Sashe 62
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauri yayi sujudu shukur yana mikama Allah godiya. Ya mike ya nufo lobor room din, ya tarar nurse na goge ma babyn jiki, be tsaya nan ba ya karasa wajen Muhibbah yayi pecking dinta a kumatu. Tunda ya karaso kamshin turarenshi ya sanar da ita shine amma ko kifta idanu batayi ba bare yasa ran zata bude. Hannayenta ya rike "Hayateee! Bude idonki yayanki ne ba doctor bace" kara runtse idanu tayi ko motsi takiyi. Doctor fareeda ta karaso gangansu rike da allura yace, "Doctor kamar akwai sauran baby a nan ko?" Yafada yana kai hannunshi cikinta "Uhmmm nima haka nake tinani naso naga cikin na motsi" da sauri ta tashi zaune tana shafa cikinta tashiga zare idanu, tayi kwal kwal da ido tana kokarin yin kuka. Dariya yayi yace, "No karki kuka blood, ke kam kin cika tsoro wasa fa ake miki" se lokacin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya batasan har ta fito fili ba Dariya doctor tayi "Madam dan gyara please" ta fada tana fasa allura (Oxytocin) ta zuka a siringe. "Doctor badai allura ba" tafada tana ya mutsa fuska "Kar muyi haka madam, kika iya santalo kyakkyawar baby bare wata allura, nayi tinanin daga yanzu ma kin dena kukan allura ai" Tana kokarin tsira alluran tayi saurin rike mata hannu "Dan Allah doctor kibar alluran nan, wllhi akwai zafi" tayi maganan tana hawaye "Kai! maman baby kina so babynki tamiki dariya kina kukan allura". Ta fada tana tsira mata alluran a cinya, tasa kuka. Juyawa tayi ta karba babyn daga hannun nurse ta mikama Fu'ad. "Congratulations sir it's a baby girl" fadada murmushin shi yayi ya karbeta yayi pecking goshinta tare da furta "Thank you doctor" "You deserve more" Kai ya Jinjina ya mikamata babyn yace ta rike ze taimaka ma Muhibbah ta gyara jiki. Akwatin ya bude ya zabo mata doguwar rigan atampha, yazo ya kamata suka karasa toilet ya mata wanka ya gyaramata jikinta tareda ziramata doguwar rigan ya kamota suka fito. Akwatin ya janyo, ita Kuma ya tallabota ta dayan gefen suka karasa special room. "Waye ya hada kayan akwatin nan?" "Aekin Aesha ne, nace mata kaya daya naga su Aunty Asma'u na sawa, amma ita ko iya kayan baby tasa sun kai kala goma" takarashe maganan tana zama kan gadon. Kai kawai ya jinjina ya mika hannu ya karba babyn ita Kuma doctorn ta fice. Shima hawa gadon yayi ya zauna gefenta, yasa hannunshi daya ya dago habarta yana kallon cikin kwayar idanunta tayi saurin runtse ido. Bata zata ba se ji tayi ya hade bakinsu guri daya ya shiga aikamata da deep kisses tayi loosing balance tayi baya baya ta kwanta yamata runfa, har lokacin yana rike da babyn a dayan hannunshi. Zame bakinta daga nashi tayi tasa hannu biyu ta ture kirjinshi ta tashi zaune ta hade kanta da guiwa tana sauke numfashi. Hannu yasa ya dago kanta yana murmushi yace, "Mammi! wai fushi kike dani?" Kai ta gyada kana tace, "Bakai bane kacemun haihuwa babu wahala ashe akwai azaba harda bala'i ma" dariya me sauti yayi "Shine laifin nawa?" Ta jinjina Kai "Sorry a gafarceni, nayi tinanin babu wahala ne shiyasa na fada miki hak" murmushi tayi "Kuma kayimun alkawari Kai zaka zauna dani har na haihu amma kayi tafiyarka ka barni da doctor, inata shan wahala wani abun ma fa da gangan takeyimun, kaga ko gurin samun hannun nan da