← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 69

Sashe 13

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mukhtar, sau nawa zan fadamaka dan Kai kadai aka halicceni, wllhi ka tsinkamun zuciya, kadena irin wannan maganan babu abinda ze faru, soon zan zama halalinka, khairan in Sha Allah". "Allah yasa haka" yafada yana murumushin yake, dan shi yanzu yadena tausayin kanshi, tausayin muhibbah kawai yake. "Ameen" ta fada a takaice. Cup din tea dake gefen side drower ta kalla seta tina da ta shigo taga Mubarak na bashi tea, tashi tayi ta dauko wani cup din tahada mai tea me kauri, tazubo soyayyan potatoe din ta hauro bed din tashiga bashi tana janshi da fira har yaci sosai kafin tabashi ruwa yasha ta tattare kayan ta ajiye a bed side drower. "ya mukhy ina wayarka naga time" yace "ai Muna gama waya dake tadauke babu chaji". Yanada chaji kawai yafada ne saboda baya so yabata wayan. Tun jiya daya baro gidansu yana driving Kiran wayanta yashigo beyi picking ba se bayan Kiran ya katse yaga ashe ta danna recording a wayarshi tun lokacin yayi kokarin goge recording din amma yakasa, shiyasa tana shigowa asibitin ya kashe wayan cikin dabara yaba Zahra yamata alama da ido ta boye mishi, yanzuma yasan ba time zata duba ba tunda ga wayarta nan a hannunta kawai tana so ta tura recording din ne, baya so ta sani yanzu tunda da su Abban naso tasani da sun fadamata da kansu duk da yasan dole sirrin boye ze bayyana. Tace "eyyyaaa sorry daka sa chajin gama socket kusa da bed din". "Aa karki damu Zahra zata zo tasa, kitashi ku tafi kinji har anfara Kiran asr". "Take care of your self, kayi chajin phone Dinka da wuri please, idan nakira naji switch off zuwa magrib zaka ga nadawo". Murmushi yayi har hakoranshi suka bayyana yace "yadda Kikace haka za'ayi madam, kiyi sauri ki tafi bye" turo baki tayi tace "au koratama kakeyi ko"?. "Na isa? Ni asuwaaaa"? Hancinshi taja tace "Kai a mijin fateema xahrah". Murmushin yake yayi Wanda yafi kuka ciwo Bata reda yace mata komai ba. Sauka daga bed din tayi tace "kayi bacci ka huta amma kada kabama zuciyarka hutu Kona second daya wajen tinanina" tafada tana daga mai hannu "Kai ya gyadamata yana murumushi, yabita da kallo har ta bude kofar ta fita". Wajen fita sukaci karo dasu umma na kokarin shigowa tareda sauran 'yan uwan mukhtar, risinawa tayi tana gaishe da umma tana sosa keya se lokacin tafara Jin kunyan abubuwan da tayi lokacin data shigo dakin, itama umma amsawa tayi cikin kulawa kana suka gaishar da sauran mutanen sukama umma salama tanata musu godiya suka wuce. Ita inda suka fita tanan suka lallaba suka shiga, Allah yataimakesu babu wanda yagansu. Hijab dinsu suka cire suna kokarin nufar parlour muhibbah ta riko Aisha tace "sedai Daya ya fara fita daga baya se dayan fita". Aisha tace "toh sedai ke ki fara fita" "nayarda". Parlourn ta nufo tana Mika tana mutsutsuke fuska tayi wata hamma tana fadin "Alhamdulillahil laxi ahyana ba'ada ma amatanah wa ilaehin nushur". Ummi tace "Aa muhibbah dama kuna ciki" "Eh ummi Muna ciki Muna kallo kawai bacci ya daukemu ashe har yamma yafara yi" "Toh ina Aishan" "har yanxu bata tashiba ummi". Umi tace "jeki ki taso ta kuci abinci baccin