← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 69

Sashe 57

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ajiye gabanta, tako ci babu laifi dan kadan ta rage. Jingina bayanta jikin kujera tayi tana Jin yadda zuciyarta ke tashi cikin ta na ya mutsawa. Da gudu ta nufa toilet, Aesha ta mara mata baya, mairo ma ta bisu. amai tashiga kwararawa seda ta fitar da indomie tass ta koma ta zauna tana sauke wahalallen numfashi hawayen wahala na bin kuncinta. Aesha ce ta taimaka mata ta wanke baki ta rikota suka fito. Mairo nata jeramata sannu Gefenta ta zauna "Sannu sister, meke miki ciwo?" "Jiri nake gani" "Ko zamuje daki ki kwanta?" Kai ta gyada, tarike hannunta suka haura dakinta. Kan bed ta kwantar da ita, itama ta zauna gefenta tana mata sannu. Wayanta ce ta dau kara, Aesha tamata picking ganin sunan mummy na yawo kan screen din. "Mummy na barka da safiya" "lafiya kike kuwa?" "Tun jiya da muka dawo bana Jin dadi malaria ke damuna" "Eyyyaaa sorry, kinsha magani? Nasan ki da kin magani Muhibbah". "Munje asibiti, Yaya ze tawomun da magungunan" "Allah yabaki lafiya" "Ameen mummy na". Sallama sukayi, mummy najin babu dadi ta bakin Muhibbahn nesa beda dadi amma yaza'ayi. "Wllhi sister ko kiyarda ko karki yarda ciki gareki dan ban yarda dake ba, zaki lakama malaria saboda batada bakin karya taki, amma ai result ze nuna kuma zakice na gaya miki". Gabanta ne ya fadi, kardai da gaske cikin ne da ita dan ko lokacin da likita yace malaria ke sata zazzabin dare, ai bata amai kuma bata Jin Jiri ko dai maganan Aisha nada kamshin gaskiya? Saurin girgiza kai tayi tana runtse ido idan ko ciki gareta ta shiga uku ya zatayi da karatun ta. "Uhmmm idan tayi wari maji" cewar Aesha Ita dai bata tanka taba har bacci ya dauketa. Duk minti minti seya kira yaji jikinta Aesha tace mai bata farka ba. Yana aiki a office yaji ana knocking, be tashi ba se izinin shigowa da ya bayar. Doctor fareeda ce ta turo kofan tashigo fuskarta dauke da murmushi "Congratulations doctor! Madam na dauke da ciki har na tsawon sati 8 da kwana biyu" tafada tana ajiye mai result din. Besan lokacin daya mike ba yana murmushi har hakoranshi na bayyana, duk da tun safe yasan da cikin sedai yana son tabbatarwa da kuma sanin adadin kwanakin cikin. Ba karamin Jin dadin albishir din nan yayi ba dan yama rasa abin fada se alhamdulillah kawai yake mai mai tawa a fili. Ita ko doctor kallonshi take da mamaki, dama ya iya murmushi har haka amma yake hade girar sama da kasa Koda yaushe. Wayanshi ya zaro yamata transfern kudade masu yawa, yace tukuicin albishir, a take Kuma yamata Karin albashi. Godiya tayi ta mai har tarasa abin fada ta fice tana fada ma wasu nurses boss ya kusa samun baby. Tattare files din kawai yayi ya fice, nurses suna ta tayashi murna, suna mamakin yadda yake amasawa fuskarshi dauke da murmushi. Gida ya nufa be gansu a parlour ba ya nufa dakinta, amai ya tarar tanayi Aisha na rike da ita. Dasauri ya karasa ya rike ta Aesha ta mike ta baro toilet din. Tana gama aman ta fashe da kuka tana kiran mummyn ta. Baki ya kuskure mata ya dakota suka fito Aesha tayi musu sallama yasa driver ya maidata gida. "Bloody! Me ke miki ciwo?" "Komai ma". Tafada tana