Sashe 25
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kashe wayan. Tasauke nannauyar ajiyar zuciya "Tashi ki tafi nidai karki jamun ukuba" "toh zo muje ki rakani" "tafdi a sauka lafiya" zun bulelen hijjab ta zira ta fita, bakinta dauke da sallama tashiga parlourn a kan lips dinshi ya amsa sallamar kanshi a kasa yana operating phone dinshi, can nesa dashi ta tsaya batare da tace komai ba, "kin wani tsayamun a Kai kamar an baki gadi na ko so kike sena kamaki na zaunar dake da kaina" ya fada cikin dan daga murya. Jiki a sabule ta zauna a daya daga cikin kujerun parlourn bataja magana ba dan tasan ranta ne ze kara baci idan tace zata furta wata kalma. Dukar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta, tafi 10 minutes a haka kafin yasa wayar a aljihunshi yace "Keeee me kike bukata?" Dago kanta tayi suka hada ido tayi shiru takasa cewa komai "ina tambayar ki kin wani tsuramun ido" "Kai ta girgiza bana bukatar komai" "ki fada idan akwai abinda kike so zan Aiko a kawomiki" mamaki ne ya bayyana a fuskarta karara, Fu'ad ne yake tambayarta me take so, Bata gama zance zuci ba yace "okay duk sanda kikayi tinanin abinda kike da bukata ki sanarmun, dan karki hadani da Abba yace ban tambayeki ba" yayi maganar yana mikewa, ajiyar zuciya ta sauke a zuciyarta tace "Nidae nasan ba banza ba ashe Abba ne yasashi nemanta amma ba don ra'ayin shi ba" murmushin yake tayi Wanda yafi kuka ciwo yama za'ayi ta hada Fu'ad da Mukhtar bataji zata samu wanda ze nunamata kulawa kamar Wanda mukhtar ya bata. Nan ya wuce yabarta zaune tana sake sake. Washe gari Ranan kamu gidan yakara cika anata fama da Muhibbah ta shirye za'aje kamu an kada an raya taki zuwa Kuma saboda ita Koda Jafar yakira Aesha da Rufaeda da summy akan event din da za'ayi sukace iya dinner da kamu kadai za'ayi saboda basa so su takuramata tunda ba ta cikin mood me dadi, seda Aunty Maiminatu ta zare mata ido dan dole ta mike babu shiri dan tasan halin Aunty maimuna kanwar Fu'ad ce daga shi se ita itama batada wasa yanzu seta zaneta idan tacika taurin Kai, gidan duk an dade an tafi kamu, Fu'ad yasha kyau abinshi ya hakimce kan kujera sanye yake cikin tsadadden shadda marro colour se sheki yake fuskarshi babu yabo babu fallasa, ita Kuma Muhibbah sanye cikin Les maroon colour fuskar nan a turbune kamar an Aiko mata mutuwa, su Aesha ko bin ta kanta basuyi ba suka cashe abinsu anci ansha a rakashe se gurin magrib taro ya tashi, bayan isha'i iyye tace se ansama amarya lalle Aunty Asma'u tace "anfa dena wannan yayin iyye" "Kajimun ja'ira gaba daya bokokon nan yasa an mance da al'adda toh se ansashi" muhibbah na tirjewa tana kuka harda majina haka iyye ta tsaya seda Aunty Maiminatu tashafa mata lalle a tafin hannu sannan aka bude turare aka feshe mata ajiki, me lallin da aka dauko ta kwana tayi musu lallen ta ciro kayanta tashiga jerama amarya saletep na hannu tafara yimata tasamata lalle bayan tagama na kafa ta cire na hannun tashiga zana mata bakin lalle har kusan karfe 1 na dare ba'a gama masu Aunty Asma'u ba dan me lallen kwararra ce Kuma tanada sauri. Gida ya dau hayaniya se aikace aikace ake danma girkin kaiwa aikatau akayi se abinda baza'a rasaba aka bari a gidan tana kwance lamo a kan beda ta kudundune kamar jaririya tana ta aikin kukan da ya zaman mata al'ada a kowane rana babu kowa dakin babu abinda gabanta yake se faduwa cikin zuciyarta take ta maimaita "innalillahi wa inna ilaehi raji'un hasbunallahu wa ni'imal wakil, la ilaha illa antas subhanaka inni kuntu mina xalimeen. Su uku suka jero sanye yake cikin tsadadden shadda fara tass yasa hularshi tangarn baka sidik takalminshi baki sidik yana kokarin saka agogo a hannunshi Wanda Shima baki ne ya fito a angonshi fess se zuba kamshi yake Jafar da Suhail Suma sanye suke cikin farar shaddan, aikin jikin shaddan ne ya banbanta dana angon. Suna karasowa kusa inda motocinsu yake abokan ango suka dau shewa ango kasha kamshi irin wannan kyau haka shakiyanci suka shigayi Mai suna dariya be ko tanka suba ya bude motan ya shige nan duk suka shige motocinsu suka bar unguwar motocin su Abba da abokansu suka mara musu baya zuwa masallacin Amina foundation. Masallaci yacika makil ba masaka tsinke kowa ka kalla kama daga family muhammad shu'aib BICHI da ma abokan arzikin su kasan yana cikin farin ciki banda ango da bazaka gane mood dinshi ba