Sashe 15
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
su hado lefen". "Dan yabada sadaki dubu dari biyar shine aiki da kudinshi za'a hado lefen zefi ganin darajarta ba wai ya sameta a sama ba". A Nan take yayi ma mummy transfern makudan kudade, daddy yace "Allah Yama albarka" "Ameen daddy". Da rinannun idanunta take kallonsu cikin matsanancin tashin hankali tace "Abba badai lefena kuke maganan ya Fu'ad yabada kudi a hadaba" "idan ba lefenki ba to nawa, bikin ki keda Fu'ad ranar asabar me zuwa idan Allah ya kaimu" cewar daddy. Maganar ce ta daki dodan kunnenta, jinta ya tsaya na dan sakonni ji tayi duniyar ta juyemata, hankali tashe takarasa ta dafa kafafun daddy "dan Allah daddy kuyimun rai wallahi bana son ya Fu'ad idan kuka aura min shi mutuwa zanyi". wani gigitaccen Mari yadauketa dashi ji kake tasss "Aiko sedai ki mutu a gurin namiji bamu samu matsala ba seke ke wacece da zamu yanke hukunci kice ba haka ba" ya fada yana huci. Mikewa tayi "Abba kafadamusu akwai wanda nake so, kunmayi magana dashi, Dan Allah Abba kar kabari a aura mun wanda bana so wllhi bana son ya Fu'ad gara a aura mun koma waye akan shi Aisha kicemun mafarki nake bada gaske ba innalillahi wa inna ilaehi raji'un. Zuciyarshi wani tafarfasa take kalaman muhibbah nasa zuciyarshi kuna, "idan kin kwantar da hankalinki nima ba sonki nakeyi ba yarinya dan banida yadda zanyi ne bazan iya ja da maganan su daddy ba, Amma da banga abinda zanyi dake ba". Yafada a zuciyarshi. Itama Aisha kuka take saboda ba karamin tausayi muhibbah tabata ba ta ina zata soma rayuwa da ya Fu'ad karkashin inuwa daya miskilin mutum Abu kadan ya kamasu ya zane a haka ne zatayi rayuwar farin ciki dashi. Kuka take kamar ranta ze fita numfashinta yafara kokarin daukewa se ji sukayi ta fadi kasa tiimm ba motsi............ *Ah ku tafamun yaufa nayi typing me yawa babu laefi, ku danna mun likes kuzuba comments indai kunji Dadin long page din dana Baku, thank you so much my fans ina alfahari dakuuu*