Sashe 24
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga Allah" seta Kuma fashewa da kuka. Lallashinta yayi sannan tayi shiru. "Iyye kinsan yaran zamanin nan ne se a hankali shiyasa kawai a kyaleta tunda tace bata sonshi". Kuka ta fasa "Au ni har in bada umarni a ketare saboda ban isa ba, munaji Muna gani zamu zuba ido su biyu su lalata zuminci baka ganin dan sun hadu inuwa daya se kallon banza auren ne kawai zesa su dena wannan iya shegen idan suka gaji dole su sauka su zauna lafiya tunda hausawa sunce tsugunne ba zaune ba, Amma shikenan tunda ban isaba kuje kuyi abinda kuke so". Ta karasa maganan tana karama kukanta sauti. Hannunta ya riko yana Bata hakuri "Kiyi hakuri bazamu taba ketare ma umarninki ba har abada, in Sha Allah aure kamar an yishi". Daker ya lallabata ta sauko sukayi fira ganin har la'asar tayi kuma ba kwana zeyi ba yasa ya ajiyemata kudi tanata samai albarka ya wuce............ *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 30* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Tana zaune ta zabga tagumi tana ta sake sake ji take garin yamata zafi duk wani tinani da zatayi tayi shi amma har yanzu bata samu mafita ba, Abba data ke ganin shine hope dinta shima hakuri kawai yake bata, Mahaifinta batada iKon da zata tun kareshi akan auren dan baze saurareta ba sedai ma ya hada mata da duka, haka ma mahaifiyar ta Koda ta tunkareta itama yanzu babu sauki da tana rarrashinta yanzu Kam ma fada take mata, ga farin cikin rayuwarta Shima ya juya mata baya idan zata kirashi sau dari bazeyi picking ba ko message dubu zata turamai baya budewa bare yamata reply, abubuwa sun hadu sun mata yawa duniya ta mata zafi tarasa inda zatasa rayuwarta taji sanyi. A firgice ta dago kanta Jin hajiya hawwaye nata kiranta, murmushi ta kakalo "Hajiya kece" "wane irin tinani kike haka tun dazu nake tsaye ina magana amma bakiji ni ba" ta karashe maganan tana janyo karamin center table din dake tsakiyar parlourn ta ajiye wani bowl a Kai. "Babu komai hajiya kawai kaina ne ke dan yimun ciwo". "Toh Muhibbah ba dole kanki ya miki ciwo ba kin daurama kanki abinda yafi karfinki, wannan tinani dakike ai yafi karfin shekarunki, ki wuni kina kuka ki ta kura kanki ai ko abinda yafi ciwon Kai ne zakiyi". Aesha da suka shigo parlourn tare da zahrah bayan sun taya hajiya hawwaye hada magani tace "Wllhi hajiya da Muhibbah najin shawara da duk haka bata faruba na fadamata kuka baya maganin komai yawan tinani yafi saurin illata rayuwar dan Adam amma bataji". "Aiko taurin Kai ba naki bane kina mace saboda gidan wani zaki wannan ki bar ma namiji shine zeyi duk abinda yaga dama Kuma ya kwana lafiya". Nan tashiga yimata nasiha tareda bata shawarwari da dabarun zaman gidan miji, can Kuma ta koma lallashinta "kiyi hakuri ki runguma kaddara kinga taro ake karki yarda ki shiga mutane a haka har su fahimta bakya farin ciki da auren ki runguma kaddararki babu Wanda yayi abinda Allah beyi ba komai kikaga yafaru da bawa jarrabawa ne kiyi kokari ki cinye jarabawar ki babu yadda za'ayi wani aura matar wani haka zalika babu yadda za'ayi wata ta aure mijin wata kicire damuwa a ranki ki runguma mijinki hannu bi biyu kinji?" Ta Kai karshen maganan tana janyo bowl din dake kan table din. Ita dai muhibbah batace komai ba se hawaye dake zarya a kumatunta, daker ta iya tsaidasu ta tashi taje toilet ta wanke fuska ta dawo ta zauna tana ajiyar numfashi. Bowl din dafaffiyar Kazan maganin ta Mika mata "Ungo" karba tayi ta tsurama bowl din ido a ranta take raya badai ita zataci wannan abun ba gwanin kyama, bata gama tinanin ba taji tace "Maza kick mana kar yayi sanyi sosai". Hannu tasa ta fara ci tana turashi daker tanajin kamar zatayi amai, ture kazar tayi tana yatsina fuska kamar zatayi kuka. "Ya kika ajiye?" "Hajiya na koshi ne" "oya karba maza maza ki cishi tunda sauran duminshi kafin ya karasa hucewa" haka ta ciga da cin Kazan tana hawaye seda taci sosai Jin tafara kakarin amai yasa hajiya hawwaye dauke kwanan tana mika mata gorar ruwa, karba tayi tasha kadan ta ajiye. Mikama su Zahra sauran kazar tayi tace "Ku dauka Kuma kuci" Zahrah tayi saurin girgiza Kai "Aa nikam na koshi" Aesha ma tace "Ah hajiya a ajiye mata an jima sena dumama mata ta karasa cinyewa" wani uban harara ta watsamata