ya isa haka" "toh ummi". Tana shiga dakin tafada kan bed tana dariya taba Aisha labarin wayan data masu ummi basu gane sun fita daga gidan ba. Dining suka dawo sukayi lunching dinsu. Kitchen suka shiga suka fara girke girke, Aisha nayin na gida ita Kuma muhibbah nayin na kaiwa asibiti. Aunty suhaila ce tashigo ta samesu tace "me ake dafa mana"?. "Tuwon shinkafa da miyan agushi" cewar Aisha. Ta bude dayan pot din taji kamshi ya duke hancinta tace "wannan Kuma girkin fa" suka Kalli juna ita da Aisha, muhibbah tayi saurin cewa "namu ne mu bazamu ci tuwo ba gaskiya" toh kun huta mu ai zamuce tafada tana barin kitchen din. Favorite food din mukhtar ta dafa ta dauki hadadden flask ta zuba aciki ta hada juice din banana ta zuba a hadadden mug ta jera food flask da mug din a basket tasa spoons da cups ta kwance gyalen riganta dake daure a kanta ta yafa ta fita taba driver tafada mai sunan hospital din da abinda ze ce idan yaje, kafin ta juya ta koma ciki. Kama ma Aisha aikin tayi suka jera abincin a dining suka shirya gurin tsaf. Wanka sukayi sukayi sallahn magrib basu fito ba seda sukayi Isha'i. Parlourn daddy suka nufa suka gaishe dasu kafin suka dawo dining din sukaci abinci. A parlour suka baje anata fira tana ma yusrah wasa ita Kam se wangale baki take tana dariya tana so muhibbah ta dauke ta amma taki daukarta. Suhaila tace "Kai muhibbah ki dauketa mana" tace "Aa ki rike 'yarki rawa take so nikuma bazanyi ba". "Toh ai ke kika koyamata rawan" dariya tayi tace "toh nikuma yazu bana Jin yin rawan, kiba mummy ko ummi suyi mata". Ummi tace "Aa da dare nan sedae mummy din" ai kamar tasan me ake fada tasa kuka mummy tace "Suhaila tashi ki goyata kozatayi bacci". Maida hankalinta tayi kan wayarta tana chatting da mukhtar se murmushi take, itama Aisha chatting dinta take suka bar su mummy suna firar su. Kamar daga sama sukaji muryan Fu'ad ya kira sunan su "Aisha! Muhibbah!" Har suna hada baki wajen cewa "Na'am" yace "follow me" Zaro ido sukayi suna dafa kirji, yana gama fadar haka ya juya yabar gurin. Ummi tace "ko bakuji kiranku ake ba" mummy tace "ai da Gani basuda gaskiya yanzu haka wani laifin sukayi tunda kika ga haka" "kuje ku karba hukuncin ku zaku hadu da ya fu'ad" cewar suhaila tana dariya. Sum sum suka tashi tare da barin wayoyinsu suka wuce, suna isa gabanshi sukayi kneeling down Wani kallo ya watsa musu Wanda yasa 'yan hanjinsu kadawa yace "ina kukaje dazu" ai take gabansu yayi mugun bugawa suka hawa rawar Baki, suna mamakin yadda yaga fitar su daga gidan. Aisha tace "munje mall ne" muhibbah ma tayi saurin karbe zancen gudun kar Aisha ta kwafsa tasan halin shirmenta tsoro ze iya sa asirinsu ya tonu "dama munje mall ne shine muka biya gidan su summy kawata muka gaisheta batada lafiya". Harara ya watsa musu yace "wa kuka tambaya?" Sukayi shiru kana can muhibbah tayi karfin halin cewa "babu kowa, kayi hakuri" dan Allah Yaya kayi hakuri wllhi bazamu kara ba" cewar Aisha tana matsar kwallan tausayin kansu. "No ban hanaku ba kucigaba gobe ma ku kara" suka shiga girgiza Kai suna bazasu karaba. yace su kama kunne, sun Kai 20 minutes a haka se zufa suke suna kuka tun hawaye na zuba har idonsu ya kafe, amma ko