Sashe 55
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sosai din nan fa" ta fada a shagwabe "Toh kizo ki sameni yanzu ina jiranki" Zaro ido tayi "Kai gidan mummy fa muke" "na sani kizo maza ina jiranki" Turo baki tayi "Toh ya Suhail fa" "Shima yasan yanzu da dah ba daya bane yasan ina da mata shiyasa ma ya barmun dakin ni kadai" "Aa nikam idan su mummy suka ganni fa to ina zan ce musu zanje" "Gurin mijinki, nabaki 5 minutes idan baki zo ba wllhi wllhi ni zan zo da kaina ai kinji abinda nafada ko?" "Uhmmm" abinda tace kenan ta ajiye wayan Mikewa tayi ta dauki hijjab dinta har kasa tasa ta fice dan tasan ba karamin aikinshi bane yazo har dakinta yadda ya fada. Tana tafiya tana waige kamar mara gaskiya ta bi ta kofar kitchen ta isa bangaren su da sauri ta karasa shiga dakin kamar an korota har tana bugan kirjinshi dan shima har ya mike yana shirin zuwa ya sameta "Ji yadda duk kika firgice kina zaro ido kamar wacce aka Koro" turo baki tayi ta karasa ta zauna gefen bed Karasawa yayi ya zare hijjab din jikinta yayi wurgi dashi ya dagata cilak ya kwantar da ita tsakiyar gadon ya mata runfa "Wai fushi kike" "Dan Allah Yaya ka bari kar muyi abin kunya gidan mutan..." Be bari ta karasa ba ya hade bakinsu yajima yana bata hurt kisses kan ya zare bakinshi ya kai saitin kunnenta "Waye yace miki gidan mutane muke? Nan dinma ai gidan mu ne kuma babu wanda besan mu ma'aurata bane, su mummy da dare nan babu abinda ze kawo su part din nan" Yana maganan yana yawo da hannunshi a jikinta Duk ya kashe mata jiki dole yasa ta biye mai suka sha bidirin su seda suka samu nutsuwa kan ya dauketa suka shiga toilet sukayi wanka suka kwanta rungume da juna tanata rigimar yabarta ta tafi dakinta yaki a haka har bacci ya dauke su. Koda yatashi da asuba toilet ya shiga yayi alwala har ze tasheta ya fasa dan yasan rigima zata tsiro kan yabari ta kwana tare dashi a gidan daddy A hankali ta bude idanu Jin har an sallame sallah a masallaci yasa ta diro daga gadon da sauri ta dauki hijjab dinta ta zira ta fice daga dakin cikin sanda ta biyo ta kofar kitchen seda ta leka parlourn taga babu kowa kan ta karasa dakin ta da sassarfa. Gidan Aunty Asma'u sukayi ma tsinke ta tura kofar parlourn bakinta dauke da sallama su yusrah da Abdulrahman da Muhsin suka rugo da gudu suka rungumeta suna mata Oyoyo kan suka karasa suka rungume Fu'ad ya daga su daya bayan daya yana direwa guri suka samu suka zauna, Jin hayaniyar yaran yasa ta nufo parlourn da sauri ganin su Muhibbah yasa ta fadada murmushin ta cike da farin ciki ta kara so ta zauna "Yaya wannan bazata haka saukar yaushe?" "Babu ruwana laifin rigimamiyar yarinyan nan ce Mummy zata kiraki ta hanata" Shagwabe fuska tayi "Nicema rigimamiyan?" Gira ya dage mata batareda yayi magana ba, ita dai Asma'u se murmushi take dan bakaramin birgeta sukayi ba kamar basu ne suke kin junan su ba a kasan ranta ta furta Alhamdulillah "Aunty hadamu yake so yayi amma ni surprising dinki nake so nayi ne shiyasa nace kar mummy ta fada miki, Kuma fa jiya ne muka zo" "Ah ai kam kunyi surprising din nawa" ta fada tana mikewa abin tabawa