← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 69

Sashe 19

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

bal baleta da fada dukanta ne dai yanzu ya dena. Rai a dagule ya shigo parlourn, yana shigowa su Aesha suka kama gaban su parlourn yayi saura daga mummy se ummi, nan ummi ta haushi da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba "Da girmanka zaka tsaya jayayya da bawan Allah, Ina ruwanka da zuwanshi kofar gidan, gurinka yazo ne? Ko An daura maka aure da Muhibbahn ne dazaka hanata rawar gaban hantsi, kashiga hankalin ka dani fa kaji na fadamaka". Fada take Mummy na bata hakuri, seda ta Kai aya sannan yace "Ummi kiyi hakuri". "Tashi ka bani guri" jiki babu kwari yatashi ya wuce. juyowa tayi ga Mummy tace "Wllhi wannan lamari na damuna a haka Muhibbah zata zauna da yayansu da zafin zuciyar nan nashi, na rasa inda zan bulloma wannan al'amarin nayima Abbansu magana ya nunamun aure babu fashi, Muhibbah karamar yarinya ce ina tsoron zamansu inuwa daya tunda ba sonshi take ba". Murmushin karfin hali tayi "Haba ummin su addu'a zamu bisu dashi ai shi yayan nasu ya mallaki hankalinshi, indai tayi abinda yake so zasu zauna lafiya dama shi zaman aure dan hakuri ne, batun bata sonshi duk shirmenta ne bata gama sanin menene son ba ma, karki damu khairan in Sha Allah". "Nima ina fatan haka" tasan dai mummy tafada hakan ne kawai amma ba wai tana son auren sosai har cikin zuciyarta bane. Kan bed ya kwanta ya tsurama ceiling ido yana tinanin abubuwan dasuka faru dazu tsakaninshi da Mukhtar tina kalaman da Mukhtar yayi suka kara bata mai rai idonshi ya kada yayi jajir yakama lip dinshi na kasa ya tauna da karfi, ya jima a haka kafin ya mike yashige toilet ya sakarma kanshi ruwa. Bayan angama dinner a halin gidan suka hallaru a babban parlourn daddy anata fira ana Raha banda Muhibbah da ta hade rai tanata faman duban waya kozataga Kiran Mukhtar, tun kafin magrib take Kiran wayanshi tayimai more than 5 missed calls amma ba'ayi picking ba tacika tayi fam kamar zata fashe. Abba ya kirata "Maamana" dasauri ta dago ta kalleshi "Na'am Abba" "lafiya kike? Ko jikin ne" "Eh lafiya kalau, na war ware". "Allah yakara sauki" "Ameen Abbana". "Maamana tun dazu anata maganan hall din da za'ayi walimar graduation dinki dana Aisha amma baki ce komai ba, bakida choice ne?" Kai ta gyada "Eh duk abinda kuka tsara dai dai ne" Aisha tayi saurin cewa "Aa gaskiya sister ki zabamana guri me kyau, kinsan ni bansan kan kd sosai ba". Da kyar Aesha tasa ta zaba musu, Aka bari akan jibi za'ayi walimar zuwa gobe se a gayyata 'yan uwa na kusa.........
Chapter 19 · 0% Book details