Sashe 40
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
fa akwai nacin jaraba base an fito an ce ba'a sonka ba a alamu zaka gane". "Hmmmm kedai bari kawai Ramlat zan seta mishi hanya daga yanzu yaga ina tankashi ne baze jazamun bala'i ba in ke daukarwa kaina zunubi". Aesha tayi saurin taran numfashinta "Wallahi sister nima abinda nake tinani kenan kar ubangiji ya kamaki kuma wllhi ina tsoron ranan da ya Fu'ad ze sani mun Kade bake kadai abin ze shafa ba harda ni ke hatta su Ramlat bazasu tsira ba sedai idan basa gurin amma wllhi se yamana bugun sakwaran lagos" duk dariya sukasa harda rike ciki Muhibbah ko kawai hasaso irin shakar da ze mata take se ta gwanmacin marin da yamata akan mukhtar sau dari kan ukuban daze mata idan tasake yaji labarin nan. "Toh shi haka ya Fu'ad din yake da zafi, baya so ku kula kowa" "Bazaki gane yaran bane, shi baya so muke kula samari barkatai yace har yanzu mu yara ne bamu isa aure ba". Da sauri Umaina ta tari numfashin ta "Amma dai duk da haka Aesha ki kalla yadda fateema kema sauban wulakanci har gara malam mukhtasir yasa mu arzikin magana amma shi kam bawan Allahn nan ko muryarta be taba jiba har saki tayi kika cemai wai tanada aure se jiya ya tareni yake tambayata dagaske ne kinada aure, dole namai karya nace eh nima bansan kinada aure ba seda naje gidanki saboda dai ya hakura ya dau dangana ko zuciyarshi zata samu salama babu kyau irin abin nan baki ga yadda jikin bawan Allahn nan yayi sanyi ba nan nabarshi tsaye gwanin tausayi, wai kina cewa ubangiji ze kamaki kiji wata magana naga fa". Dogon tsaki taja "toh kema naga macece ki aure su mana, shikuma sauban yake kowa dama ya tambayeki kin kara tabbatar mishk inada aure amma dazu da safe dana shigo school ya biyoni har bakin department dinmu yanamun magana naki kulashi ya gaji ya juya tsabar be san abinda yakeyi ba" "Maida wukar kawata abun bana fada bane gani nayi bashida wani aibi Kuma bacewa nayi ki kulashi ba se yaje yasamu ya Fu'ad din idan yayi bincike akanshi yaga yayi shikenan, amma tunda bakya son maganan in Sha Allah bazan kara ba". Daganan suka ajiye zancen suka dauko wani firan. Bakinta dauke da sallama tashiga parlourn a zaune tasamu mairo tana kallon MBC Bollywood da fara'arta ta zauna kusa da ita "Sannu da gida Aunty mairo, ko kefa ba gashi kin samu abin debe kewa ba amma seki zauna shiru" "Yauwa hajiya sannu da dawowa, ya makarantan" "Makaranta ba dadi ba damar bari". Dariya tayi tana mikewa, kitchen taje ta kawomata abinci da ruwa tajanyo center table din dake parlourn ta ajiye a kai. "Kai ai da kin bari na tashi na zubo da kaina sannu da kokari nagode" Ganin sun gama film din ta kai hannu ta dauki Remote ta canza channel din MBC 3 "Yi hakuri Aunty bari na dan Kalli cartoon dan ni bana gane kallon film sama da cartoon" Murmushi tayi "Bari na tafi" "Se ana fira kice zaki wuce" "Yamma tayi kuma yanzu zakiga mijinki yadawo" Dariya tayi sosai "Oh kice Yaya kike gudu bakya so ku hadu" murmusawa tayi sukayi sallama. Seda tagama cin abincin kan ta haura dakin ta ta ajiye jaka da hijjab din ta ta nufa kitchen ta hada dinner ta shirya dining ta je tayi wanka ta dawo parlourn ta hakimce ta cigaba da kallon cartoon dinta hankali kwance. Da sallama iya kan lips dinshi ya shigo kamshin turarenshi ya sanar da ita dawowan shi. Mikewa tayi ta karasa ganganshi a dan tsorace take amma ta daure "Sannu da dawowa" "Yauwa" ya fada yana Kallon ta itama shi take kallo kawai ta tsinci kanta da sakin murmushi. Shima murmushin gefen baki ya mata seta lumshe ido gani take kamar a film. Karbar ban brief case din hannunshi tayi suka fara takawa a tare har dakinshi ganin yafara kokarin cire kayan jikinshi ta ajiye brief case din ta fito ta rufo mai kofa. Wanka yayi ya zira jallabiya sauri sauri ya fice ya nufa masallaci. Itama dakinta ta haura tayi sallah seda tayi isha'i ta fito tana zama yana shigowa. Seda yagama dinner ya koma parlour ya fara aiki a wayanshi a kujeran dake facing dinshi ta zauna ta dauki wayan ta ta fara chatting da Aesha tana kwatanta mata ukubar da ya Fu'ad ze musu idan yasan malam mukhtasir na kula ta. "Sister kinga nidai shawarar da zan baki kifara sanarma Yaya da kanki tun kafin ya gane da kanshi" "Waa rufamun asiri so kike gobe da safe a zo a dauki gawata sedai idan ke zaki fada mai kinga a gaban Ummi baze miki komai ba" "Sannu muguwa ke dakike matarshi kina jin tsoro se niii, ai wllhi ko gaban Abba ne sedai idan ban mai laifi ba dukana yakeyi". "Keeeee hadomun coffee" seda safe tama Aesha ta ajiye wayan ta shiga kitchen. Bata jima ba ta dawo rike da cup waya ta hangi yanayi dan zaro ido tayi Jin sautin kuka na tashi daga cikin wayan, indai kunnenta ba karya yake fadamata ba muryar mace takeji tana kuka "Dan Allah doctor ka saurareni sonka na neman kaini lahira, wllhi ni ko baka sona indai zaka aureni zan zauna dakai a haka" "Ba kisan inada aure bane?". "Kar kadamu ni wllhi ko mata 3 gareka zanzo ata hudu" duk da tayi mamakin Jin yanada aure bata taba Jin labarin aurenshi ba ko a social media bata tinanin ko nurses din dake aiki a asibitinshi sun san yayi aure, wata zuciyarta Kuma na kokwanto akan auren kodai kawai ya fada ne. Jin yayi shiru tace "Dan Allah yaushe zaka shigo ka gaida Ammi kullum ina bata labarinka" ganin Muhibbah tsaye tana kallonshi ya saki murmushin gefen baki "Ki ajiyemun address dinki zuwa gobe idan Allah ya kaemu zan shigo". "Thank you" "It's my pleasure" yana kai nan ya yanke wayan. Bata ankara ba taji glass cup din hannunta ya kufce ya fadi kasa seji kake tuusss ya fashe, dasauri ta matsa baya a tsorace ganin kallon dayake mata takun da zatayi se ji tayi ta taka fasashen glass din ta ko saki razananniyar karaaaaa tayi baya zata fadi yakarasa da hanzari ya tarota ta fado jikinshi yasa hannu ya rungumeta a kirjinshi........