "Wa alaekumussalamu warahmatullah" ya amsa can kasan makoshi. "Sannu da hanya my d" "Yauwa, kina lafiya?" "Lafiya kalau, fatan kaima haka" shiru yayi be Kuma magana ba, tunda ta karaso kallo daya yamata ya dauke kai. Ganin alamun ya gaji da magana yasa ta kama bakinta gudun tayi laifi "Mukarasa ciki" gaba tayi yabi bayanta se wani canza salon tafiya take shiko kanshi na kasa ko sau daya be dago ya kalleta ba. A kan carpet ya zauna yashiga gaishar da Ammi cikin girmamawa, amsawa tayi cikin sakin fuska, itama Rumaisa ta gaisheshi ya amsa. "Zainab kaishi yaci abinci" toh kawai tace ta mike Mikewa yayi ya ajiyema Ammi kudi masu yawa daker ta amsa tana ta samishi albarka da addu'ar gamawa da duniya da iyayenshi lafiya, addu'o'inta ba karamin dadi suka mai ba. Gidan babba ne ya hadu sunada arziki dai dai gwargwado sunada son jama'a da girmama na gaba dattakun mahaifiyar su ya birgeshi da ace yanada burin zama da mata biyu toh da tabbas Zainab ce zata zo a ta biyu amma gaskiya baya ra'ayin zama da mata biyu sedai tayi hakuri. Shi shigan da tayi bega aibinshi ba yasan tasa ne duk dan ta birgeshi Kuma acikin gida ne be ga aibin haka ba dan ko randa suka fara haduwa da shigan kamala yaganta. Parlourn baki ta mai masauki ta zauna suka kara gaisawa kan tajere mai abinci da abinsha dasu fruits ta barshi yaci ta koma gurinsu Ammi Ganin Kiranshi yasa ta mike ta nufi parlourn yadda ta ajiye abincin haka ta dawo ta sameshi "Dr naga bakaci komai ba ko duk babu abinda yama ne kafada me kake so inje insama ma" "No karki damu kinga babu dadi naje gida banci abincin madam ba bazata ji dadi ba" saurin kallonshi tayi dagaske kenan yanada mata. Danne abinda taji yana tasomata tayi ta kakalo murmushi "Kazo har gidan mu ace ko ruwa baka sha ba, dan Allah kaci ko babu yawa please". Ganin ta takura yasha ruwa da kunun aya. Seda ya numfasa kan yafara magana "Kamar yadda na fadamiki inada mata, Kuma a hakikanin gaskiya banaji zan iya auren mata biyu, kiyi hakuri ki nemi wani zan tayaki addu'a Allah yabaki nagari" Tunda yafara maganan take kuka seda taja majinar kuka kafin tace "Naji na amince zanje ata biyun Kuma nama alkawari zan zauna dakai da matarka lafiya in Sha Allah, kai wllhi ko matanka uku ne ni nayarda zanje ata hudu" tausayi ta bashi yayi shiru kan yace "Zanyi tinani" ya mike ya fice, da sassarfa ta karasa wajen da yayi parking motan "Zuwa yaushe zan jiraka?" "Duk abinda na yanke zan kiraki na sanar dake" yana Kai nan ya shige mota ya fice daga gidan. Seda ta dai daita nutsuwarta kan tashiga ciki. Gudu yake sosai hankalinshi na kan Muhibbah ita kadai a gida ga dare yayi. Be sameta parlour ba ya leka kitchen Bata ciki kafin ya haura sama handle din kofar ya murda ya shiga dakinta kwance ya sameta tana baccinta hawaye duk sun bushe a fuskanta daukarta yayi ya nufo dakinshi. A kan bed ya kwantar da ita ya sauya kayanshi zuwa na bacci ya kashe hasken dakin ya haura gadon ya ja blanket ya lullubesu, janyota jikinshi yayi ya dora kanta kan kirjinshi taja dogon ajiyar zuciya tana kare gyara kwanciyarta a kan chest dinshi. Ya kusa makara sauri sauri yayi alwala ya nufa masallaci. A hankali take bude ido tashi zaune tayi tana karema dakin kallo ganin ba dakinta bane yasata shiga zare ido tana tambayar ya akayi tazo dakinshi ita dai tasan a dakinta tayi bacci ganin babu me bata amsa ta mike ta sulale tayi dakinta. Wanka tayi ta hado da alwala tazo ta tada sallahn asuba bata koma bacci ba ta shiga kitchen ta hada breakfast, ta shirya dining kan ta koma daki takarasa shirinta Bata tsaya jiranshi ba tayi breakfast ta mike takara hade rai taje tayi mai sallama yabata peck a goshi ta fito tana murmushi duk da har lokacin haushin shi take ji dan tasan jiya gurin budurwarshi yaje fira. Courses biyu sukayi suka fito Koda malam mukhtasir ya gansu ko kala bece musu ba Koda su Aesha suka gaishe shi sama sama ya amsa Muhibbah ko kallon arziki be samu daga gareta ba baki ta tabe a ranta tace tafi nono fari a dadina Allah yasa karya sake mata magana har tabar school din. Harta gama girki ta jere a dining tayi dinner shiru be dawo ba ta cika fam ta wuce daki ta