← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 69

Sashe 10

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da wata munafa ba, Allah ya tabbatar mana da alkhaeri." "Ameen! Ya fada a fusace ya wuce yabarta nan zaune" "Bayanshi tabi da kallo tasauke ajiyar zuciya, tana addu'ar Allah yazaba abinda yafi alkhaeri idan Kuma babu alkhaeri Allah ya lalata al'amarin cikin sauki"........ *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 18* Kwanci tashi babu wuya gurin Allah Zaune take a parlour tana faman chatting tana sakin murmushi da alama firan ya dauke hankalinta, wucewa ya zoyi aiko ya take kafanta "wayyo Allah mummy na nashiga uku" "Harara ya watsamata ya bige kafan ya wuce yabarta nan tana matsar kwalla" Seda taga yabar gurin kafin tace "Allah ya isa ban yafe ba" bata zata ba taji rankwashi "wa kike ma Allah ya isa". A guje ta nufi dakin mummy tana zare ido "Lafiya kika shigo babu sallama kike ta zare ido kamar kinyi karya?". Numfashi tasauke kafin tace "babu komai fa mummy, dama kitchen zanshiga na hadama su Abba dinner kafin su sauka shine nace bari na leko banji motsin kiba". Kallonta tayi badan ta yarda ba tace "naji! Muje nima ganinan zuwa in kama miki". Tom kawae tace ta juya ta shiga kitchen Haduwa sukayi da mummy da me aikinsu suka yi girkin a dafa wannan a dafa wancan muhibbah tace be isaba seda akayi abinci kala 5 da drinks kala 3 sun Kai 5 hours kafin suka kammala, muhibbah ce ta shirya dining din kafin me aikin ta gyara kitchen din tsaf aka zuba mata abincin a food flask ta tafi dashi. Wanka tafito ta tsaya gaban mirror ta taje gashin kanta ta kama da ribom ta dan shafa powder tasa kwalli se lipstick, wardrobe ta bude ta dauko black abaya ta zira tayi rolling gyalenta ta feshe jikinta da turare ta dauko black flat shoe dinta tasa ta nufo parlourn. "Daddy mu tafi please su Abba sun kusa sauka" tafada tana duba agogon dake manne a parlourn Ki bari yayyinki su fito su muke jira, ba tace komai ba Kuma bata zauna ba seda suka kara kusan 10 minutes kafin suka fito *Fu'ad* Akanta ya sauke idonshi yana karemata kallo, tana dago idonta karaf suka sarkafe dana juna, juyamai ido tayi "ya tabe baki yana dauke Kai" "itama dauke Kai tayi daga kallonshi tabi bayan mummy suka fita". Saukar flight dinsu babu jimawa suka karaso airport din. *Muhibbah* Da gudu ta karasa tayi hugging din Ammar tareda fadin "oyoyo ya Ammaar, I really miss you". "Miss you too muhibbah" ya fada yana rabata da jikinshi "Ke Kam muhibbah bazaki taba girma ba, Baki san kin girma bane kike hugging din Ammar" cewar mummy. Dan turo baki tayi ta karasa zatayi hugging Abba yayi saurin riko hannunta yace "maamana kinfa girma". "Nidai Abba ban wani girma ba fa" tayi maganar a dan shagwabe, duk gurin sukasa dariya. Hugging din Aisha tayi tace "you are welcome dear, Miss you" "Miss you too sisto" Driver ne yazo ya dauki kayansu yasa a booth Abba da daddy suka shiga mota Daya, Mummy, Ummi, suhaila suka shiga dayan motan, Muhibbah, Aisha, Ammaar suka shiga mota Daya, Anas, Fu'ad da Suhail suka shiga dayan motan suka dauki hanyan unguwar rimi low-cost. Mazan basu shiga ciki ba suka nufi masallaci saboda kiraye