cigaba da kukanta, murmushi ya danyi Jin tace komai ma ciwo yake mata. Zeyi magana wayanshi tafara ringing ganin sunan ummi yasa yace "Please bloody kidena kukan nan, kar kanki yamiki ciwo kinji?". Kai ta gyada, gaba daya tausayin ta ya kamashi da da yadda zeyi daya amsarmata ciwon. Numbern ummi yayi dialing ringing biyu ta dauka, "Assalamualaikum, Ummi ina wuni" "lafiya kalau! Ya jikin Muhibbah?" "Dasauki". Yafada yana kallonta "Allah yakara sauki" "Ameen" "Suhailat ta sauka yanzu mijinta ya kira yake fadamun, A asibitin ku ne ma, kafita kenan su Kuma suka shiga". "Alhamdulillah! Allah ya raya, me aka samu?". "Ansamu dan saurayi" "Allah ya raya shi akan Sunna" "Ameeen! Kayi ma Muhibbahn sannu" kafin yayi magana ta yanke kiran. Murmushi kawai yayi, idan da sabo yasaba da halin ummi yau ma yayi mamaki da sukayi magana har haka Doctor fareeda ya kira yace a tabbatar an ba Suhailat kulawa na musamman kafin yaje asibitin dasafe. "Aunty Suhailat ce ta haihu?" Kai ya gyada mata yana shafa fuskanta yanajin wani farin cikin dabe taba tsintar kanshi a ciki ba kamar na yau. "Allah ya raya" "Ameen blood". Muma Allah yakawo mana namu babyn lafiya. Murmushi kawai tayi tana rufe fuska. "Albishirinki?" "Goro". "Toh se kin bada tukuici kana zan fada miki" "Aa seka fara fada kana zan baka". Lakace hancinta yayi "Aa banyarda ba, kiji wayau". Dariya sosai tayi "Ai ni nayi alkawari zan baka kai dai ka fadamun". Cikinta ya shafa yana murmushi "Congratulations mun kusa yin baby". Dan zaro ido tayi "baby Kuma?" Kai ya gyada mata kana yace, "Kinada ciki". Da mamaki take kallonshi "Ciki? Niiii?" Tayi maganan tana nuna kanta. Gira ya dage mata "Uhmmm kinada ciki har na tsawon sati 8 da kwana biyu". A zabure ta mike tana taba cikinta, tana girgiza kai. "Aa badai ni ba" mikewa yayi ya riko hannunta ya zaro result din ya damka mata. "To idan bake ba waa? Karanta kigani"Yafada har lokacin yana murmushi. Karba tayi ta karanta tayo saurin wurgar da papern kasa, tana fashewa da kuka "ciki! Makarantan fa? Dame zanji rainon ciki ko karatu? Yaya kana ganin irin azabar danake ci tun daga jiya har zuwa yau ban isa inci abinci na zauna lafiya ba se na fitar dashi. wllhi bazan iya ba, inaa ban shirya ba, ba yanzu ba, sedai a zubar dashi, baze yuwu ba." tana maganan tana kuka kamar wacce ta zare. Ranshi ne yayi kololuwan bacci ya fara matsawa inda take, ganin ya koma mata Fu'ad dinta na dah, yasa zuciyarta bugawa, tana ja baya har ta kai karshen bango. Da yatsa yashiga nunata "Idan kika Kuma ambaton zubar mun da ciki wllhi sena tsinkamiki mari, kuma idan kika kara zancen akan makaranta bakya son cikina har kika bari naji toh wllhi wllhi keda makaranta har abada, zabi ya rage naki ciki dai yana nan daram a jikin ki kuma dole ki haifemun dana, makaranta Kuma idan kinga bazaki iya ba is fine, zaki iya hakura da ita banida matsala da wannan be da meni ba. sannan kince baze yuwu ba ko? Toh dan Allah kiyi abinda kika ga dama ai ga cikin nan a jikin ki, nace kiyi abinda kika ga dama kinji ko?" Masifa yake kamar ze kai mata duka beta ba tinanin yadda take fadan bata son cikin dagaske take har a zuciyarta ba. Beyi tinanin har yanzu bata san inda yake mata ciwo ba. Tsaki