ta cika musu gabansu dashi kan ta Kai zaune "Yaya ka biye ma yarinyan nan kuka tawo ni na dauka seta haihu ai ita da garin nan" Shidai bece komai ba yana jinsu sedai ya danyi murmushi "Kai Aunty wane irin haihuwa tun yanzu school fa nake gaskiya ba yanzu ba tukunna" "Eyyeeee mu duk da muka haihu muna karatun me yasa me mu? Ai yayan najinki gaki gashi nan" "Kudai fara Shirin zuwa sunan Aunty Suhailat" "Toh Allah ya sauketa lafiya" Sun dan jima suna fira kan ta kirata suka shiga daki ta cikamata leda da magunguna ta kara fadamata wasu sirrikan hade da nasihohi a kunyace ta karba tamata godiya kan sukayi sallama Fu'ad ya ajiyemata kudi tanata godiya kan suka fice Gidan su summy suka biya tanata mata tsiyan taki kiransu suje suna yola bata jima sosai ba saboda Fu'ad na jiranta waje se summy ce tace zata zo gobe sukara gaisawa Gidan su Rufaida ya kaita nan ma tsiyan take mata kamar sun hada baki da summy bata jima ba ta wuce har gidan umman mukhtar ya kaita taji dadin ganinta sosai sun sha fira da zahrah kan ta musu sallama ta ajiye ma umma tsarabarta ta wuce umma nata godiya ShopRite suka nufa sukayi siyayya kan suka siya ice cream suka zauna suka sha sukayi hotuna. Se yamma likis suka shiga gida. Daker ya bari su kayi kwana 5 da kuka ta baro gidan babu rokon da batayi mai ya tafi yabar ta ba yace inaa idan ta bata mai rai ma se tayi 2 years bata dawo garin ba. Har airport su daddy suka rakata sunata rarrashinta daddy na mata albishir din may be ma su dawo yola da zama, ita dai rai a bace sukayi sallama daddy ya cikata da gift mummy ma ba abarta a baya ba Driver suka samu na jiransu airport ya karba kayansu ya zuba a booth kan suka shiga yaja motan "Bloody!" "Ni kadenamun magana" dariya sosai yayi "Wai fushi kike da Yayanki?" "Haka nan ka dauko mutum daga gidan su amma kaita iko dashi kamar siya na kayi, yana da ga cikin abinda yasa fa tun farko na tsani auren ka saboda bana so nayi nisa da iyayena" da iyaka gaskiyarta take maganan Hannunta yakama ya gimtse cikin nashi yana murmushi "My love auren nawa kika tsana" Baki ta dan tura "Ai dah ne" tafada tana kauda kai gefe Chakulkuli yashiga yimata tana dariya yanata janta da wasa har ta mance ma tana fushi dashi. Bangaren Aesha da Mukhtar ma sun sa santa tsakanin su sunata Shan kauna ba kama hannun yaro. Driver na parking ta sauka ta nufa ciki Murda handle din kofar tayi ta shiga kamshin dadi ya bige hancinta amma da mamakinta se taji kamshin na yamutsa mata ciki bata zauna parlourn ba ta shige dakinta tana kokarin shiga toilet ya turo kofan yashigo ya dauketa tana dariya suka nufa toilet seda suka bata lokaci kan suka fito dakinshi ya koma ya shirya ya fice masallaci ita Kuma ta karasa shiryawa doguwar riga iya guiwa tasa kan ta zira hijjab tayi sallah seda tayi isha'i ta nade pray mat ta sauko down stairs tana kokarin zama taji ana danna door bell ta karasa ta bude taga me gadi tsaye rike da basket karba tayi tana murmushi a zuciyarta tace "Allah sarki ummi na Allah ya biya" Kulolin ta fiddo ta shirya kan dining taja kujera ta zauna zamanta ba jimawa ya shigo bakinshi dauke da