kulasu beyi ba bare su sa ran ze hakura sema zama dayayi yana operating phone dinshi.......... *Sister ta ta haehu tasamu baby girl kusama babyn albarka* *Ku lallaba da wannan please* *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 22* "Go on your knees" ya fada batareda ya ko Kalle su ba, dama kamar jira suke suka zube kan guiwowinsu suna matsar kwalla. A hankali ya mike ya tako gabansu, suka yi saurin kankame jikin su suna jira suji saukar duka, kawunan su ya gwara babu zato se ji kake kuuuum, kuka suka sake tsabar azaba ya dora dan yatsarshi a kan lips dinshi yace "shiiiiii! Ku hadiyeshi bana son Jin ko tarinku anan, ba kun raina mutane ba kanku na rawa ko, zan gyara muku zama". Hannu suka sa suka toshe baki suna kokarin hadiye kukan. "Get out" yafada cikin tsawa. Da gudu suka kwasa har suna bige juna wajen rige rigen fita, babu kowa a parlour se wayoyinsu suka dauka suka karasa bedroom da gudu kamar ance gashinan a bayan su, a kan bed suka zube suna fitar da numfashin wahala ko motsin kirki sun kasa, daker muhibbah ta fisgo maganan tace "wllhi na kosa ya Fu'ad ya bar garin nan kije kita amsar ukubanki ke kadai ayi mutum babu imani". "Allah nima bazan bar garin nan ba ai nazo kenan shiyasa na tattaro duk wasu takardun school dina nima nan zan cigaba da school" ta karasa maganan tana haki kamar wacce tayi tseran gudu. Basu San lokacin da baccin wahala ya daukesu ba, makara sukayi basu tashi farkawa ba se 6am, dasauri muhibbah ta ziro kafanta da niyyan shiga toilet ta dauro alwala base kafa tace takani mu gani ba, hawaye ne suka shiga ambaliya a fuskarta se da rarrafe ta shiga toilet din tazo tayi sallahn a zaune. Rarrafawa ta karayi ta haye gadon ta tashi Aisha itama kasa mikewa tayi seda rarrafe tayo alwala. Wajen 9am Aisha tabasu shawarar suyi wanka su gasa kafar ko haka ko akayi bayan sunyi wanka sun fito suka dauki man zafi suka shafa, cikin iKon Allah ko sukaji dama dama daker suka isa parlourn Koda sukayi break fast ma dawowa bedroom sukayi suka cigaba da baccin wahala. Su ummi na zaune a parlour sukaji ana danna door bell, Fu'ad ya kalla Ammaar dake zaune suna game da Anas, sum sum ya tashi yaje ya bude kofar, Bala driver ya gani tsaye suka gaisa ya mika mai basket din hannunshi da wata white paper yace wai gashi a ba hajiya karama, bece komai ba ya karba ya koma cikin parlourn yaba mummy ya fada mata abinda drivern yace. Da mamaki take kallon basket din tace "oh ni hafsatu wa kuma muhibbah ta aikama abinci". Suhail yace "Anas jeka ka kira Muhibbah". Tsayawa tayi tsakiyar parlourn tana mutsutsukan idanu. Mummy ta dubeta tace "wakika ai kama abinci". Se lokacin ta ware idonta da kyau ta kalla basket din ta waske tace "Laaa mummy mantawa nayi ban fada miki ba, wani class mate dina ne bashida lafiya shine fa na aika driver ya Kai mai abinci" ta karasa maganan tana saurin daukan basket din saboda hango white paper din da tayi a ciki, a kitchen ta tsaya ta war ware papern taga an rubuta "ThANk YOU SO MUCH DEAR, LUVS YOU HAYATEEE". Wani murmushi ne ya kufcemata a kan lips dinta tace "LUVS YOU TOO LIFE CYCLE" tafada tana kashe ido daya tanajin kamar tana gabanshi.
Chapter 13 · 0% Book details