dan dama ba ma'abocin murmushi ko dariya bane. A yau Asabar 21 ga watan satumba shekarar 2025 dubbanin mutane suka sheda daurin auren Fu'ad da Fatima, Abba ne yabada auren abokin daddy Kuma ya amsa. Ni Haruna Muhammad Shu'aib BICHI nabada auren 'yata Fateema Abdullahi Muhammad BICHI ga Fu'ad Harun Muhammad BICHI. Ni Khamees Abdulkhadir na karba ma dana Fu'ad Harun Muhammad BICHI auren Fateema Abdullahi Muhammad BICHI a bisa sadaki naira dubu dari biyar lakadan ba ajalan ba. Aesha dake zaune gefen bed din ta bude status din Anas taga ya daura videon daurin auren aiko tayi tsalle an daura an daura tazama matar ya Fu'ad nan kawaye suma suka dauka, aka hau guda tunda ga parlour tana jiyo gudar 'yan uwa da abokanan arziki, gabanta ne ya tsananta bugu ji take kamar zuciyarta zata tsago kirjinta ta fado kasa, rasa abinyi tasauka daga gadon tanajin kanta na saramata kamar ana juyata Jiri ne ya dibeta tafara gani dishi dishi mikama Aesha hannu tayi Jin tana kokarin kaiwa kasa Aesha da bataga saukowarta ba s e yanzu da ta bude baki daker ta kwala mata Kira da gudu ta nufeta ita da zahrah ko kafin su isa gareta se ji kuke tim ta zube kasa, zahrah tashiga jijjigata ba motsi Aesha ta kai hannunta wajen hancinta ina babu numfashi ai seta kwala ihun dayasa su Aunty Asma'u da Aunty Maiminatu fadowa dakin da gudu.............. *Andaura andaura taxama matar Fu'ad Allah mun godema* *F&F alkawarin Allah yacika* Allah dai yasa na yi daurin auren daidai dan bantaba zuwa daurin aure ba labari nakeji *Aunty na (Mum muneefa), ummu masoyi (Sirikata), sis seemah, Aunty Safiyya, ummu intisar, mamar mammy, sis bushira, sis mama tanko, Aunty kulthum, Sis Fatima Adam, sis ayyusha, mummy Aunty Farida,sis habeebah, sis Ameenatu , Aminiyar ango, name sake Niger, da wa inda ban ambaci sunansu ba* *Ku fito kusha shagali mu rakashe mu cashe, anko ne get pass din dinner duk Wanda beda anko yayi sauri ya mallaka kar ayi bashi , Kuma Wanda beyi anko ba bashi ba zuwa Kai amarya yola ko yaje bazata bashi ruwa ba bare chin chin [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 31* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Kanta suka nufo suka shiga jijjigata babu abinda Aesha take se kuka tana fadin "Aunty ki duba kiji wllhi bata numfashi Muhibbah ta mutu innalillahi wa inna ilaehi raji'un" abinda kawai take maimaitawa kenan tana kuka "Ke dalla rufema mutane baki, kibarmu muji da abu daya mana" Aunty Maimuna tafada. Ummi a sukwane ta nufo dakin zani a hannu "innalillahi wa inna ilaehi raji'un, ke maimunatu tsayuwar me kuke kunyi cirko cirko ku kamata ku haura da ita sama". Aunty Maiminatu da Aunty Asma'u da zahrah suka ciccibeta Aesha na biye dasu tana shasshekar kuka itama ummi binsu tayi a baya tana gyara zani yana kwancewa tsabar tashin hankali. Suna barin dakin aka dau kace nace akan amarya ta fadi kowa na mamakin abinda yasata faduwar kodai dama bata son mijin ne tunda dama ko wanka takiyi, Summy da Rufaeda ne suka shiga kareta, summy tace "Waye zeki farin ciki ranar aurenshi, ai idan kinga mutum na bakin ciki ranan aurenshi toh be son mijin ne amma ita da aka aura mata zabin ta Kuma yayanta kinga babu yadda za'ayi ace bata farin ciki" "Tun satin bikin nan take zazzabi ko jiya seda aka mata allura tun safe naji tana cewa zazzabin yadawo shiyasa ma akace kartayi wanka ta bari se Rana yayi" cewar Rufaida. Wata daga cikin kawayen tace "Kodai jimamin rabuwa da mummy ne?" Dayan tace babu wani jimamin rabuwa da mummy ita dai taji dashi dai ai duk wayen amarya se ansha romanta" nan suka shiga shakiyanci suna dariya wasu namata fatan samun sauki. Nan parlour ummi ta tsaya tana ma mutane bayanin amarya zazzabi take shine ma ya kaita ga Suma saboda tasa ma kanta tinanin rabuwa da iyaye, wata kawar ummi tace "Allah sarki Allah yabata lfy ai kowa da haka yasaba se hakuri". Dama mummy Koda a ka fadamata cewa tayi idan ta mutu Allah yajikan ta dan batasan me Kuma zatama Muhibbah ta fahimce su ba dan haka batada lokacinta ta bakinta takeyi. Up stairs suka haura da ita a bedroom din ummi da take sauka idan tazo gidan suka ajiyeta kan bed sharaf tasaki jiki tabi gadon alamun babu numfashi a tattare da ita, tsayuwa kawae sukayi akanta suna kallon ta gaba daya sun rasa mezasu mata Aunty Maimuna tace "Aesha bani wayanki" se lokacinma ta tina akwai waya a hannunta, da sauri