yaja ya juya ya fice dan yadda ranshi ya bacin nan ze iya Kai mata duka idan ya cigaba da tsayuwa. Seda taga fitar shi ta sauke numfashi, dan ba karamin tsorata tayi ba, ko a baya bata taba ganin fushin shi kamar na yau ba. jira kawai take taji saukar mari. Zamewa tayi ta zauna a kasa ta daura hannunta a kai tareda sakin kuka me sauti............. AMINIYAR ANGO [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD AMINIYAR ANGO* *Page 54* Dakinshi ya wuce yayi wanka yasa kaya ya fice masallaci. Ta jima tana kuka, seda taji an soma kiraye kirayen sallahn magrib kan ta mike ta shiga toilet. Gaban shower ta tsaya ruwa nata sauka kanta, ta dade a haka kan ta fito daure da towel. Rigar bacci ta dauko tasa ta zira hijjab ta tada sallah, tana nan zaune tana azkar seda aka kira isha'i kan ta mike ta gabatar da sallahn, ta nade pray mat din tareda zare hijjab din jikinta ta haye gado. Yunwa takeji amma tana tsoron sa wani abu a cikinta gudun ta shiga Kwara amai, Blanket taja ta rufe gaba daya jikinta tare da rufe idanunta babu jimawa ko bacci ya dauketa. Seda yayi isha'i ya biya restaurant ya siyo musu abinda zasu ci kan ya shigo gidan. Koda yashigo be sameta parlour ba, ya wuce kitchen ya dauko plate, ya dawo ya zauna a dining yayi serving kanshi. Har ya gama bata fito ba be nemeta ba ya wuce parlour ya zauna tareda kunna tv, Rabin hankalinshi na kanta yana tinanin ko wane hali take ciki? kuma yasan ko abinci bata ciba. daurewa kawai yakeyi saboda yana so ta gane kuskuren ta. Mutsu mutsu ta shiga yi, gaba daya ta kasa bacci cikinta se juyi yake, ji take kamar an mata yasa. Dole yasa ta ziro kafafunta kasa tasa takalmi ta nufo down stairs. Jin taku alamun ana saukowa yasa ya Kalli gurin, zuciyarshi ce tayi tsalle lokacin da idanunshi suka kai kan 'yar rigan baccin dake jikinta dabata karasa guiwaba, hannunta na vest daga saman wajen kirjinta net ne ana hango komai na jikinta, wani abu ya hadiye yana jin zuciyarshi na fisganshi zuwa gareta, suna hada idanu ya dauke kai ya mayar kan tv. Ita ma bata ce komai ba ta karasa dining ta zuba abincin tashiga ci, zuciyarta fal fargaban dawowan abincin. Tako ci sosai ta dauki ruwa tasha tare da furta Alhamdulillah. Mikewarta keda wuya tafara yunkurin amai, ko dakinta bata nufa ba, ta fada wani daki a guje, ta shiga Kwara amai. Da hanzari ya mara mata baya, seda ta fitar da abincin data ci tass kan ta zauna cikin toilet din tana sakin kuka me ban tausayi. Mikar da ita yayi, ya kuskure mata baki yayi sama da ita suka fito daga toilet din Dakinshi suka haura ya kwantar da ita saman bed, ya dauko magungunan daya tawo mata dasu daga asibiti ya balla yabata, tsabar Jin jiki batama San takarba ta watsa a baki ba ya mikamata ruwa ta kora, haurawa gadon yayi ya janyota jikinshi, har lokacin Kuka take sosai tana Kiran mummynta. Hannunshi ta rike "Yaya dan Allah katausayamun a cire cikin nan, zan mutu....." Kallon dayake watsamata yasata saurin yin shiru, tana kokarin zamewa daga jikinshi. Zamewa yayi ya kwanta, ya janyota ya dora kanta a kirjinshi yana shafa gashinta tareda dan bubbuga bayanta, a haka har bacci ya kwashesu. Allah ya taimake ta yau zazzabin dare
Chapter 57 · 0% Book details