← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 69

Sashe 17

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t A bakin gado suhailat ta zaunar da ita, ta nufa bathroom ta hadamata ruwa tace "zaki iya shiga bathroom din ko na taimaka miki?" Tayi maganar cikin sigar tambaya. Girgiza Kai tayi tace "Aa Aunty suhailat zan iya" ta karashe maganan tana mikewa. Cikin sanyin jiki ta karasa toilet din, suna ganin shiganta suka fito daga bedroom din. A gaban mirror ta tsaya tana shafa body lotion cikin sanyin jiki, ta dauko humran da umman mukhtar ta bata ta shafe jikinta dashi batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba saboda tinawa da dramar ta da me gadin gidansu mukhtar, can Kuma wasu siraran hawayen tausayin kanta suka zubo mata. Shiryawa tayi cikin doguwar riga dinkin captain gaban rigan yaji stones, harta bude Dan kwallin zata daura kome ta tina kuma ta wurgar da dan kwalin kasa taja dan karamin tsaki ta nufa kan bed ta kwanta, ta shiga duniyar tinani. Zaune yake ya rike haba ya kurama TV ido amma kwakwata bema San meke wakana a cikin TV din ba se magana yake da zuciyarshi. Mukhtar! Mukhtar!! Mukhtar!!! Shiru babu amsa. Karasowa tayi ta tabashi, firgigif ya dawo daga duniyar tinanin daya tafi. "Mukhtar lafiya kake kuwa?" Cewar umma. "Lafiya kalau umma". "Aa ba batun lafiya kalau, kwanan nan ina karantarka ko abincin kirki bakaci sedai kadan yafuta Shima na ganin ido ne, kafadamun abinda ke damunka" takarasa maganan tana zama kusa dashi. "Umma lafiya kalau nake kawai bangama war warewa bane, amma in Sha Allah soon zan dawo normal". Muskutawa tayi tare da dafa kafadarshi tace "Ban yardaba, nasanka gaba da baya ina sane da duk yanayinka, nifa mahaifiyarka ce bakada kamata a duk fadin duniyar nan idan baka fadamun damuwarka ba wazaka fadamawa". Gyara zamanshi yayi ya riko hannun umma kana yace "umma hakikanin gaskiya ina cikin wani hali amma nafi damuwa da halin da Muhibbah take ciki". Yakarasa maganar a raunane. "Wani abun ne yasamu Muhibbahn?". "Batada lafiya, nakira wayan muhibbahn naji ya suka koma gida, se Aisha tayi picking take fadamun Muhibbah na asibiti, Kuma dalilina ne yakaita ga kwanciya gadon asibitin". Kallon ban fahimta ba tabishi dashi kafin tayi magana ya dora dacewa "Iyayenta sun rabani da ita sunce nayi nesa da ita domin anyimata baiko da yayanta wato cousin brother dinta, wannan dalilin shi ya kaini gadon asibiti, nayi iya kokari na domin kar mummunan labarin nan ya risketa amma bayan sun bar nan gidan tasamu labarin wajen mahaefanta shine itama damuwa ya kwantar da ita rashin lafiya". Ya karasa maganan yana dauke wasu siraran hawaye daga idanunshi. Bakaramin sanyin jiki labarin yasa umma ba, girgiza Kai tayi ta dauke hawayen dasuka zubomata a fili ta furta "Tabbas SO ba karya bane". Zahrah da tun dazu tashigo tana sauraron bayanin da mukhtar kema umma, ta karaso ta rike hannun mukhtar tasa kuka tana fadin "innalillahi wa inna ilaehi raji'un! Ya mukhtar hakika duk inda Muhibbah take tana cikin wani hali, ni shedace akan son da take maka banaji ko kanta tanama irin wannan son". Umma tayi karfin halin cewa "ka kira Muhibbahn kaji a ina take?". "Aa" yafada a takaice. "To me kake jira, Maza kirata Muji wane hali take ciki, kafa ce har oxygen aka samata". "Munyi waya da Aesha tace jikin dasauki dan harma tadawo gida". "Maza tashi ka shirya mutafi gidan nasu na gano jikinta". "Iyayenta sun ce nayi nesa da ita Karna kara zuwa inda take, dan Allah umma kibar batun zuwa gidan, ko a waya ne seki mata sannu". Hannu ta daga mai "Nagama magana ba amincewarka nake nema ba, umarni nake baka" ta karasa maganan tana mikewa ta wuce tabarshi zaune, Zahra ta mara mata baya. Yafi minti 10 zaune ganin zaman baze fissheshi ba ya mike ya haura sama. Aesha ce ta shigo ta taba ta, tayi firgigif ta tashi zaune ta kakalo murmushi. Aesha tace "Sister wai har yaushe zaki dena wannan tinanin, babu kyau yawan tinani ze iya haifar miki wata matsalar, da zarar tinanin yazo miki kiyi kokari ki yakiceshi sannan kidena zaman kadaici ki dinga kokarin fitowa cikin mutane Koda bazakiyi maganaba, domin zama guri daya shike haifar da tinani marasa amfani". "Ashe abinda ya mukhy ke kokarin boyemun kenan, hakika ya mukhtar masoyin gaskiya ne yafi son farin ciki na akan nashi, ya boyemun ne domin kar inshiga damuwa duk da yasan dole zanji amma be yarda nafara Jin shi daga bakinshi ba, amma nayi mamaki da tun bayan barowarmu