sallama ta amsa kan ya karaso dining din ya zauna tare da mikar da ita ya dawo da ita kan kafafunshi ya janyo food flask din yana budewa kamshin abincin ya daki hancinta ta dauke numfashinta na seconds tare da binne kanta a kirjinshi tanaji cikinta na yamutsawa "Hayatee! Lafiya kuwa" "Lafiya kalau" "Anya kuwa kwana biyu naganki wani sukuku ko wani abu na damunki ne" "Aa Yaya Lafiya ta kalau kawai kwana biyu zazzabin dare nake fama dashi da safiya kuma tayi se in nemeshi in rasa" "Sorry shine baki fadamun ba" "Ai ba sosai bane" "Uhmmm duk da haka dai kinga da nasan maganin da zan baki" "Yaya yunwa" lakace hancinta yayi "Toh da Ummi bata aiko mana abinci ba fa dase kinjira andafa" "bakaji ba kace da amma yanzu tunda an kawo case closed" ta fada tana dariya Serving dinsu yayi ita dai daurewa kawai take dan kamshin abincin ba karamin hawa mata kai yake yi ba A baki ya soma bata tana karba chokali uku tayi ta fara kokarin mikewa ya riketa "Ina zaki? Kina bukatar wani abu ne?" Ta bude baki zatayi magana amai ya kufce mata tashiga kwarara mai a jiki............ *Gobe Monday Aminiyar ango Aminiyar ango **Toh bance gobe zanyi update ba gaskiya se wani iko dg Allah dan se yamma zan dawo gida* [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD AMINIYAR ANGO* *Page 53* *Dedicated to masoyinah, Abdulraheem (yaron umma), wannan page din naka ne, Allah yakarama lafiya me dorewa Kokarin mikewa take ya riketa, ta kalleshi ya dagamata kai. tako cigaba da kwarara amanta, seda ta amayar da duk wani abu da taci tun na safe har zuwa na rana kan ta kwanto kan kirjinshi tana maida numfashi. "Bloody! Kingama?". Kai ta jinjina ya mike da ita a jikinshi ya haura sama. Dakinshi ya nufa ya direta a toilet ya cire mata kaya yasata cikin kwamin wankan shima ya zare kayan jikinshi yashiga yamata wankan kan Shima yayi. A towel yana dota ya kwantar da ita kan bed. ya nufa wardrobe ya dauko jallabiya yasa itama ya dauko mata jallabiyarshi Ash colour ya karaso ya zauna bakin bed din tareda rungumota jikinshi yasa mata jallabiyan. Hannunta yarike cikin nashi kan yace "Heebbah!" "Uhmmm". "Meke miki ciwo?" "Babu" tafada tana yatsina fuska. "Toh me yakawo aman?" Yafada yana kallon kwayar idanunta. "Nima bansaniba. Tunda naji kamshin abincin kawai naji cikina yana yamutsawa". "Eyyyaaa sorry my Angel. Yanzu me kike so?" "Cake". "Cake Kuma bloody?" Kai kawai ta Jinjina, yace "okay" ya kwantar da ita ya fice. Tattare dining din yayi ya gyara gurin. Ya hada coffee ya dora kan tray kan ya bude fridge ya dauko cup cake ya dora gefen tray din ya nufa dakinshi. A kan bed ya ajiye tray din ya haura ya dagota yamata masauki akan cinyarshi yashiga bata cake din. Ko daya bata cinye ba tace ta koshi. Lallabata yaitayi har yasamu tacinye daya. Akan kafafunshi ya kwantar da kanta yana shafa gashin ta a hankali yana sipping coffee din har yagama kan ya mike ya maida tray din kitchen. Ya dawo ya kwanta ya janyota jikinshi ya matseta a kirjinshi yana shafa bayanta a hankali. "Hayatee! Yanzu me kikeji ajikin ki?" "Bacci nakeji" tayi maganan a shagwabe. Bece mata komai ba se matseta