takeyi kar kaso kaji azaba har kwakwalwata". Pecking kumatunta yayi "A gafarceni guiwowina a kasa, nayi kokarin na kasance tare da ke amma nakasa juran ganin halin da kike ciki, Kuma na fahimta zamana kusa dake rauni yake sa miki, koda na koma office kasa hakuri nayi seda na kunna CC TV camera Ina kallon abinda ke faruwa, I'm sorry". Murmushi tayi ta kwantar da kanta kan kafadarshi, ya doramata babyn kan jiki "bloody! Ki Kalli babyn nan dake take kama" hannu tasa ta rungume babyn tayi pecking kumatunta, Aiko tasa kuka. Kallon juna sukayi, sukasa dariya. "Yaya kaji gulma fa, da bata tina da kukan ba seda na dauketa. Base kin fada ba ai ni tun kina ciki na gane ba sona kike ba kinata wahalar dani kinzo duniya hakan ma be miki ba na daukeki kin wani tabe baki kina kuka uhmmm" "Kisha kuruminki gobe Aunty Suhailat zata tafi dake ta hada da Aadil na barmata". Ita ko baby kamar tanajin abinda ake cewa tayi shiru se wuwurga kafa take. Murmushi yayi "Sannu maman baby kinga ai taji fadan Ammin ta tayi shiru" hannunta ya kama yayi pecking "Allah ya miki albarka blood, Allah ya biyaki da gidan aljannahtul firdaus Allah ya rayamana babyn mu akan sunna ya albarkaci rayuwarta mu kuma Allah yakara mana kaunar juna". "Ameen my heart, tnx too" shiru sukayi na seconds kan tace, "Hearty! Banga su ummi ba tun dazu nake zuba idon ganinsu amma shiru". "Bansanar musu ba, kinsan da sunji duk zasu daga hankalinsu, yanzu Kuma dare yayi shiyasa na bari se zuwa safiya nayi surprising dinsu" Kai ta jinjina tana murmushi "Ka kiramun mummyna please" "Da daren nan? 3:10am fa, kiyi hakuri har zuwa asuba uhmm". Kai ta gyada batareda tayi magana ba. "Kin mintsine babyn kuwa?" Dariya me sauti tayi tana kara shafa fuskan babyn tanajin yadda kaunarta ke mamaye zuciyarta "Uhmmm na hakura" "Toh ni bari nacika alkawari na, kar ki kuma fushi kice nayi alkawarin zan rankwashe baby Kuma ban cika ba" ya fada yana Kai hannunshi kamar ze rankwasheta tayi saurin kankame babyn a kirjinta ta rike hannunshi sukasa dariya a tare. "Ai ni ta wahalar kuma na riga na yafe" kallon yadda babyn ke mutsu mutsu yayi kana ya maida idanunshi kan Muhibbah. "Bloody babyn nan fa abinci take so" Kafada ta make "Ta bari seda safe kasiya mata NAN" tafada tana mikamai babyn, ta zame ta kwanta. Bata jima da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita dan jikinta duk ciwo yake mata. A kafada ya sabata yana dan bubbuga bayanta, saida da ta koma bacci ya kwantar da ita kusa da mamanta, ya gyara ma mamanta kwanciya ya lullubesu ya tofa musu addu'a ya koma kan kujera ya kwanta. Karfe 5:20am ya tashi yashiga toilet ya dauro alwala ya fice masallaci, dama baccin nashi rabi da rabi ne yanayi yana farkawa ya dubasu kana yakoma ya kwanta. Koda yadawo masallaci stood ya janyo ya zauna yana kare musu kallo yana jin farin ciki mara misaltuwa na lullubeshi se sakin murmushi yake. Wayarshi ya zaro ya shiga dialing numbern mummy, ringing biyu ta dauka "Yayansu lafiya kuwa?" "Lafiya kalau mummy, dama Muhibbah ce ta sauka" yafada yana shafa kai "Alhamdulillah! Yaushe? Me aka samu??". "Cikin dare, ansamu budurwa" "Masha Allah! Allah ya raya. Ina Muhibbahn?" Seda ya kalleta kafin yace, "mummy tana bacci" "Allah sarki, toh shikenan idan ta tashi ka kirani" daga