gidansu be nemeni ba me hakan yake nufi kodae ya hakura dani ne?" Takarasa maganan cikin sigar tambaya. Ajiyar zuciya tasauke "Ya Mukhtar yana tare dake, bayan mun dawo ya kira wayanki na sanar dashi kina asibiti abinda ya hanashi zuwa dubaki ya sanar dani Daddy da Abba sun ce ya nisan ce ki, ya fita daga rayuwarki domin ke din matar wani ce anyi miki baiko da ya Fu'ad, Kuma bayason wani abu mara dadi ya sameki damin zuwanshi ze iya zama matsala a gareku daga ke har shi wannan dalilin yasa bezo ba Kuma kusan duk bayan 1 hour seya kirani yaji ya jikinki ko dazuma ya kira wayanki nake fadamishi har kin dawo gida". Kuka ne ya kwacemata kafadar Aisha ta kwanto "sister meyasa su daddy basa son farin ciki na, meyasa suka zabi su faranta ransu fiye da nawa, innalillahi wa inna ilaehi raji'un". Bubbuga bayanta tashigayi alamar rarrashi "Sorry dear, yanzu duk ba wannan ba kitashi ki dauro alwala lokacin sallahn azuhur yayi ki fadama ubangiji damuwarki, shi yace mu rokeshi ze amsa mana, ki rokeshi zabin Mafi alkhaeri, sannan kiyi kokari ki dena yawan tinanin nan domin damuwa na saurin illata mutum". Kwallar idonta ta share "thank you, I will try". Toilet ta nufa ta dauro alwala, itama muhibbah ta dauro nata suka tada sallah, tajima tana addu'o'i kafin ta mike ta zare hijjab din jikinta ta tsaya gaban mirror ta gyara fuskan ta tayi spraying body spray a jikinta ta dauki dan kwalinta ta daura, ta riko hannun Aisha suka nufo parlourn. A dining suka samu gaba Daya a halin gidan suna lunching cikin farin ciki, ta gaeshesu suka shiga tambayarta jiki ta amsa da Alhamdulillah. Kujera taja ta zauna tasa abinci gaba tana jujjuya cokalin takasa kaiwa baki, a jikinta taji alamun ana kallonta ta dago Kai idanunsu suka sarkafe ana juna, sun jima suna kallon juna kafin ta lumshe idonta ta mike da niyan dauko ruwa a fridge taji ana danna door bell. Karasawa tayi ta bude kofan ai setayi mutuwar tsaye tama kasa magana se kura musu idanu datayi kamar bakin halittu. Umma ce tayi kokarin Kiran sunanta "Muhibbah!". Murmushin karfin hali tayi "Umma kece da kanki". "Ah nice Muhibbah ai zama be ganni ba diyata babu lafiya, hankalina baze kwanta ba se nazo naganki". Me gadi yace "Hajiya tacemun gurinki zata zo shine nace ba'a barin shiga idan batare da ansan da zuwanta ba amma da naga babba ce shine nace bari na rakota nayi miki bayani". "Okay Allah ya ceceka da kayi yunkurin hanata shigowa da ka rasa aikinka, matsayin mahaifiya take a gareni dan haka duk sanda tazo kabarta tashigo direct". "Toh hajiya". Iso ta musu har cikin parlourn ta nunamusu guri suka zauna Ta fadama su mummy akwai baki, kowa ya nufo parlourn, ita Kuma ta nufi kitchen nemo musu abin tabawa. Abinci dasu snacks takawo musu ta ajiye, kafin ta risina tashiga gaida umma "Umma ina wuni". "Lafiya kalau diyata, ya jikin naki?". "Jiki yayi sauki Alhamdulillah". "Allah yakara sauki" "Ameen ummana". "Aunty zahrah ina wuni?" "Lafiya kalau, ya karfin jiki". "Naji sauki". Mummy na karasowa parlourn tace "hajiya Sa'adatu! Kece a gidan namu" "Hajiya Hafsat! Dama nan ne gidanki". Da mamaki take kallonsu "Mummy dama kinsan umma ne? Umma kema dama kinsan Mummy ne?". "Kwarai kuwa nasan hajiya Sa'adatu sosaema tun shekaru da dama, Muna business tare da ita sedai online business mukeyi bata taba zuwa gidana ba Nima haka amma mukan hadu wajen taro inda mukeyi duk karshen month tare da manyan 'yan kasuwa mata". Jin jina Kai umma tayi "Wannan gaskiya ne dalilin business muka San juna kullum Muna wakar zamu ziyarci juna amma Allah be nufa ba". Mummy ta juyo gurin Muhibbah "ke Kam ina kika san hajiya Sa'adatu?". Shiru ta danyi kafin ta fisgo magana "Umman ya mukhtar ce". "Wane mukhtar din?" Kasa tayi da Kai tace "Ya Mukhtar dina". Gaban mummy ne ya fadi gaba daya kunyan umman mukhtar yakamata a ranta tace ana wata ga wata, daker ta iya samun guri ta zauna tana tinanin ta inda zata fara. Wani kallo Fu'ad ya watsamata Jin tace Mukhtar dinta, yatsina fuska tayi ta tabe Baki ta wuce tashiga kitchen dauko cups.................. *Kwana biyu kunjini shiru ku gafarceni, sister tace ta haehu tasamu baby girl (Unaesah) say a prayer to my adorable daughter please and ni nake yimata aeki shiyasa nayi busy kuyi hkr please* *Aminiyar ango ***Aminiyar ango * *Aminiyar ango ceeeeee *[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 25* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And
Chapter 17 · 0% Book details