kirayen sallahn magrib da akeyi. Su Kuma matan driver yakarasa dasu gida Suma babu Wanda ya zauna suka nufi sama dakunan da suke sauka idan suka zo kd, muhibbah da Aisha suka haura da kayansu da driver yashigo dashi. Seda suka idar da isha'i kafin suka sauko kasa, basu Kai ga zama ba mazan suka karaso, za'a soma gaesuwa ne mummy tace "Aa gaisuwar nan bazata kare ba a bari aci abinci tukunna" haka ko akayi suna zaune a dining gabaya Daya a halin kowa cike yake da farin cikin ganin 'yan uwa. Muhibbah ce ta soma saving dinsu Daya bayan Daya kowa seta tambayeshi abincin da yake so da drink din daze Sha tana zuwa kan fu'ad ta kafeshi da ido taki magana Shima bece komai ba da ido tayi mai alaman me zeta samishi, kadan ya rage beyi dariya ba saboda yadda tayi da idon amma ya fiske, yayi kamar besan da itaba. Kuma babu Wanda ya nuna yasan me sukeyi, ganin ya kyaleta se danna wayanshi yakeyi ya sata cewa "me zan zuba ma?" Seda ya dauki mintina kamar baze yi magana ba se Kuma ya dago yace "komai ma" ya maida kanshi kan wayarshi. Sanin baya son cin abinci me nauyi musamman da dadare yasa ta zuba Mai jallof din spaghetti ta tura Mai, ta bude baki daker kamar anyi mata dole tace "drink fa?" "Any one" yafada a takaice, kunun Aya ta zuba Mai takara tura Mai Parlourn daddy ta Kai musu nasu abincin, kafin tadawo tasoma cin nata suna dan taba fira da Aisha. Parlour suka koma aka shiga gaesawa daganan aka hau firan yaushe gamo, Aisha ta dauko dinkin su ita da muhibbah Wanda za susa gobe tashiga nuna mata aikam ta hau tsallen murna saboda yadda dinkin ya tsaru. Se 10 suka tafi bedroom, Aisha Kuma tabi muhibbah bedroom dinta suka kwanta Da wuri suka tashi, sauri sauri muhibbah ta shirya cikin riga da wando, a bayan rigan an rubuta sunan school dinsu (KA'AB BN MALIK) class of 2025, sama sama tayi break fast din ta dauki after dress ta daura tasa baby hijjab ta tafi. Seda taje school din suka kara shiryawa da kyau sukasa graduation gown dinsu Tanata waige waige gurin graduation se can ta hango a halin nata reras a zaune take sanyin dadi ya rufeta, tanajin a kaunar dangin nata har cikin Kashi da jijiya. Sunayensu aka fara kira daya bayan daya ana basu gift Ana Kiran the must obidient student in the school kamar daga sama taji ance *FATIMA A MUHAMMAD (BICHI)* Gabanta ne ya yanke ya fadi tashiga zare ido take, summy tace "kije mana kefa ake kira" cikin sanyin jiki ta iso filin gurin Abba ya karaso ya rike gefe itama ta rike dayan gefen akayi musu hoto, kamar jira take a dauka ai Ko tafada jikin Abba tasa kuka, rarrashinta yashigayi mutane na kallon shagwaba suna mamakin miye abin kuka wasu Kuma suna dariya sunaji ta birgesu, daker tayi shiru ta koma gurinta ta zauna. The must brilliant student in SSS 3 *FATIMA A MUHAMMAD (BICHI)* tun kan ta fita hawayen farin ciki suka balle mata daddy yafito ya rike gefen gift din itama ta rike gefe aka daukesu hoto, har tadawo ta zauna Bata bar hawaye ba, summy se sharemata su take wasu na gan garowa. Best student in physics *FATIMA A MUHAMMAD (BICHI)* Ai sandarewa tayi a zaune tama kasa tashi seda teachern physics dinsu Dan ladi Dan juma dake ba bahaushe bane ya riko hannunta