haka sukayi sallama Seda 7 tayi kana ya kira Ummi tun kafin yayi magana tace, "Lafiya?" "Lafiya kalau, Muhibbah ta sauka" washe baki tayi cike da farin ciki tace, "yaushe? Me ta haifa?? Kuna ina yanzu???" Ta jero tambayoyin cike da kosawa da Jin amsoshin tambayoyin. "Jiya da dadare, tasamu mace, ummi muna asibiti amma base kunzo ba yanzu zamu dawo gida" "Alhamdulillah! Ina Muhibbahn?" "Ta shiga toilet" "Fatan dai babu wata matsala" "Komai lafiya ummi" "Yauwa toh nan gidan zaka kawomun ita" "in sha Allah" yana kai nan tayi hanging call din, yabi wayar da kallo jikinshi yayi sanyi Jin Kalmar ummi na karshe cewa ya Kai Muhibbah gurinta beso haka ba. Baki ta wanke ta fito ta zauna bakin gadon "Good morning my heart" "Morning our adorable mum, ya karfin jiki?" Murmushi tayi "Dasauki our beloved father" hancinta ya dan ja "Munyi waya da mummy kina bacci" yafada yana dialing numbern mummyn. zatayi magana ya manna mata wayar a kunne. "Hello mummy na......." Kawai ta fashe da kuka "Muhibbah lafiya, me yafaru?" "Mummy ashe haka haihuwa take da wahala, banzata zan rayuwa ba nayi tinanin mutuwa zanyi" "Allah sarki auta na, sannu kinji" "Dan Allah mummy ki yafemun, natuba" takarashe maganan tana sakin sabon kuka "Toh miye na kukan Kuma, nikam bakiyimun laifin komai ba, koma kinyi mun bisa kuskure na yafe miki duniya da lahira" "Ki rokamun Abba ya yafemun" "Shima ya yafemiki, kidena kukan nan kinji" Kai ta gyada sukayi sallama. Gefenta ya zauna yasa hannu ya share mata hawaye, yasa spoon yana dibo tea din yana kaimata baki, saida yaji yayi yadda zata iya sha ya cire spoon din yana bata da cup din har ta shanye. Hijjab ya dauko mata ya zira mata yadauki babyn ita Kuma ya rikota ta dayan side din suka fito anata mai barka yana amsawa fuskarshi dauke da fara'a. Aunty fareeda ta biyo su da akwatin. "Toh maman baby Allah ya raya" a kunya ce tace "Ina kwana" "Lafiya kalau, ya karfin jikin?" "Alhamdulillah". Bayan booth yasa akwatin ya budemata ta shiga ya mikamata babyn Shima ya zagaya ya shiga yaja motan suka fice daga asibitin. Gidan ummi ya nufa, a parking lot yayi parking ya fito ya bude mata ya dauki babyn kana itama ta fito suka karasa ciki Tasamu har Aunty Suhailat ta iso, ana fadamata haihuwan mijinta ze tafi aiki tako zaro mayafi ya sauke ta gidan ummi kan ya wuce. Daki daban aka ware mata kafin ta iso an kara gyarashi ansa turare, Aesha ta karasa ta karba babyn bakinta yakasa rufuwa tsabar farin ciki. Ita Kuma Suhailat taja akwatin suka nufi dakin "Ina kwana Ummi" ta gaisheta tana sunkuyar da Kai "Lafiya kalau Muhibbah, sannu da kokari Allah yabada lafiyar shayarwa" murmushi kawai tayi tana kallon yadda Aesha ke rike babyn ji take kamar zata fadar da ita ganin idanun ummi kawai yasa ta daure batayi mata magana ba" "Sister wllhi babyn nan sak ke kamar an tsaga kara, ko Aunty Suhailat?" "Sosaima kamanninma bana wasa ba kamar tayi kaki" Aesha tace, "Kuma irin babyn da kike so kinganta 'yar lukuta tubarkallah" Ita ko baby se wuwurga kafa take tana tabe baki tana kananun kuka, hakurinta ya kusa karewa. "Wai Aesha kinaji yarinya na bukatar mamanta kin ki bada ita, ko se ta bude baki zaki fahimta yarenta" Ummi ta fada, duk akasa dariya. Karbanta tayi ta mikama Muhibbah "Karbeta yunwa takeji, Allah ma