Sashe 31
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suka takasu ze kaisu ga hanya madaidaiciya, zaman lafiya ze dore a gidansu sannan farin ciki ze dawwama a rayuwarsu. Kinga hakuri: Wannan na mutum biyu ne se kin zama me hakuri Shima Kuma se yayi hakuri dake amma idan so samu ne hakurin 'ya mace yafi na da namiji zaki ci ribar hakurin a gaba Koda baki samu wajen miji ba zaki samu wajen 'ya'ya domin akwai matakin da zaki kai yaranki zasu maida ki tamkar sarauniya Juriya: Ana so ki zama me juriya duk abinda miji ze miki ki jure duk tsananin da zaki shiga a gurin miji ko 'yan uwanshi ki jure komai nada lokaci wata rana se labari Uzuri: ana bukatan ma'aurata su kasance masu yima juna uzuri, zamantakewar da babu uzuri a cikinta bata karko Kulawa: yana daukan ma'ano ni, Auren da babu kulawa acikinshi babu tattali baya nagarta ki tattala mijinki kibashi kulawa yadda ta dace yanayin kulawa dashi yanayin kaunar shi gareki Shima kulawa na mutum biyu ne Kulawa yana daukar ma'anar kiyayye dukiyar miji ki tattala kayanshi ki tayashi kula da dukiyarshi duk wani abu nashi kiyi kafa kafa dashi Kulawa yana daukar ma'anar kulawa da kanki kare mutuncinki daga kula wasu mazan daba muharramanki ba kiyaye kanki daga shigan banza ko sa kayan da zasu fidda surarki a waje. Tausayi: kinsan ma'anar tausayi toh matukar babu tausayi da Jin Kai tsakanin ma'aurata toh zamansu babu inda ze je Shima tausayi na mutum biyu ne Biyayya: Shine gaba idan har baki ma miji biyayya duk abinda zaki mishi bashida amfani dan baze ganshi ba ko goyashi zaki dingayi indai baki mai biyayya bashida amfani Biyayya Yana nufin, duk abinda mijinki yace kiyi toh kiyi iya iyawarki matukar be sabama shari'a ba, idan yace ki bari toh duk sonki da abun nan ki hakura ki barshi se a zauna lafiya Biyayya na 'ya mace ne. So: ki so mijin ki domin idan babu soyayya duk abin da na lissafa miki bazaki iya yinshi ba, ki koyama zuciyarki son mijinki So na mutum biyu ne domin ko namiji idan baya sonki baze iya kyautatamiki ba Kauna: kauna shine gaba domin so tsuntsu ne ya kan iya tashi daga wata bishiyar zuwa wata amma kauna bata tsufa, Shima kauna na mutum biyu ne Wannan shine kadan daga matakan rayuwar zaman gidan aure, idan nace zan zayyano su gaba daya a yau zamu kwana zaune bamu gama ba. Dan haka ki koyama zuciyarki kaunar mijinki kiyima iyayanki biyayya Allah ze taimakeki kinji ko?". Kai ta Jin jina tana share hawayen da suka silalomata Yana sauraron duk nasihar da mummy ke mata se yaji duk jikinshi yayi sanyi. "Dazu umman Mukhtar da Zarah suka zo yimana ban gajiyan tashin taro" "Allah sarki umma ai ita yakamata aje ama ban gajiya, Allah yabiyata, zan kirata na mata ban gajiya, Amma kinga ya Mukhtar? Ko bashi ya kawo su ba". "Aa driver ya kawo su, tun kafin biki banji yakara zuwa kofar gidan mu ai" rau rau tayi da ido hawaye sun cikamata ido tace "Allah sarki ya Mukhy na" dagowa yayi ya tsareta da idanu tunda tafara wayan yaji tasa kuka ya daga Kai ya Dan kalleta ya maida kanshi kasa be kara ko kallonta ba se yanzu da yaji tace ya mukhy ta. Fada mummy tafara mata "Kina matar wani kina Kiran sunan wani namiji ba muharramunki ba, kina so ki hadu da fushin ubangiji ne?" Kai ta girgiza kafin tace "Aa" "Toh kar in Kuma ji kinji ko?" Kai ta Jin jina "Allah yamuku albarka yabaku zaman lafiya, ki gaida yayan naki seda safe" ganin irin kallon daya ke mata yasa tasha jinin jikinta tayima mummy godiya sukayi sallama. Yana ganin ta gama wayan Tsamm ya mike tsaye ya ajiye cup din hannunshi akan center table, idonshi ya kada yayi jajir tsabar baccin rai cikin tafiyar shi na takama ya nufota ganin gurinta yake yowa ta mike da sauri tana ja da baya yana binta seda ta kai karshen bango ta tsaya, kirjinta na bugawa da karfi zuciyarta ta tsinke tsabar tsoro hawayen dake kwance a idanunta suka samu nasarar silalowa Ji tayi numfashinta na kokarin daukewa ganin yazo daf da ita har numfashin su na gaurayuwa dana juna yasa hannunshi daya ya dafa bango se taga kamar ze rungumeta, hancinshi ya kai setin wuyanta yana shin shina lumshe ido yayi Jin wani sihirtaccen kamshi dake tashi a ilahirin jikinta, tsoronta ne ya karu zuciyarta ya tsananta bugu kamar saukar aradu haka taji muryarshi yana magana "A cikin gidana kike Kiran sunan wani Kato a gabana tsabar