ya karaso da ita, Abba yace Suhail yaje ya amsarmata daddy yace aa Fu'ad yaje tunda shine gaba da Suhail, hakanan ya karaso ba don yaso ba, ita Kuma se juye juye take tacika fam da haushi bataga mukhtar ba karaf suka hada ido ya dagamata hannu, tako washe baki tana dariya aka daukesu wannan karon award ne aka bata. Seda aka tashi suka dinga selfie ita da family dinta sunyi gaba dayansu sannan suka koma yi da ita idan wannan yashiga anyi musu wannanma yashiga fu'ad ko daker yatsaya aka musu tako kwanto jikinshi akayi musu hoton ana dauka ya tureta ta tabe baki a ranta tace "kaji dashi dai" Aisha taja bayan classes din a can suka samu mukhtar tsaye ai Kam aka shiga daukarsu hotuna. Daga Mai hannu tayi tace "bye dear zamu tafi ina jiranka anjima a gida after asr". "Okay I will be there in Sha Allah" Gida yacika babu laifi family sun hadu su Aunty Asma'u dasu Aunty hafsat duk sun zo anata fira ana Raha. Wanka tashiga ganin har 3pm gashi sunyi da mukhtar by 4 zezo Me kwalliya aka kira tayi musu itada Aisha sun hadu sosai sunyi kyau ha r sun gaji da kyau Parlourn ta nufo sanye da less me bala'in tsada maroon colour straight gown yaji bead work ta yafa gyalenta me nett maroon ga sarkarta se sheki take kamar ta gold, Aisha na biye da ita sanye da irin kayanta, ai Kam tana isowa parlourn ya dauki guda Aunty Asma'u tace "kunga Amaryar next week kin ganki kuwa kamar yau ne ranan" murmushi tayi dan bata fahimce komai tace "Ah Aunty kice yau shalele idan ya ganni seya rude" murmushin tausayinta tayi tace "uhmmm! ba lallaima ya iya ganeki ba" murmushi tayi tace "Nagode" Hannun Aisha ta rike suka karasa compound din. Can ta hango shi jingine jikin motarshi, cikin tafiyarta me daukar hankalinshi take takawa har ta isa gabanshi, iska ta hura mishi a ido tace "Hey" shikam tun fitowanta ya kafe ta da ido yakasa ko motsi ya daskare a tsaye yaushe numfashi ya ja ya sauke ajiyar zuciya yace "baby kin ganki kuwa, you look so cute, and adorable, kinyi kyau" fuska ta rufe tace " kaima kayi kyau irin sosai din nan fa" sukasa dariya dukansu har Aisha. Karaf idanunsu suka hade dana juna gabanta yayi mummunar faduwa tsoro yakamata amma ta fuske tacigaba da murmushin yake, Ai suna hada ido da Aisha tace "innalillahi wa inna ilaehi raji'un, muhibbah kinsani a musiba daga rakiya nima nasan nashiga cikin ukuba"............ *Wanda be SO kutambayeshi dame yake more rayuwaaaa* *Yau yakamata atamfamun nayi page me Dan tsayi nayi kokari atafamun Kuma ayimun comments indai anji Dadi [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 19* Jikin Aisha ne ya dauki kerma, kirjinta se bugun sakwaran Lagos yake ta sadakar kawai jira take taji saukar duka, itama muhibbah tsareshi tayi da ido ganin ya nufo inda suke tsaye tana jira taga iKon Allah koran mukhtar din zeyi ko kuwa dukansu zeyi a gaban mukhtar. Karasowa yayi ya mikama mukhtar hannu sukayi musabaha yace "Barka da yamma" "barkaka dai". Murmushin karfin hali muhibbah tayi kafin tace "baby ga big bro". "Oh shine ya Suhail din?". Girgiza Kai tayi tace "Aa wannan shine babban yayanmu gaba daya ya Fu'ad sunanshi daga yolah" juyowa tayi tana
Chapter 10 · 0% Book details