tana saurin cewar "Wllhi bazan ciba kuma se kuncishi ashe babu dadi ni komai aka dauka abani na durama cikina" tafada tana tura musu Kazan. Dariya hajiya hawwaye tayi tace "Aesha ku dauka kuci babu abinda zatai muku". Aesha na kaiwa baki "Ashe akwai bauri" "Da ba gani kuke dadi bane kuke zuga hajiya tasa na ci ba, Kuma fa magungunan nan basuda wani fa'ida sema cutarwa da sukeyi bawani bincike da akayi akansu bare a gane sunada sight effect ko aa" dakuwa hajiya tamata "kinci gidanku tun shekaru nawa ana amfani dasu basu cutar da kowa ba se ke, ba'a so mutum yasiya magani gurin masu Saida magani barkatai ki samu shararriya Wanda maganin ta yake da inganci ta hadamiki magani babu wani cutarwa da sukeyi". Suna zaune a bedroom Jafar yace "Wai ni tunda nazo banga amarya ba, ko tun yanzu an fara boye mana ita ne mutumina" twsssss yaja tsaki "Nifa matsala ta da Kai kenan se ana maganan arziki seka nemi batama mutane Rai" dariya suka sheke dashi "Tun dazu muna fira baka kulamu ba se yanzu da gaji mun soso ma inda yake maka kaikayi" "Kyaleshi Jafar yana so yana kaiwa kasuwa, ya fito ya fallasa sirin zuciyarshi amma se zagaye zagaye yakeyi" Suhail yakarasa maganar yana dariya. Banza yayi musu saboda ya fahimta neman magana suke, karshe ma ya tashi yabar dakin. Gida yafara cika mutanen Kano an hallara Ummi ta karasa inda mummy ke zaune cikin room dinta tareda 'yan uwanta dasuka fara zuwa daf da ita takarasa tayi mata magana a hankali kamar me rada "Kinga iyye ta iso, ki kira hajiya Sa'adatu kice Muhibbah ta dawo gida gyaran ya isa haka, kar asamu matsala tun isowarsu take tambayan ina muhibbah da Aesha nace sunje gidan kawarki amma sun kusa dawowa". "Hakane wllhi na sha'afa bari yanzu zan kira in yaso ko bala driver ne sena tura ya dauko su". Wayarta ta dauka ta kira hajiya Sa'adatu, ta shaidamata babu jimawa zasu dawo in Sha Allah, nan Mummy tashiga yimata godiya da kulawar data nuna ga diyarta. Karfe biyu na rana sega su sun dawo harda umma, Muhibbah fuskanta daure da nikab saboda hajiya hawwaye tace karta dinga fita idan fitan ta kama dole to ta dinga rufe fuskanta, Su Fu'ad na Shirin fita su Kuma suna shigowa gidan kallo daya ya musu ya dauke kai ya gaeda umma ta amsa cikin kulawa, Suma su suhail suka shiga gaisheta ta amsa da sakin fuska, seda suka gama gaishe da umma zahrah da Aesha suka gaishe su banda Muhibbah da sauri sauri ta wuce su. Seda umma suka gaisa dasu mummy tayi musu godiya kana ta mike tayi musu sallama Suma sunata godiya suna Jin jina kirkinta, itama zahrah gidan aka barta tace bazata bi umma ba se sunje yola sun dawo. Iyye sukaje suka gaishar tafara tsokanar Muhibbah, ita Kam bata ce komai ba se Aesha data zake tana shigarma Muhibbah iyye tace "Oh an kashe bakin mara kunya amma da yanzu wayaga Fatsuma anan da tuni ta ishemu da surutu kamar an kunne radio" haushi ne ya isheta ta mike zata bar parlourn kenan su Fu'ad suka kutso Kai kallon kallo suka shigayi kamar yau suka fara ganin juna rabawa tayi ta gefenshi ta wuce Jafar yace "se anyi magana mutum yace ba haka ba" be kulasu ba, iyye tace "kyalesu jafaru saji dashi dai duk su gama Shan kamshin su da iyayinsu aure dai babu fashi karkashin inuwa daya zasu dawo idan sun so su yayyanki naman junansu karshen kiyayya" Jin kalamanta sun isheshi yasa shi tashi yabar parlourn, Aesha tace "Kai tsohuwa kema fa kin iya surutun ke muka gado nida Muhibbah" dariya akasa, ta dauki carbi ta wurgamata ta tashi a guje, Ummi ta shigo ta kirasu su ita da zahrah su Kai flour gidan hajiya jummai me dubulan an Kai buhu daya anyi chin chin wannan na dubulan ne, hijjab suka zira driver ya Kai su, suna shigowa Fu'ad yace "Aesha idan kin shiga kice Muhibbah ta sameni parlourn Baki" da toh ta amsa tana wucewa. Tana shiga dakin tace "Muhibbah ya Fu'ad yace ki sameshi parlourn baki yanzu" da mamaki take bin Aesha da kallo "wane ya Fu'ad din?" "Ya Fu'ad nawa muke dashi, nima dai nayi mamaki nasan dai ba wani laifi mukayi ba, amma kije ki jiyo mana meke faruwa" Gyara kwanciyarta tayi, au kwanciya kika gyara ko hmmm nidai nasan na isar da sa..." Ringing din wayanta ya katseta Adiriri ce ta dauka wayan "Hello" "wane sako na baki?" Ya jefomata tambayar. "Dama dana shigo tana toilet ne se yanzu ta fito tace gata nan zuwa" kit ya