kin rainani ko? Dasauri ta girgiza Kai "Ya mukayi dake tun a kd? Bance kar in kara ji kin kiramun sunan wani kato ba" runtse ido tayi da karfi dan ta tsani taji yana Kiran Mukhtar da Kato "Ba tambayarki nake ba" ya fada da dan karfi Dasauri ta gyada Kai can Kuma tace "K.... Ka...fadamun" "toh iskanci ne yasa kika ambata a gabana ko kunya?" Shiru tayi takasa cewa komai ji take kamar kasa ya tsage ta shige tsabar tsoro "Nace iskanci ne ko raini?" Tayi Saurin girgiza Kai "Dan Allah kayi hakuri" "Rike hakurinki bakin rai nani ba zanyi maganin bakin rashin kunya". Ta bude baki zatayi magana taji ya hade bakinsu guri daya............... *Uhmmmm nayi shiru ni nayi nan Muhibbah Allah ya kubutar dake hannun wannan baudaden mutumin* *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 36* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Kai tashiga girgiza mai hawaye na zarya a kuncinta tana kiciniyar raba bakinta da nashi amma takasa Hannunshi ya Kai ya zagaye kugunta, hankalinta ya kara tashi tsoronta ya ninku numfashinta yadena fita dai dai, ji tayi kafarta taki daukarta jikinta ya mutu tana kokarin faduwa tayi saurin kai hannunta ta rike kugunshi, seda ya ladaftar da bakin kan ya raba bakin shi da nata ya Kai hannunshi saitin zuciyarta yaji yadda yake bugawa dasauri tsabar tsoro, bakinshi ya kai wajen kunnenta kamar me rada yace "Matsoraciya kawai, kinsan kina tsoro kike rashin kunya? ni babu abinda zan miki bakin rashin kunyan kawai na ladaftar gobe kuma kika kara sena miki abinda yafi wannan, yana Kai nan ya dan tureta ya nufi upstairs" Tafi minti biyar tsaye a gurin tana kuka kana itama ta haura ta nufi dakinta tana shiga ta rufo kofar da karfi ta murda key, toilet ta wuce ta dinga zira yatsanta a makogoro tana kakarin amai amma yaki fitowa dole ta hakura tayi brush tafito ta kwanta tayi Allah ya isa a ranta yafi cikin kwando, ko miyau taki hadiyewa se ya taru taje toilet ta zubar a haka har tayi bacci da guntun zazzabin daya lallabo ya rufeta. Yana shiga daki yafada kan bed yayi ruf da ciki yanajin yadda cikin shi ke murdawa se faman sauke ajiyar zuciya yake, mikewa yayi dafe da mararshi ya shige toilet yasakarma kanshi ruwa yajima sosai a toilet din kana ya fito daure da towel ya nufa wardrobe ya dauko rigar bacci ya zira ya kwanta yanata faman juyi har bacci barawo ya saceshi. Tun 7 ta tashi tashiga kitchen tafara kokarin hada break fast soyayiyar doya da miyan source tayi tashirya dining ta koma daki tayi wanka tashirya cikin doguwar rigan abaya maroon colour A dining ta zauna ta zuba doyan tafara ci seda ta kusa gamawa sannan ya fito shirye cikin farar t shirt da wandon jeans, kujera yaja ya zauna a kunya ce tace "Ina kwana" "Lafiya" yafada yana kashemata ido daya tayi saurin dukar da kai Serving dinshi tayi ta mike ta koma parlour dan dama tariga ta koshi, be wani ci dayawa ba ya mike ya fice daga parlourn ta bishi da kallo har yakarasa ficewa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta mike tashiga gyaran gidan. Parlour ta dawo tayi ta gumi tarasa me Kuma zatayi ta gaji da zama shiru jinta take kamar a freezon karar wayanta ne yadawo da ita daga tinanin data tafi Ummina sunan da taga yana yawo a screen din wayan Da murmushi ta dauka "Assalamualaikum" "Wa alaekumussalam" "Ina kwana Ummi" "lafiya kalau Muhibbah, ya gidan" "Lafiya kalau Ummina" "Ya zaman shiru, aiki ya miki yawa ko? Bari zuwa gobe za'a samo miki 'yar aiki" Murmushi tayi "Aa Ummi aikin ma babu yawa tunda ba bata gidan ake ba, sedai gidan shiru babu dadi" "Kinga idan aka kawo me aikin zata dinga debemiki kewa kafin ta tafi, Kona turomiki mairo ne? Idan yaso da yamma se driver ya dawo da ita nan saboda nafi yarda da nutsuwarta tafi shekara 5 tana mana aiki batada wata matsala" "Shikenan ummi hakan ma yayi nagode Allah yaja da kwana" "Ameen diyar kirki, Amma se munyi magana da mijinki kinsan baudaden halinshi kar na turota ya korota" dariya tayi tace "Haka ne Kuma ummi" "sekin kara hakuri da yayan naki kinji ko?" Murmushi me sauti kawai tayi batareda tace komai ba "Allah yamiki albarka" "Ameen Ummi, Allah yakara girma" Ameen ta amsa dashi tana ajiye wayan. Kwanciya tayi kan kujera ta rufe ido tana tino moment din su na jiya bata San ta saki murmushi ba tina yadda duk ta tsure kamar wacce tayi arba da